← Book details Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 40

Chapter 5&6

Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Xaune suke a pallow xaljamil ta xubawa mom ido tana jiran jin labarin yareema jawad. Daria mom tayi xaljamil kin cika san labari amma inasan kafin kisan jawad ki fara da sanin asalinmu gaba daya dan anan ne xaki samu labarin yareema jawad cikakke. Ajiyar xucia xaljamil ta sauke tare da gyara xamanta dan jin labarin. A hankali mom ta fara bata.


Asalinsu


Babbar masarauta ce wacce duk nigeria ba'a taba masarauta irin wannan ba, masarauta ce mai ixxa da kasaita, suna da arxiki wanda su kansu basu san iyakarsa ba, amma sun fi kauri a noma. Suna da gidajen gonaki a wajaje daban daban.


Kakanki alh Abubakar Abdulaziz ya samu sarautar a hannun mahaifinsa, bayan rasuwarsa, mutane da yawa sun yi kokarin a daura su akan karagar mulkin amma yan majalisar sarki da waxiri suka ga bbu wanda ya chanchanta sai kakanki alh Abubakar Abdulaziz da daya tilo ga sarki Abdulaziz, saboda yana da ilimin addini dana boko, kowa yyi amince da nadin waxiri dan haka a ranar da sarki Abdulaziz y rasu a ranar aka nada Abubakar grand fa dinki.


Mai martaba Alhaji Abubakar Abdulaziz yana da mata hajia aminatu wacce ake kira da fulani, ita kadaice matar kakanki yayanta maxa biyu farouq da aliyu sun tashi cikin kulawa a wajen mahaifansu har suka kammala karatunsu wanda sukayi a kasar waje. Dad dinki Aliyu shine babba sai farouqkaninsa, bayan kammala karatunsu mahaifinsu ya bijiro masu da maganar aure, dukkansu a lokacin basu da wata budurwa dan haka suka bawa mai martaba damar xabar musu matan aure. Mai martaba yyi farinciki da xabin da suka bashi dan haka ya kira Alhaji usman akan ya nasan ganinsa. Baiyi kasa a gwiwa ba ya nufi gidan sarki dan amsa kiran amininsa.


Xaljamil ce ta kuma gyara xamanta ta kalli mom fuskarta dauke da murmushi da alama labarin yana matukar birgeta, mom ki cigaba bana san dad ya dawo baki karasa mini ba, daria mom tayi ok bani ruwa a fridge sai mu cigaba. Da sauri xaljamil ta mike ta nufi fridge ta daukowa mom ruwa ta taho da cup ta xuba mata ta mika mata, karba mom tayi ngd xaljamil, aiki nane mom na kula dake ta fada tana murmushi.

Mom na shanye ruwan ta ajiye cup din a gefe,mom wanene Alhaji Usman aminin sarki? Murmushi mom tayi, mahaifi nane. Ok nagane xaljamil ta fada tana jiran mom ta cigaba.


Alhaji Usman ya je kiran da sarki ke masa, bayan sun gama hirar su ta abokai mai martaba ya nemawa aliyu da farouq auren ya'yan alhaji usman aysha da maryam, ba tare da bata lokaci ya amince ya kuma shaidawa sarki shi mai bada auren ya'yan ne. Sosai sarki yyi farinciki dan yasan aliyu da farouq sunyi dacen mata masu hankali da tarbiyya.


Xaljamil ce ta kalli mom, su waye aysha da maryam, ni da kanwata mom ta bata ansa, gyada kai xaljamil tayi alamar gamsuwa, ok mom cigaba.


Farouq da Umar sun yi na'am da xabin sarki dan haka sarki ya saka musu albarka ya kuma shaida musu ba dadewa xasuyi ba xaayi auren.


Alhaji Usman da fara'arsa ya nufi gidan sa ya shaidawa matarsa hajia fatima, itama tayi murna dan tasan xumuncin su da fulani ya karu bayan amintaka ga kuma surukuta.

Abbanmu ta bawa maman mu akan tasanar damu xabin daya mana, bbu musu muka amince dan bama iya yiwa mahaifan mu musu.


Sosai aka fara shirye shirye a fada da cikin gida, bikin yayan sarki su biyu. Muna munyi shiri sosai dan mahaifin mu ya fitar damu kunya. Bayan bukukuwa na alada aka saka mu a lalle aka daura aure ko wacce aka kaita gidan mijin ta da aka gina a gidan sarki. Ni aysha aka aurawa aliyu kanwata maryam aka aura mata farouq.


