← Book details Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 10 OF 40

Chapter 17&18

Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

LONDON

"Yareemah jawad karatune ya kai shi london, ya karanci physiology ya kammala ya samu aiki a chan, aiki yake sosai and sunajin dadin aikin nasa dan yasan mai yake yi.


"Haduwarsa da xahra xahradeen a london ne, watarana ya fita xaga gari kamar yarda ya saba duk week end, shi kadai yake tafia kasancewarsa bashi da friends a london, tun yana skul wasu da yawa ke san abota dashi Amma yaki basu dama,saboda ixxa irin ta yareema jawad da kuma rashin son hayaniya. Abinda ya rabashi da gidansu kenan baya san hayaniya.


"Xaune yake a gefen wani beach yana shan drink, hankalinsa kwance yana cike da nishadi, sbd yana son kasancewa a irin wannan yanayin.


"Hello! Yaji wata murya mai d'auke da kissa ta daki dodon kunnensa, kamar baxai juya ba , dan duk nishadin da yake tare dashi ya dauke in seconds. Ya koma yareema jawad dinsa na asali, ya hade girar sama da kasa, cike da gadara ya dago sexy eyes d'insa ya kalleta. Omg! Xahra ta fad'a tana wani gyara tsayuwa,gaskia guy diinnan ya hado, fari tayi mai da ido kasancewar ta yar dunia.


"Riga body hug orange sai trouser purple, sai dan wani siririn veil data xagaye wuyanta dashi, kanta a bude yake, hakan ya bawa gashin kanta damar xuba gadon bayanta. Fara ce, mai matsakaicin tsaho, kyakkyawace ajin farko, banda maganar da tayi masa da hausa xai iya cewa kareena kapoor khan ce.


"Please xan iya xama? Ta fad'a tana masa wani shu'umin murmushi , bai tanka mata ba ya cigaba da shan drink d'insa a gayen ce.ganin bashi da niyar mata magana yasa ta nemi waje ta xauna.


"A hankali ta fara magana, sunana xahra xahradeen, mahaifina babban attajiri ne a k'asar nigeria, ni kadai ce yar'sa mahifiyata ta rasu ina karama, hakan yasa mahaifina ya kara daukan son dunia ya daura mini, ya kuma dauki nauyin kula dani duk da yawan ayyukan dake gabansa. A cikin family a kwai masu maganar xasu rikeni amma dad yaki yarda da hakan, sai kawai ya yanke shawarar kawo ni london yarda xan samu better life bbu mai takura. A time d'in na gama secondry dan haka university na fara a london, samari da yawa na kawo mini tayin soyayyayrsu amma duk basu mini ba cux mai aji nake nema irinka. Nan wajen xuwana ne, na tab'a ganin ka a nan na taho da sauri dan yi maka magana wayata tayi ringing, ganin precious dad ne yasa na kyaleka ka tafi da addu'ar Allah ya kara hadani da kai.duk daga ranar kullum sai naxo wajen nan ko xan ganka amma haka xan gaji na tafi , suddenly kawai na hangoka dan haka Ban tsaya bata lokaci ba na taho gareka, akan ka amince da soyayya ta gareka, hakane xaisa xucia ta ta xauna cikin kwanciyar hankali.


"Sosai ya d'ago ido ya kalleta up nd down, tsaki yaja a ransa yace "mace har mace amma bbu aji, wai a haka take neman mai aji irin yareema jawad ya so ta, tabbas ta had'o amma bata dace da irin matar da yake bukatar ya aura ba.


" Mikewa yyi tsaye tare da ajiye tin d'in drink dake hannunsa, wayoyinsa ya kwasa da mukullin mota ya xuba a aljihu, hannu daya ya xuba a aljihu ya fara tafia. Mikewa tayi itama "please ka taimaka mini ta fada tana matso hawaye,wallahi ina sanka" . Tsayawa yyi chak dan ya tsani wannan kalmar ta fito daga bakin xahra, d'ago wa yyi ya kalleta da sexy eyes d'insa da suka kara rud'a xahra, cikin husky voice d'insa ya firta"ni kuma bana sanki "kamar mai ciwon baki.


" Juyawa yyi ya cigaba da tafia cike da k'asaita, da gudu xahra ta bi bayansa, "dan Allah ko sunan ka ka sanar dani"
"jawad "ya fad'a a hankali ya nufi motarsa.Badan ran xahra yaso ba ta hakura ta kyale jawad, tana tsaye har ya tashi mota ya bar wajen,ajiyar xucia ta sauke, tayi wani murmushi tana lumshe ido, a hankali ta firta jawad, wow nice name, sunan yyi kama da sauki mai shi.


"Yareemah jawad da takaicin xahra yaje gida, yana shiga ya baje a palour yana dan hutawa, wayarsa ta fara ringing yana dubawa yaga mai marta ba, cik'e da ladabi ya d'aga ya gaida mahaifin nasa,sannan yyi shiru yana sauraronsa.


