Chapter 43&44
Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Zama Jawad yyi a kujerarsa da irin babbar nan ta sarauta, wani irin annushuwa yake ji aransa, yau dream d'insa ya tabbata, ya mallaki Zaljameel cikin sauk'i, bai tab'a tunanin hakan ba, gaskia grandfa ya masa k'ok'arin da bazai da hakan ba, a hankali ya furta
"luv u grandfa, how will i forget u in my life ka min komai a rayuwata".
Fuskarsa ya d'aga sama yana kallon ceiling, ya lumshe idonsa fuskar sa d'auke da murmushi.
Sallama Bala yyi a parlour, ganin Yareema Jawad zaune a karagarsa yasa ya k'arasa, a gaban sa ya zauna a k'asan k'afarsa. Fara'a ya fara magana!
"Barka da hutawa ranka ya dad'e"
"Barkan ka dai Bala" ya fad'a fuskar sa d'auke da murmushi.
Mamaki bayyane a fuskar Bala, dan rabon da Jawad ya k'ira sunan sa har ya manta, hakan ya bashi damar cigaba da zancen sa! Ina taya ka murnar Aurenka, ina rok'on Allah ya baku zaman lpy kaida gimbiya Zaljameel, ya azurtaku da salahan ya'ya masu biyayya ga iyayen su"
Wani dad'i ya ratsa zuciyar Jawad, Bala bai tab'a faranta ransa ba sai yau, tunda Bala ya fara magana idonsa a rufe yake, dag'o kai yayi had'e da gyara zaman sa, tar ya d'aura idonsa akan Bala dake zaune! Sai da yyi wani murmushi sannan yace!
"Bala na 'yanta ka na kuma biya maka aikin hajji, na d' auki dawainiyar aurenka na kuma baka gidan da zaka zauna, kai na daban ne yanzu a wajena, tunda aka d'aura mini aure Areef shine wanda ya fara faranta ta raina da kyakkyawan labari, sai kai Bala"
Mutuwar zaune Bala yayi dan jinin dake jikinsa jiyay ya daskare, anya abinda kunnensa yaji gaskia ne?D'aga ido yayi ya kalli Jawad wanda shima d'in Bala yake kallo, Bala gani yay kamar maganar ba daga bakinsa ta fita ba, tsantsar mamakin da Jawad ya gani a fuskar Bala yasa ya nanata masa abinda ya fad'a a baya.
Fashewa da kuka Bala yayi dan bakinsa ya gaza gode ma Jawad, kuka sosai Bala yayi ba tare da Yareema Jawad ya lallashe shi ba, sai da yayi mai isarsa sannan ya fara magana muryarshi a shak'e!
"Ranka ya dad'e godia nake, duk da bakina ya rasa kalmaomin da zanyi amfani wajen gode maka, akwai alfarma da zan nema a wajen ka, Dan Allah ka barni a matsayin bawanka, ina son na dawwama ina maka hidima, bana son rabuwa dakai ranka ya dad'e.
Cikin kulawa Jawad ya d'auke idonsa akan Bala ya maida part d'in Zaljameel, ji yake inama zata fito ya ganta, Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya fara magana!
"Muna tare Bala, bbu wanda zai iya d'aukar dawainiyata sai kai, kasan komai nawa, dakai kad'ai na yarda, ina ganin' yanta ka ba matsala bane".
Bayan ya gama yi ma Jawad godia ya nufi bedroom d'insa dan had'a masa ruwan wanka.
Zaljameel zaune a d'akinta, tana jiran shigowar Areef da friends d'insa dan taji muryar su, jin shiru yasa ta sauke mayafin kanta tana k'arema d'akin kallo, babban d'akine an masa decoration da Arabian furniture, design d'insu irin na sarauta ne,gefe cushion ne white colour an masa ado da golden, sunyi kyau, a gefe wata shegiyar plasma ce bango d'aya ta cinye, kamar ta fad'owa mutum dan girma, a hankali Zaljameel ke bin d'akin nata da kallo, gaskia iyayen ta sunyi k'okari.
Wall clock ta kalla, 11:56pm hankalinta ya tashi, to ina Areef ya shiga? Ni sumy nace yana wajen matarsa suna rak'ashewa. Lol
Wasa wasa bbu Areef bbu alamunsa, ganin haka yasa Zaljameel ta fara shirin bacci, kayan jikinta ta cire ta nufi toilet dan yin wanka.
