Chapter 53&54
Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Tsaf Zahra ta k'arema Zaljameel kallo, sosai ta k'ara tabbatar da soyayyar da Zaljameel kema Ya Jawad, sai dai ga dukka alamu Zaljameel bata san ta kamu da soyayyar ba. gyara zama tayi ta kalli Zaljameel tana murmushi!
"Zaljameel gaskia kinyi mini dai dai abinda kika yima Jawad, kar ki kuskura ki nuna kina tsoron sa, ina san ki dake zuciyarki ki kwaci yancin ki a wajen Jawad, karki yarda ya k'ara marinki ko da wasa, kefa macece Zaljameel, Allah yayi ki da kyan sura, gaki kyakyawa wacce duk wani namiji mai lafiya idan ya ganki sai ya yaba"
Shiru Zaljameel tayi tana sauraron Zahra, a zahirin gaskia bata gane mai Zahra ke nufi ba, murmushi tayi ta kalli Zahra "Zahra ban gane mai kike nufi ba, ki fahimtar dani a yaren dazan gane"
Daria Zahra tayi, Zaljameel kenan ke yarinya ce, kuma baki son komai ba, amma zan sanar dake yanzu ki gane kamar yarda kika buk'ata"
"Zuba ma Zahra ido Zaljameel tayi, matsowa Zahra tayi a dai dai kunnen Zaljameel ta rad'a mata wani abu dani kaina bansan menene ba! A razane Zaljameel ta d'aga kai ta kalli Zahra, fuskarta na bayyanar da tsoro," What are you saying Zahra? I can't gaskia bazan iya abinda kika fad'a ba har abada, so kike ya raina mini hankali? Gaskia bazan iyaba ki bani inason wata shawarar ba wannan ba.
Dafa k'afadar ta Zahra tayi a hankali ta fahimtar da Zaljameel, Zaljameel ta yarda da shawarar Zahra ta kuma ce zata gwada, a haka sukayi sallama ta tafi gida.
Bathroom Zaljameel ta shiga ta fesa wanka, d'aure take da towel ta nufi wardrobe, side d'in English wears ta fara dubawa dan dama tunda tazo gidan bata saka su ba. Wata ficiciyar riga yellow ta d'auka mai siririn hannu iya gwiwarta take ta kama jikinta sosai, hakan yasa hips d'in ta ya zauna das a rigar, raba gashin kanta tayi biyu, tayi 2 babies, tayi light make up, Arabian perfume ta fesa ta kalli kanta a mirror, a hankali ta furta "Wow" dan ita kanta taga irin kyan da tayi, sai dai bata tunanin zata iya fita Ya Jawad ya ganta a haka! Ta fi 15 mints a tsaye a kofar room dinta amma ta kasa fita, tsoro da fargabar abinda zai je yazo ne ya shige ta, wata zuciyar ce tace mata, "Haba Zaljameel, wannan abinda zakiyi kwatar ma kanki yanci zakiyi, kuma ai mijinki ne" Cikin dakiya Zaljameel ta mird'a handle ta fita. Kwas Kwas take taka tiles d'in parlour da wani high hill a k'afarta, fridge ta nufa ta d'auka ice cream sannan ta zauna a 2cter ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya, kallo take a mbc 3 ana Tom and Jerry tana kwasar dariya, a hankali taji an mird'a handle, Ya Jawad ne ya shigo hannunsa d'auke da briefcase da alama daga office ya dawo, kallo d'aya ta masa ta dauke kai ta maida hankalin ta ga TV, baki da hanci Ya Jawad ya saki yana kallon tsantsar kyan Zaljameel, idonsa ne ya sauka a santala santalan cinyoyinta wanda sai da ya had'iye wani yawu kut! Gaba d'aya yayi mutuwar tsaye Zaljameel ta gama kashe shi. Jin maganar Areef da friends d'insa da suka taho tare ya fargar da Ya Jawad, Zaljameel ma kam ta tsorata da jin muryar maza a baya amma ta share cuz tana son ganin mai zai faru ta cigaba da kallon TV amma a zahirin gaskia kallon take ba kirjijnta ke bugawa yarda k'artar maza zasu ganta a haka.
Matarsa Zaljameel ita maza zasu kalla a haka, nan da nan wani mugun kishi ya rufe shi, da yayi niyar barin ta mazan su shigo su ganta haka, amma gaskia bai iyawa.
