Chapter 68&69
Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Gidan sarki Jawad ya nufa, hankalin sa kwance, tun a gate ya lura da yanayin masu gadin gidan yasan babu lpy, tsayawa yayi suka gaida shi, a dak'ile ya amsa ya tambaye me ke faruwa, d'aya daga cikin su ya bama Jawad labarin b'atan Zaljameel, baice dasu komai ba yaja motarsa da k'arfi ya k'ure speed ya nufi part d'in Fulani. Cikin tashin hankali Jawad ya shiga parlour yana kiran Fulani, Ammi nah! Ammi nah!, zumbur Fulani tayi ta mik'e daga zaunen da take tana kuka ta nufi inda taji muryar Jawad, har tuntub'e tayi ta fito.
Tsaye ta tarar da Jawad ya rik'e kansa yana hawaye, sororo tayi tana kallonsa dan ita ta gama believing Zaljameel na tare da Jawad, to mai yasa taga yana kuka.
Inda take tsaye Jawad ya nufa ya rumgume Fulani ya fashe da kuka, "Fulani wai Zaljameel ta b'ata, wannan wane irin tashin hankali ne yazo mana da rana tsaka, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ya Allah ka bayyana mini Zaljameel" ya kuma fashewa da kuka.
Duk da haushin da Fulani keji na Jawad sai da ya bata tausayi, amma ta dake, a zafafe ta ture shi a jikinta, tana nuna sa da yatsa, "Kul Jawad, karka kuskura ka k'ara zuwa kusa dani, bana son ganin ka Jawad, har kana da bakin kuka saboda rashin ganin Zaljameel, gaskia Jawad rashin kunyar taka takai, duk abinda ya samu Zaljameel da hannun ka a ciki Jawad, wallahi indai kaga na sakar maka to Zaljameel ta dawo gare ni da dan dake cikin ta, tun wuri Jawad, tun raina bai b'aci ba ka dawo da Zaljameel, nasan kai ka d'auke ta.
A razane Jawad ya d'ago ya kalli Fulani, sosai kirjinsa ya buga dan yayi tunanin asirin sa ya tuno, amma ya basar.
"What?! Fulani what are you saying, kina nufin nasan inda Zaljameel take? Ba haka bane Fulani, nasan nayi kuskure na korar Zaljameel da nayi wallahi Fulani ina son Zaljameel ina kuma son abinda ke cikin ta dama sharrin shed'an ne, amma bani da sa hannu a b'atan ta "Jawad ya durkusa ya cigaba da kuka.
Binsa Fulani tayi da kallo, Jawad na kuka, abinda ta dade bata gani ba kenan, a kalaman sa ta tabbatar da gaskiar sa, to ina Zaljameel ta shiga, shine tambayar data damu Fulani,ja da baya tayi ta zauna a karagarta jin kanta na juyawa. Jawad ta kalla, "Jawad! Kamar yarda na fad'a maka baka fa sauran sakewa a gidan nan in har Zaljameel bata dawo ba, na d'aura maka alhakin neman Zaljameel duk inda ta shiga a duniyar nan" tana gama fad'in haka ta mik'e tabar Jawad a durk'ushe, mik'ewa yayi ya fita, direct part d'insa ya nufa zuciyarsa fal farin ciki, Allah ya taimake shi shima zai bar gidan, dan dama yana ta tunanin yarda zai dinga zirga zirga daga gidan sarki zuwa gidansa inda ya ajiye Zaljameel, room d'insa ya shiga ya kira Bala akan ya had'a masa abinda yake buk'ata.
Mamaki bayyane a fuskar Bala, ganin yarda Yareema Jawad ya nuna halin ko in kula da b'atan Zaljameel, sanin halin Jawad bayason shishigi a lamarinsa yasa Bala ya kama bakinsa, ya had'ama Jawad kayansa ya fita kawo masa dinner.
Washe gari
Ana idar da sallar asuba Jawad ya bar gidan. Gidan sa ya nufa ransa fes zaiga Zaljameel.
Horn yayi gate man ya bud'e masa, parking motar yayi ya shiga ciki,sai fara'a yake.
Tunda Jawad yabar gidan Zaljameel bata tashi ba, baccin ta kawai take cikin kwanciyar hankali.
Jawad na shiga upstairs ya haye, ya nufi room d'in Zaljameel, yarda ya barta haka ya same ta,sai dai ta yaye blanket d'in, tayi d'ai d'ai tana bacci, gashin kanta ya rufe mata fuska. Murmushi Jawad yayi ya nufi bed idonsa na kanta, duba ledar daya kawo mata yayi, komai na nan,hakan ne ya tabbatar masa da Zaljameel bata farka ba, juye juye Zaljameel ta fara alamun zata tashi a bacci, hakan yasa Jawad ya fita a room d'in da sauri, yana fita Zaljameel na bud'e ido, gani tayi gari ya waye hakan yasa tayi du'a ta mike ta shige toilet.
