← Book details Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 7 OF 40

Chapter 11&12

Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Gaba d'aya ta shiga rud'ani, ynx ta yaya xata cigaba da rayuwa a cikin mahaukata, ita dai mutanen data gani sun bata tsoro. Nawal ce ta kalli xaljamil! Aunty su waye mahaukata kuma? Da sauri xaljamil ta kalli nawal, sai sannan ta gane maganar da tayi a fili ne ba'a xucia ba. Murmushin yak'e xaljamil tayi tana kallon nawal, baby ya sunan ki? Daria nawal tayi, ni sunana nawal, wow nice name, murmushi nawal tayi thanks my aunt.


Mom ce ta turo k'ofa hannun ta dauk'e da coffee, a kusa da xaljamil ta ajiye sannan ta mikawa nawal nata.wow mom thanks alots, daria mom tayi dan manyancen nawal na birgeta, yarinya ce da bata wuce shekara 5 ba amma wayonta ya mata yawa.


"Xaljamil ce ta kalli mom duk ta shagwabe fuska kamar xatayi kuka, cikin yaren larabci ta fara magana,mom wai muna nigeria ne? Kallon ta mom tayi cikin rashin fahimtar tambayar da xaljamil ke mata. Cikin yaren larabcin mom ta bata ansa, yea muna nigeria akwai matsala ne? Hawaye ta fara yi dan tasan ta rasa rayuwa mai yanci, ta daina fita, shikenan ita a d'aki xata kare rayuwar ta.


"Nawal ce ta kalli mom da duk jikinta yyi sanyi ganin aunt dinta na kuka, mom mai ya samu aunty xaljamil? Murmushi mom ta kirkiro ta kalli nawal, baby nawal kinsan bata da lafia shiyasa take kuka. Eyyah sannu my aunt, xaki samu sauki very soon kinyi? Gyad'a kai tayi tana gunguni a xuciar ta, nifa gaskia wannan yarinyar ta takura mini da yawa. Tashi nawal tayi daga jikin xaljamil, mom, aunt bari naje na duba uncle dina idan ya dawo, ok nawal mom ta ce nawal kam ta fita da gudu.


"Xaljamil ta kalli mom fuskarta na xubar da hawaye, mom baxan iya xama a nigeria ba, dan Allah ku mai dani qatar, murmushin takaici mom tayi ta kalli xaljamil, hmmmm xaljamil kenan, naga alama so kike ki jawo mana maganar da xama a gidan sarki sai ya gagare mu, duk ranar da aka gane bakyasan jinsinki, jininki wallahi xaljamil kin jawo mana tashin hankali, ko wane tsuntsu kukan gidan su yakeyi, ke yar nigeria ce kuma baxaki tab'a chanja wa daga hakan ba. Bbu maganar komawa qatar xaljamil kina nigeria harki mutu a nan xa'a binne ki inda aka binne yan'uwanki da danginki, kina bani mamaki xaljamil, sai na rasa ina hankalinki yake da ilimin ki suka tafi, kin chanja gaba d'aya daga yarda na sanki, ya kamata ki tattaro nutsuwarki ki da tunanin ki gaba d'aya kamata ki rungumi k'addarar ki, ki saki jikinki sai ki huta.


" Da bak'i da fari halittar ubangiji ne, kuma bbu wanda yake xabar yarda xa'a halicce shi da kuma a k'asar da xa'a halicce shi. Kuma indai yaren hausa ne indai kina gidan nan xaki iya, daga ranar da kika fara fahimtar hausa xaki gane ba shirme bace, shiru mom tayi tana kallon yarda xaljamil ta nitsu tana sauraran maganar ta.


"Jikin xaljamil kam yyi sanyi, sai dai itama bayin kanta bane, amma xata daure tayi kokari ta fara sakin jikinta da gidan ko xata samu xuciar ta ta xauna lpy. Ajiyar xucia ta sauke ta kalli mom da itama xaljamil d'in take kallo, mom insha Allah ba xaki kara jin irin haka daga gareni ba,ta fada hawaye na xuba a idon ta. Rungumeta mom tayi itama sai da tayi kukan saboda tausayin xaljamil,Allah ya miki albarka xaljamil. Ameen ta amsa tana goge hawayen fuskata.


"Ga coffee dinki ki sha sai kishiga wanka kinji, yes mom ta fada tana murmushi.


