← Book details Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 11 OF 40

Chapter 19&20

Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

"Ajiye phone d'in sa yyi a kan table d'in gabansa, yana duba watch d'in dake d'aure a wrist d'insa, watch ne mai tsada wanda ba'a ko wane hannu ake ganinsa ba sai a wajen su yareema jawad. Bai ankara ba yaji ta kawo hannu ta d'auki phone d'insa mai tsadar gaske iPhone 8, yana kallonta ta gefen ido yyi kamar bai ganta ba.


"Operating wayar ta fara yi cikin kwarewa, ta shiga nan ta shiga chan tana ta masa bincike, number d'in ta ta saka a cikin phone d'in yareema jawad tayi dialing sim d'inta ya shiga, saving tayi masa a number d'in "Zahra" murmushin nasara tayi, "ai tunda na samu number d'inka, to xaka sha naci yareema jawad" sai ka xama mallakina, sai na aureka, tunda ina sanka ya xama dole kaima ka so ni "tunda nake a rayuwata ban tab'a neman abu na rasa ba kuma baxan fara akanka ba.


" Bata mayar masa da phone d'in ba ta cigaba da operating, gallery ta shiga, pictures d'insa ta fara gani, sanye yake da kayan sarauta, kansa sa rawani, daria yake a pic d'in, wanda ya bayyanar da kyawun yareema jawad. Wani murmushi Zahra keyi,"dama guy d'in nan jinin sarauta ne? No wonder ashe abinda ke dawainiya da shi kenan"ji tayi ya kara shiga ranta, a dunia "Zahra" nasan sarauta sai dai Allah bai basu ba. Lallai da suna da mulki da anga ixxa, Idan ta auri yareema jawad ta xama gimbiya kenan, aiko xata shinfida mulki da ko sarkin albarka. Ido na xare ina kallon Zahra dan duk burina na auren yareema jawad ta fini"lol"


"Watch d'in hannunsa ya kalla, 6:30pm amma bata bashi wayarsa ba, gashi tym d'in tafiarsa gida yyi, gashi kasaitarsa ta hanashi ko kallonta ballantana ya mata maganar phone d'inshi.


"Zahra ta lura da hakan dan haka ta cigaba da danne-dannenta a phone d'in, watch d'in ya kuma dubawa 6:45pm mikewa yyi ba tare da ya kalli Inda Zahra take ba ya fara tafiarsa cike da k'asaita irin tasu ta ya'yan sarakuna, tafiarsa yake hankali kwance ya nufi motarsa.


"Tashi tayi da gudun tatabi bayansa, please jawad ga phone d'inka, ko kallo bata ishe shi ba ya karasa jikin motarsa. Budewa yyi ya shiga xaija kofar motar ta tare da hannunta, kunnenta ta kama tana masa wani shu'umin murmushi,"kayi hakuri jawad baxan kara ba, banxa yyi da ita ya fara yiwa motarsa key, ganin yaki karba kawai tayi sauri ta xura masa a aljihun gaban rigarsa, da karfi yaja murfin motor ya bar wajen.


"A tsaye ya barta cike da mamakin girman kai irin na jawad, wato dayace ta bashi phone gwara ya tafi yabar mata phone d'in a nan. "lallai ina da aiki babba a gabana".


"Gudu yake tamkar shi kadai ne a road d'in, har ya karasa gida. A fusace ya shige gidan cike da takaicin abinda Zahra Zahraden ta masa.


" Lallai Zahra xata gane kuranta, ta sansa amma batasan halinsa ba, amma xai ganar da ita Idan bata fita a harkarsa ba, tunda yake bbu macen da ta tab'a gigin tab'a masa waya sai yau, dole ya bar London ko dan saboda tsinanniyar yarinyar nan, saboda Idan ta cigaba da bibiyarsa to kwa lallai da ita da baban nata da take takama dashi xaiyi maganin su. Tsaki yaja ya nufi bedroom d'insa dan yin wanka, saboda xufar data tsatsafo masa, bayan ya fito ya shirya tsaf kamar yarda ya saba.


"Kitchen ya nufa ya hada coffee, parlour ya dawo ya xauna ya kunna TV yana kallon news a aljazeera, bayan ya gama shan coffee ya tashi ya rufe ko ina yyi switching TV da Ac ya nufi bedroom d'insa. Light ya kashe ya rage Ac ya haye bed d'insa, blanket yaja ya rufe har kirjinsa, addu'oin kwanciya bacci yyi wanda suka xo a hisnul Muslim ya shafe jikinsa, bbu dadewa bacci ya d'auke shi.


"Da asuba alarm d'in dake kan bedside ya fara k'ara, ya saita ne cux ba Kiran sallah xaiji ba.


"Tashi yyi ya kashe alarm d'in yyi addu'ar tashi daga bacci ya nufi toilet. Alwala da wanka yyi ya fito daure da towel a waist d'insa, da small towel yana goge sumar kansa daya jik'e. A gurguje ya shafa mai ya xira jallabiya dan kar tym d'in salat d'in ya wuce, prayer mat ya shinfida ya tada sallah, bayan ya idar yyi addu'oin kamar yarda ya saba ya shafa. System d'in shi ya dakko ya fara aikin office dan baxai koma bacci ba, ranar Monday ne akwai aiki. Bayan ya gama ya nufi kitchen dan hada break fast, yareema jawad expert ne a wajen girki, tunda yaxo London da kansa yake girki, kasancewarsa mutun mai kyankyami. Ba wani abu mai wuya yyi ba Irish and egg ya soya sai tea da yyi boiling d'in shi a kettle in minutes ya kammala, bayan ya gama ya jera a dining ya duba wall watch, 7:00am ya gani dan haka a gurguje ya nufi toilet ya sake wanka yyi shirin office.


"Sanye yake da English wears kamar yarda ya saba, t-shirt ce yellow mai karamin hannu, sai trouser pencil black wrist d'insa daure da black watch, yyi kyau sosai ya nufi dining.


SUMYNBASH CE


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

YAREEMAH JAWAD


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

P. M. L. W


A romantic love story

2017


Story & written by
SUMAYYA SALEES SADEEQ
Chapter 11 · 0% Book details