Sosai maxajen mu ke bamu kulawa ana haka maryam ta samu ciki, sosai gidan sarautar ya dauki murna har karamin biki aka hada a gidan nima nayi murna sosai haka ma aliyu. Cikin maryam ya shiga wata tara ta haifi danta namiji.. Mom ce ta kalli xaljamil data kara nutsuwa danjin yarda xata kasance, murmushi mom tayi a tunaninki wane irin budiri xaa yi da haihuwar baby boy a gidan sarki. Murmushi xaljamil tayi eh lallai kam tunda a samun ciki ma anyi bidiri ballantana a haihuwa.


Ranar suna aka sakawa yaro suna jawad, anyi kade kade da bushe bushe irin na gidan sarauta an yi hawan dawakai duk saboda murna, sarki Abubakar yyi gayyata har abokansa na kasar waje a cikin su harda sarauniyar england, sarauniyar england
? Xaljamil ta fada mamaki bayyane a fuskarta. Kwarai kuwa kuma ta halarci wannan ranar, dan nima a ranar na fara ganinta. A jiyar xucia ta sauke eh lallai jawad dan gata, daria mom tayi gaskia kam dan gata, dan ya samu kyaututuka na gidaje da filaye harda wanda ya dauki
nauyin karatunsa har ya gama.


Tunda aka haifi jawad ka bashi kuyangu masu kula dashi, amma ni a wajena yake wuni, ina kaunar jawad sosai ina kuma kula dashi kamar dan cikina. Hakan yasa maryam ta dauke kanta a kan jawad dan tana tausayamin na rashin haihuwar da banyi ba.


Jawad ya girma har an sakashi askul amma ni shiru bbu ciki bbu alamunsa, mahaifiyata ma abin ya fara damunta duk da aliyu bai taba nuna damuwarsa akan hakan ba, amma ni kaina ina san naga na haifi baby na.


Kwanci tashi bbu wuya a wajen Allah jawad ya kallama yana primary skul yana shirye shirye tafia secondry. A lokacin mai martaba ya bawa aliyu shawara akan muje kasar waje dan duba lapiyata ina haihuwa ko banayi, aliyu kam ransa ya baci har mai martaba ya lura da hakan ya kuma sanar da mai martaba bbu inda xamuje muna jiran ranar da Allah xai bamu. Sosai dad dinki ya kasa xaman nigeria, dan yana ganin kamar ina xaune ne a cikin damuwa saboda rashin kulawar da bana samu a gidan sanadiyyar rashin haihuwar da banyi ba. Muna xaman mu sai dad dinki ya samu aiki a qatar, da kyar mai martaba ya yarda, shiri sosai muka fara a tym din jawad na ss1.


Aliyu ya kaini gida mukayi sallama da mamana da babana suka mini fatan alkhairi,.a daren na shiga wajen fulani da mutan gidan nayi Sallama dasu dan gobe da safe xamu wuce. Jawad kam xama yyi a part dina yana kuka wai saina tafi dashi qatar da Ni kaina saida nayi kokan rabuwa da jawad saboda shakuwar da suka yi kyar aka lallashe
hi akan xamu dawo mu tafi dashi.


Mom ce ta kalli xaljamil kinji yarda muka rabu da yareema jawad, a jiyar xucia xaljamil ta sauke mom ki cigaba ina jinki. Ok habibty! Da asuba muka bar gidan sarki aka kaimu airport, karfe 8:00 jirgin mu ya tashi sai qatar. A gidan nan muka sauka sai da muka huta sannan dad dinki ya tafi yyi reporting ya sanar da xuwansa.


A kwana a tashi mukayi 3 month a qatar, rashin lapia na farayi sosai kamar baxan yi ba, hankalin dad ya tashi harda kuka, daria xaljamil ta fara harda rike ciki, eh lallai soyayya, hararata mom tayi eh ai kadan ma kikaji. uhum romeo nd juliet ta fada tana daria. Hmmmm mom tayi murmushi,, muna xuwa hospital doctor ya tabbatar mana da ina da ciki wata 2,wani tsalle dad ya biga a office din ya fara rawa, doctor din daria kawai yake masa. Kudin dake jikinsa gaba daya ya cire ya bawa doctor.


Muna dira gida aliyu ya fara bige bigen waya yana sanar da yanuwa da abokanan arxiki. Mai martaba sai da yaxo qatar ya ganni shida fulani da maryam da farouq, amma baaxo mini da jawad ba dan kar ya makale,.


Sallama dady yyi ya shigo pallon, duk da xaljamil taji dadin dawo warsa amma bata ji dadi ba dan tasan anan labarin xai tsaya. A gurguje suka shirya dan flight din ya kusa tashi suka nufi airport.


SUMYNBASH CE 💋

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

YAREEMAH JAWAD

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

P. M. L. W


A romantic love story

2017


Story & written by

SUMAYYA SALEES SADEEQ
Chapter 4 · 0% Book details