Wanka tayo ta fito tayi sallah ta nufi mirror tayi shafa da light make up ta nufi wardrobe, sai a time d'in ta lura da kayan gaba d'aya new ne, hankakinta ne ya kwanta hakan yasa ta kuma duba kayan ta d'auka wata red gown mai k'aramin hannu iya gwiwa, ta gyara kanta, zama tayi a sofa ta buga tagumi dan ta fara jin yunwa, idonta ne ya sauka a kan ledojin da Jawad ya ajiye ga kuma paper kamar an bar Note, tashi tayi ta nufi wajen, letter d'in ta fara karantawa sannan ta fara bud'e kayan, gas chicken ne guda biyu, sai yoghot guda biyu shima,d'ayan kuma kayan chocolate ne da sweet,murmushi Zaljameel tayi, "Ha Ya Jawad kenan, ana so ana kaiwa kasuwa". Sai a time d'in ta tuna bacci ya d'auke ta ne a parlour, to waya kawota kan bed, "Ya Jawad" ta fad'a tana murmushi, tashi tayi ta nufi kasa ko zata ga kitchen, ta dan gasa chicken d'in a macro wave.
Jawad zaune a parlour yana watching film a mbc bollywood , Bajrangi baijaan, film d'in ya masa kyau ya bada duk wani attention nashi, hannun sa d'auke da hot coffee yana sha.
Jin k'amshin turaren Zaljameel yasa Jawad juyawa da sauri, itakam bata lura dashi ba ta fara neman kitchen, ganin ledar dake hannun ta yasa Jawad gane inda take nema, murmushi yayi ya mik'e ya nufi inda Zaljameel ta nufa cuz ba hanya bane. Tafia take tayi tana zare ido, cuz ta fara ganin kamar tabi wrong way dan ta rasa kitchen, wani door Zaljameel ta bud'e tana lekawa taga duhu, gashi tana ganin alamar mutun a ciki, gani tayi kamar mutun d'in ya nifo ta, ai da sauri daja door d'in ta kwalla k'ara ta fara neman hanyar gudu,gudu take sosai tana kuka tana kiran Jawad "Ya Jawad! Ya Jawad! Please need ur help. Ji tayi tayi karo da mutun wata razanar niyar kara Zaljameel ta kwala ta fara k'ok'arin kwace kanta, hugging d'inta Jawad yayi yana shafa bayan ta" Relax Zaljameel its me Jawad ".
Jin muryar Jawad yasa Zaljameel ta kara shigewa jikinsa tana sauke ajiyar zuciya. Shafa bayan ta Jawad ya cigaba dayi, ji tayi wani yarr a jikinta haka shima, fara kokarin kwace kanta tayi amma Jawad yak'i bata dama, sai da tayi tayi ta gaji sannan ta hak'ura ta d'aura kanta a kirjinsa tana jin bugun zuciyarsa. Perfume d'in da ta saka yayi ma Jawad dad'i hakan yasa ya fara shinshina wuyanta yana shakar k'amshin ta, kissing dinta ya fara yi tako ina har ya sauka a kan lips d'inta nan ya fara sha. Jikin Zaljameel banda rawa babu abinda yake yi, Jawad kam ya birkice sai kissing d'in ta yake, cika lips d'in yayi ya kuma hugging din Zaljameel yana buga bayan ta, saboda kukan da take.
"Please Ya Jawad ka sake ni yunwa nake ji". Banza ya mata ya kama hannun ta suka fara tafiya, "Ina kike nema?".
Kallonsa tayi taga kamar bashi yayi maganar ba cuz hanya kawai yake kallo.
D'auke kanta tayi, "kitchen nake nema"
"To gidan ki ne da bazaki nemi mai gidan ki tambaye shi ba, kinsan kuwa ba mutane ne kad'ai ke rayuwa a gidan nan ba amma kika fara shiga inda bai shafe ki ba,da banzo ba Zaljameel kinsan mai zai faru?".
Rike Jawad tayi kam tana girgiza kai, please Ya Jawad take me home, ina son ganin Fulani da Mom, nasan basu san da zamana a nan ba, please ka dauke ni a gidan tun wani abu bai same ni ba, bazan iya zama ba"ta fashe da kuka.
Hugging dinta yayi, jin tausayinta yayi aransa, "Zaljameel keda da Mom da Fulani sai ranar da nai miki ciki ya fito ya zama k'ato kika haife dan dake cikin ki sai muje gare su, a tunanin ki wace irin murna zasuyi?"
A firgice Zaljameel ta kalli Jawad tana hawaye, "Ya Jawad kasan mai kake fad'a kuwa? Please karka mini haka, wallahi zaka kuntata rayuwata, komai na duniyar nan zai daina mini dad'i, taya zan fara rayuwa a gidan nan ni kad'ai Ya Jawad a tunanin ka ka mini adalci?"
D'ago fuskarta yayi ya had'a ta tasa, "I'm here for you Zaljameel, karki damu da komai kinji" Yarda ya mata magana ya bata mamaki d'aga kai tayi ta kalle sa, shima ita yake kallo,sun dau lokaci a haka, sannan Jawad ya hura ma Zaljameel iska a idonta, lumshe idonta tayi tana jin wani sabon yanayi na shigarta,mai da kanta tayi kan kirjinsa tayi luf.
SUMYNBASH CE💋
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
YAREEMAH JAWAD
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
(We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers)
A romantic love story
2017
August 2017
Story & written by
SUMAYYA SALEES SADEEQ