"Yareema jawad, tafe yake a motarsa wacce sai shik'e takeyi ya nufi gidan su areef xuciar sa fal nishadi, a wani tangameman gida yyi parking fita yyi daga motar ya taka da kansa har jikin gate d'in, knocking yyi gate man ya lek'o dan duba waye, ganin yareema jawad yasa ya bud'e gidan jikinsa har rawa yake yi, bajewa yyi a gaban yareema yana kwasar gaisuwa, sosai ran jawad ya b'aci amma ganin tsofan gate man yasa ya d'anyi murmushin da bai kai xuci ba, kud'i ya cire a a aljihunsa ya mik'awa gate man yyi gaba cikin takun kasaitarsa, a hankali ya k'arasa har inda xai sada shi da cikin gidan. Hayaniyar masu gidan yaji a babban palour d'insu, jin muryar tayseer yasa yareema jawad yaji kamar ya juya, dakewa yyi ya tura kai cikin palourn da sallama. Hajia binta, areef da tayseer xaune suna hira, gaba d'aya hankalin su yyi jikin kofar jin muryar yareema jawad. Wani ihu tayseer tayi ta nufi yareema jawad tana murna, mutuwar tsaye yyi dan yasan tayseer rungumar sa xata yi, dan haka yyi saurin durk'usawa k'asa ya fara kokarin cire takalmin kafarsa, hakan kam ba karamin bata ran tayseer yyi ba, amma tana tsaye bata tafi ba, a hankali ya gama cire takalmin nasa sannan ya mik'e ya nufi cikin palourn, caraf tayseer ta rik'e hannunsa, d'aga idonsa yyi ya kalli hajia da areef da suka xuba musu ido, murmushi ya kirkiro amma a xuciar yana Allah wadarai da irin tarbiyyar tayseer.


"Areef kam gaba d'aya ya kasa magana dan mamakin ganin yareema jawad yake,bai sanar dashi xaixo nigeria ba, amma ya sanar dashi ya kusa dawowa. Cikin tafiar k'asaitarsa dake tafia da tayseer ya karasa gaban hajia bayan yyi kokarin raba hannunsa dana tayseer. Durkusawa yyi har kasa ya gaida hajia cikin girmama wa, dan yareema jawad mulkin sa bai dame saba, yana bada respect ga duk wanda ya girmeshi. Da fara'a hajiar areef ta amsa tana tambayar sa fulani, cikin murmushin sa wanda ba kowa ke ganin sa ya bata ansa, tana gaishe ki. Ina ansawa yareema jawad ta fada tana murmushi. Tayseer kam xama tayi ta xubawa yareema jawad ido cike da so da kauna.


"Areef ne ya tashi bakinsa yak'i rifuwa dan farincikin ganin yareema jawad, hannunsa ya kama suka nufi part din areef. Xaune suke a palourn areef wanda a ka cika gaban yareema jawad da kayan tab'awa. Wallahi yareema jawad ka matuk'ar bani suprise, murmushi yareema yyi ai dama haka nakeso, eh ka kyauta. Kasan ku manya masu sarauta komai naku daban ne, hararasa yareema yyi yana murmushin sa mai birgewa. Areef xaka fara ko? Wallahi ynx sai na bar maku gidan ku, daria areef yyi tuba nake ranka ya dad'e suka sa daria gaba d'aya.


"Areef ne ya kalli yareema jawad wanda ya lumshe idonsa yana xuba murmushi,yareema jawad da alamu a kawai wani abin farinciki daya sameka, bud'e idonsa yyi tar a fuskar areef still da smile a face d'in shi, a hankali ya furta baby xaljamil sun dawo nigeria, areef kaga xaljamil kuwa, ta girma sosai tayi wani kyau, wallahi xaka rantse cewa bata had'a jini da nigeria ba. Baki areef ya saki yana kallon yareema jawad duk da yasan akwai soyayya mai karfi da yareema jawad kewa xaljamil, amma daga ganin yarda yake nishadi da farinciki ya fara xargin wani abu. Kai masha Allah areef ya fada, gaskia naji dadi sosai yareema jawad, kace auren ka ya kusa kenan? Juice din da yareema jawad ya xuba a bakinsa ya fito dashi, yana hararar areef, god 4 bid, xaljamil ai kanwa tace, kana tunanin xan iya auren ta, tun ba yau ba kasan irin san dana kewa baby xaljamil amma ta yan'uwan taka ce kawai, murmushi areef yyi daya tuna wani abu, ok yareema jawad, gaskia na gane manufarka amma idan bbu damuwa inasan ka hadani da xaljamil mana,cup din hannun yareema jawad ne ya fadi a kasa wanda sai da ya fashe, duk ya wani rikice, cikin rawar murya ya kalli areef, wai, wai xaljamil kake so? Wani shu'umin murmushi areef yyi eh ya fadawa yareema jawad.


Wata xufa ce ta lullube shi, da kyar yyi controlling temper d'insa ya kuma kallon areef, gaba d'aya yanayin sa ya sauya, sai da ya had'iyi wani yawu mai d'aci sannan yace, sai ka iya larabci kafin kaje, murmushi areef yyi kai nayi murna babban yaya dan dai larabci ai mun iya haxa da haxihi.wani kallo yareema jawad ya watsa masa wanda bai masan yyi ba.


SUMYNBASH CE💋


KUYI HKR DA WANNAN WALLAHI BA K'ARAMIN K'OK'ARI NAYI BA NAYI TYPING D'IN NAN, LUV U MASOYAN SUMYNBASH

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

YAREEMAH JAWAD

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

P. M. L. W


A romantic love story

2017


Story & written by

SUMAYYA SALEES SADEEQ


PLX MY FANS UR PRAYER IS NEEDED IM SICK, PLX KU SANI A DU'A DINKU, INA KAUNAR KU A DUK INDA KUKE MASOYAN SUMYNBASH 💋💋💋💋
Chapter 7 · 0% Book details