Bayan ta fito ta shirya cikin wasu tsadadden sleeping dress red colour, silk ce, rigar iya gwiwa tabi jikinta ta lafe,duk surorin jikinta ya bayyana, a hankali ta taka gaban standing Ac ta rage ta nufi bed ta kwanta, tunanin inda Annah take Zaljameel ta fara yi, badai Annah ta tafi ba, dan bata tunanin akwai wanda yayi saura a gidan, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ina Areef ya shiga? Anya bazata kira gida ta sanar dasu ba, wata zuciyar tace ki bari anjima ko akwai abinda ya tsare shi bai shigo da wuri ba, phone d'in ta ta jawo ta hau online, messages ne suka fara shigo mata na congratulations, a wani group da take ciki, na class mate d'in ta dake Qatar.
Ta gama yi musu reply ta sauka zuciyar ta fal damuwa, dan ma Zaljameel bata da tsoro hakan yasa tayi kwanciyarta tana jiran dawowar Areef, a haka bacci ya d'auke ta.
Areef da Zahra kam sun raya daren su sosai cikin farin ciki da k'aunar juna, da yake Zahra duk wayewar ta bata tab'a yarda wani d'a namiji ya kusanceta ba, hakan yasa Areef daya dan tab'a bariki ya birkice mata gaba d'aya, su Zahra ansha kuka kamar rai zai fita, sai da suka raya daren sannan suka yi bacci.
The next day
Jawad ya tashi da asuba yayi wanka ya shirya cikin jallabiya ya fito zai nufi masjid, kamar yarda suka saba yana fitowa yaci karo da Bala a tsaye yana jiran fitowarsa, d'urkusawa Bala yayi ya gaida Jawad, bayan ya amsa masa cikin kulawa suka nufi masjid.
Bayan sun idar Yareema Jawad ya hango grandfa a gefe yana tasbihi, wajensa ya nufa fuskar sa d'auke da fara'a.
Grandfa na ganin Yareema Jawad ya nufeshi yayi kicin kicin da fuska, ganin hakan bai hana Jawad k'arasa wa ba.
A gabansa ya zub'e yana dariar ganin yarda grandfa ke cin magani, zama yayi a kusa dashi ya fara gaida shi!
"Grandfa nawa ni kad'ai"
Harararsa Grandfa yayi!
"Ina kabar Zaljameel? Da zaka ce naka kai kad'ai ".
Daria Jawad yayi dan dama yasan zasu fafata da grandfa, saboda abinda ya masa, sai da yajanyo yayi rashin lpy.
" Dan nema! Wato kana so kana kaiwa kasuwa ko? Yanzu badan na tubure ba da tuni ka rasa farin cikin ka ko? Zaljameel alheri ce a tare da kai na dad'e da gane hakan, burina ya cika Jawad dama shi kad'ai ne ya rage mini a duk buri kana, sai kuma fatan na cika da imani.
Cikin barkwanci Jawad ya bawa grandfa hak'uri, abinka da jika da kaka tuni grandfa ya saki jiki sukayi magana da Jawad.
Nasiha sosai grandfa ya masa akan ya rik'e Zaljameel da amana, ya bata duk wata kulawa data kamata, nasihar ta ratsa Jawad sai dai a zuciyarsa bashi da wani buri da zai bama Zaljameel damar shiga rayuwarsa, kamar yarda yayi alkhairi bazai tab'a bayyana mata yana sonta ba, yanzu ma kam haka za'ai, lokacin bayyana mata soyayya baiyi ba, so yake sai ta gama kamuwa da sonsa shima dan zata fi sanin darajar sa, sallama yayi ma grandfa, anan grandfa ya bashi sak'on gaida Zaljameel.
SUMYNBASH CE💋
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
YAREEMAH JAWAD
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
A romantic love story
2017
July 2017
Story & written by
SUMAYYA SALEES SADEEQ
I proudly to dedicated dis page 2 u guys u are so special in my heart.
Aishat A Muh'd (Aunty)
Aunty cute Zahra Bukar
Ummi hambali
Rahma(momyn sultan)
Faridat sweery
Maryam s bello
Maryam Abdul
Hafsat musa(indon k'auye
Aunty kausar
Aisha Ali garkuwa
Feedy luv
Dama sauran wanda ban fad'a ba, duk ina sonku.
Ina kike Aunty na
Zahra Uba Leader
Ina matuk'ar alfahri dake ina kuma godia da k'aunar da kike nuna ma littafin yareema jawad, # much love 💋