"Yareemah jawad lokaci yyi daya kamata ka dawo gida, na xuba maka ido dan ganin hankalinka amma naga baka san xuru ba, to ynx na fad'a maka k'asar ka tafi bukatar ka akan london, kwara kaxo ka bautawa k'asar ka ka samu lada, fatan ka fahinci abinda nake nufi "gyada kai yareema yyi kamar a gabansa yake," dan haka na baka xuwa one week ka ajiye aikin london ka dawo nigeria.


"To mai martaba, insha Allah xan taho a lokacin da kace"
"Shikenan yareema jawad Allah ya maka albarka "ameen ya amsa, sallama sukayi ya kashe wayar.


" Jingina yareema jawad yyi da jikin 1cter d'in daya ke xaune ya lumshe ido, yana jin dad'in xaman k'asar amma kuma ya xama dole ya barta tunda mai martaba baya so.


"Yareemah jawad mutun ne daya san darajar iyayensa, baya iya tsallake maganar su. Tagumi yyi hannu bibbiyu na rashin sanin ta ina xai fara.


"Ganin baxai iya tunanin komai ba a tym din yasa na nufi bedroom yyi wanka ya shirya cikin pajamas ya haye bed hade da du'a ya ja blanket ya kwanta da tunani kala kala.


Sunday

"Kamar ko yaushe misalin karfe 5:00pm ya bar harabar gidansa, ya nufi beach, xaune yake a inda ya saba xama yana cike da nishadi a ransa. Sanye yake da blue tshirt mai karamin hannu sai trouser red, sun glass ya saka da ya kara k'awata kyansa, sumar kansa a kwace luf ya mata style mai kyau sai kyalli take, wrist d'insa d'aure da watch mai bala'in tsada,jikinsa sai tashin k'amshi yake na turaruka masu tsada daya fesa.


"Idonsa a lumshe yake yana shan drink, jiyay daga chan nesa an kwala masa kira, a fusace ya waiwaya dan ganin mai wannan ikon, xahra xahradeen ya fad'a a ransa, harga Allah ya manta da ita, ballantana labarinta,. Da gudu ta karaso kusa dashi tayiwa kanta maxauni.


"Cikin fara'a ta mika masa hannu su gaisa, amma me? Ko kallon inda take yareema jawad bai kalla ba, marairaice murya tayi ta wani langwabar da kai tana masa shu'umin kallo, plx jawad mu gaisa mana. Yi yyi kamar bai jita ba ya cigaba da shan drink d'insa.wayarsa ce tayi ringing yana dubawa yaga fulani ce, wato "ummi" kayataccen murmushi ya saki wanda yasa xahra murxa idonta ko ba gaskia ta gani ba. A xucia ta fara magana, "dama guy d'innan yana murmushi? To ko dai buduwarsa ce? Turkashi, nan da nan taji wani kishi ya lullubeta kirjinta ya fara bigawa da karfi. Daga wa yyi suka fara gaisawa, daga yarda yake wayar ta gane ba buduwa bace maman shi ce, hhhhh! Kaji xahra da shishigi, ke da bama a tataki amma harda su kishi.


"I donta akan lips d'in yareema jawad, yarda yake magana gaba daya ya tafi da ita, ganin yarda yareema jawad ya shagwabe fuska sai abin ma yaso ya bawa xahra daria, ya xa'ai wannan guy d'in da ya kamata yyi aure da ya'ya amma ya ke shagwaba. Amsar daya baya ita ta dawo da xahra daga tunanin da takeyi, "eh ummi mai martaba yace nan da 1 week na dawo nigeria" kai alhmdlh wallahi naji dadi, dama yaushe rabon naga yareema nah, wajen shekara daya kenan fa"murmushi yareema yyi wallahi ummi na nima ina kewarki, kawai yanayin aiki nane sai a hankali, amma komai yaxo k'arrshe tunda monday xanje nayi reporting, kinga kafin friday na gama komai saturday sai na biyo jirgi.


"Murmushin jin dadi ummi tayi, to yareema Allah ya kawoka lpy, ameen ummi ya fada yana murmishi. Sun fi 30 mints suna waya da ummin sa ,cike da so da kauna na uwa da d'a. Waowayowar da xaiyi ya hada ido da xahra data kafe shi da idanunta, take annurin fuskarsa ya dauke dan ya manta da wata xahra a xaune. Take ya koma yareema jawad d'in da tssani yyi kicin kicin ya bata rai.


SUMYNBASH CE💋


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

YAREEMAH JAWAD

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

P. M. L. W


A romantic love story

2017


Story & written by
SUMAYYA SALEES SADEEQ


I proud to dedicate dis page 2 u guys, pure moment of life writers, tunda nake ban tab'a ganin group masu san juna da had'in kai irin sa ba, Allah y karama soyayyar juna ya d'aurar da xumuncin mu har abada. Ilysm 💞💞💞💞💞much love sisters.


Aisha Ali garkuwa, u are like mtn line now, every where u go😂😂karki damu sis daukaka ce Allah ya miki ya kuma bayyana miki makiyanki a fili, namiji baya kadan ynx aka fara sambado mana shi, ki cigaba da gashi sis muna jin dadin novel😍😍😘😘
Chapter 10 · 0% Book details