Cikin wani irin zafin nama Jawad ya saki briefcase d'insa a k'asa ya nufi inda Zaljameel ke zaune, sosai buguwar kirjijnta ya k'aru tana addu'oin neman mafita a ranta,yana k'arasawa dai dai ita bai tsaya dogon zance ba ya d'aga ta chak ya nufi bedroom d'inta! A razane Zaljameel ta fara k'ok'arin kwatar kanta tana dukan kirjin sa akan ya sauke ta, "Ya Jawad me haka? Ka sauke ni bana so" bai saurare ta ba sai da ya shiga da ita room d'in dai dai nan kuma su Areef suka k'arasa shigowa dan sun tsaya gaisawa da Bala.
Jawad yak'i sauke Zaljameel, tsaye yayi tana hannunsa suna kallon kallo, wani abu sukaji yana tsarga musu tun daga kai har k'afa, idonsa ya mayar kan breast dinta da suka tsaya chak, kwayar idonsa Zaljameel tabi da kallo tana son ganin mai yake kallo, ganin yarda ya k'urama kirjin ta ido yasa ta jin kunya. sun dau wajen 5 mints a haka a hankali ya taka ya shiga sosai cikin bedroom d'in, wani sanyanyan k'amshi ya bugi hancin Jawad a hankali ya lumshe idonsa kasancewarsa mutum mai son k'amshi, kamar wanda aka tsikara yayi firgit ya dawo hanyacinsa.
direta yayi a tsakiyar gadonta, idonsa ya rikid'e ya koma ja tsabar b'acin rai, a hassale ya fara magana" Keee waya baki izinin fita main parlour da wannan shigar? "
Wani murmushi Zaljameel tayi ta kalli Ya Jawad!
" Dama sai an bani damar sa irin suturar da nake so "? tayi wani far da ido, cikin sanyin muryar ta mai dad'in sauraro ta d'aura, "Haba Ya Jawad, maiyasa kake son takurama rayuwa ne, gaskia ka fita a harkata nayi rayuwata yarda nake so cuz ban takura ka ba kaima" ta karashe maganar a ciki.
Cikin b'acin rai Jawad ya nufi Zaljameel, tashi tayi tsaye a gadon ta zuba masa idanunta masu mantar dashi damuwa, jiyay ya kasa d'aukar mataki a kanta, hakan yasa ya buga tsaki ya fita a dakin.
Wani tsalle Zaljameel tayi a bed d'in ta dire tana murna, "Yes, gaskia naji dad'in shawarar Zahra, Ya Jawad ka shiga uku, sai ka tattara kayanka kabar gidan nan dan bak'in cikin ni Zaljameel, wayarta ta d'auka ta kira Zahra ta bata labari abinda ya faru Zahra ma kam tayi murna da jin haka," yawwa Zaljameel wannan had'uwa ta farko kenan, saura ta biyu, nan Zahra ta kuma bama Zaljameel shawara amma bata bari naji ba.
A kunyace Jawad ya fita a part d'in Zaljameel cuz friends d'insa na main parlour a zaune basu shiga ciki ba, suna ganin sa suka fara tsokanarsa, "Kai mutumi na baka da dama, wato tsabar gajen hakuri briefcase d'in ma a bakin k'afa aka yarda ta, Areef ne mai fad'an haka sauran friends suka fara dariya suma.
Jawad bai iya cewa komai ba, cuz Zaljameel ta gama tayar masa da hankali, ba surutu yake buk'ata ba yana son ya huta ne kawai,zama yayi shima a parlour ya d'aura kansa a saman cushion yana tunanin Zaljameel.
Jin K'ofar part d'in Zaljameel ta motsa yasa Jawad bud'e idonsa tar dan tabbatar da hakan, jin tafiya yayi hakan yasa ya juya da red eyes d'insa suka had'a ido da Zaljameel! Sanye take da brown hijab mai hannu har k'asa, ta nufi parlour. A kusa da Ya Jawad ta zauna dab dashi tana murmushi, d'ago ido yayi ya maka mata harara Zaljameel ta maida masa da murmushi, Cikin sanyin muryar ta ta gaisa da friends d'in Ya Jawad, rintse ido yayi jin muryar Zaljameel na fita tana gaisuwa da friends, muryar matarsa a sadaka wasu suke ji, jiyay zuciyarsa na tafarfasa kamar zata cire, ganin yarda take musu murmushi Jawad yaji kamar ya rufe ta da duka ko zai huce. Mikewa tayi ta nufi kitchen dan had'a musu abinda zasu ci, cuz yanzu Anna bata fiya zuwa gidan ba, kuma kuyangun ma basu zama a gidan dasun gama aiki suke tafiya.
KUYI HAKURI DA WANNAN
SUMYNBASH CE💋🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
YAREEMAH JAWAD
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
We don't just entertain we touch the heart of the readers
A romantic love story
2017
July 2017
Story & written by
SUMAYYA SALEES SADEEQ