← Book details Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 34 OF 40

Chapter 69&70

Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Jawad wani nishad'i yake ji jin Zaljameel rungume a kirjinsa, "Ya Jawad yunwa nake ji".


"Ok Zaljameel muje muci,an kammala break fast sai kici". Kallonsa Zaljameel tayi, "Ya Jawad waya girka?". Nine mana ya fad'a yana murmushi.


Hararasa Zaljameel tayi, "Haba dai Ya Jawad, ai nasan baka iya girki ba".

" To shikenan Zaljameel zan baki mamaki "cikata yayi ya kama hannun ta suka fita parlour, dining area ya nufa da ita," Gashi nan sai ki duba abinda ya miki " bai jira mai zatace ce ba ya nufi upstairs. Binsa Zaljameel tayi da kallo har ya b'acewa ganin ta. Ajiyar zuciya ta sauke tana jin dad'in yarda Ya Jawad ya fara chanjawa


Jawad wanka ya sake yi ya shirya cikin wata light blue shadda, half jumfa, tayi masa kyau, ya fashe jikinsa da perfumes ya d'auka key da phones d'insa ya sauka k'asa.


. Bayan ta gama break fast ta koma main parlour ta zauna tana tunanin gida, ita duk takaicin ta phone d'inta ai da tayima Zahra waya ta sama mata mafita, tsaki taja ta dan kishingid'a tana tunanin maganar Jawad, "Ba mutane kad'ai ke rayuwa a gidan nan ba" tashi tayi zaune tana duba gefenta, dan tayi matuk'ar tsorata, gani tayi parlour ya mata girma gashi kamar za'a kamata, mik'ewa tayi tana shirin fara gudu taji mutun a bayanta, a razane ta juya suka had'a ido, ganin sa a shirye yasa gaban ta ya fad'i, cikin rawar murya ta fara magana "Ya Jawad ina zaka je haka?" kallonta yayi yana mamakin abinda ya bata tsoro yayi crossing hands yana murmushi "Aurena kike da zaki tambaye ni inda zani?" Zan fita ne zaga gari, akwai matsala ne? ".


" matsala d'aya ma kenan, wallahi Ya Jawad bazaka barni a gidan nan ka fita ba, gaskia sai dai mu tafi tare, ka maida ni inda ka d'akko ni", ta fashe da kuka.


Jawota Jawad yayi ya rungume ta tsam a jikinsa yana shafa gashin kanta sigar lallashi, "Zaljameel ki zauna mana, babu abinda zai kamaki, abinda na fad'a miki d'azu I'm joking fa".


Mak'e kafad'a Zaljameel tayi "Ni dai a'a gaskia sai dai mu tafi tare" ta cigaba da kukanta, kukan dake ratsa duk wani sassa na jikin Jawad, bayason jin kukan Zaljameel ko kad'an, zama yayi a kujera tana manne a jikinsa yana jin son Zaljameel na kuma k'aruwa a zuciyarsa.

"Zaljameel ki barni naje mana, kinga baki da kayan kwarai, ko da wannan kayan na jikin ki zaki fita, kayan ma da bakisan na waye ba kika d'auka kika sa a jikin ki". Wayyo Mom! Fulani "ta fad'a a tsorace, Ya Jawad kayan waye?" naki ne Zaljameel" ya fad'a yana yana shafa bayanta "Nawa kuma?" Yeah naki mana Zaljameel , na dad'e da siyansu "


Tashi tayi a jikinsa ta kalle shi, sun dau time suna kallon juna, shagwabe fuska Zaljameel tayi," Ya Jawad ina da hijab sai na saka"


"Ha Zaljameel mai yasa rigima ta miki yawa, ni babu inda zani dake sai dai na fasa fitar" Kwantar da kanta tayi a kafad'ar sa "Yawwa Ya Jawad, haka nake so".


Shiru sukayi for some minute, a haka Zaljameel tayi bacci, kallonta Jawad yayi, kwanciya yayi ya gyara ma Zaljameel kwanciya itama a kirjinsa yayi hugging d'inta a haka bacci ya d'auke shi.


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

YAREEMAH JAWAD

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L

(We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers)


A romantic love story
2017

August 2017


Story & written by
SUMAYYA SALEES SADEEQ
Chapter 34 · 0% Book details