← Book details Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 16 OF 40

Chapter 31&32

Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Zaljameel xaune a parlour, sanye take cikin top and jeans, gashin kanta baje a bayanta, light make up tayi, hannun ta dauke da jotter tana duba karatun da areef ya mata, taunar chewing gum take ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya, mom xaune a gefenta tana watching film, Nawal ta tafi part d'in fulani, phone d'in Zaljameel ya fara ringing, cikin zumud'i ta d'auka wani k'ayattacen murmushi tayi sannan tayi picking call d'in. Kallonta Mom tayi tana nazarin farin cikin daya ziyarci babyn tata.


Cikin muryarta mai dad'i ta masa sallama, sai da ya lumshe idonsa ya bud'e a hankali, ajiyar zuciya yayi wanda ta daki dodon kunnen Zaljameel, "wa'alaiki salam sarauniyar kyawawa, murmushi tayi, cikin shaukin so areef ya kira sunanta," Zaljameel "yarda yaja sunan nata ya bala'in birgeta..

" Sarauniyar kyawawa Zaljameel, ina sanki,ina matukar kaunarki, burina bai wuce ki amince da soyayyata ba ni kuma na bayyana miki tsantsar kauna Zaljameel" Duk da tana san Areef sai da taji zuciyarta ta buga, bazata ce bata sansa ba tunda bata san so ba amma tasan tana jin feelings a kansa, "Kinyi shiru Zaljameel, ina san na sanar da jawad akan maganar ya kika gani? " ras taji gabanta ya fad'i jin an ambaci Jawad, "Jawad" ta maimaita a ranta,"Yeah Areef ka sanar dashi," dam gaban Mom ya fad'i" mai Zaljameel ke shirin yi? Badai Areef zata bawa dama ba"shiru tayi tana kallon Zaljameel." Ok my dear insha Allah yau zamuyi magana dashi naji yarda za'ayi, dan ina buk'atar ganin ki a kusa dani Zaljameel " murmushi tayi ta lumshe ido ta bud'e, jin ta take kamar ba itaba bata tab'a tunanin a kwai wani wanda zata so ba, amma yau gashi har ta amince da wani. Sallama sukayi cikin shaukin so, cikin nutsuwa Zaljameel ta hang up d'in call d'in sai a lokacin ta tuna da Mom a parlour, ji tayi kunya ta kamata ganin Mom na kallon ta , hannu tasa ta rufe fuskarta tana daria mara sauti, zumb'uru baki Zaljameel tayi cikin shagwaba, "kai Mom mai yasa kike kallona" murmushi Mom ta k'irkiro


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

YAREEMAH JAWAD

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


Pure moment of life writers
p. m. l. w


A romantic love story
2017


July 2017


Story & written by

SUMAYYA SALEES SADEEQ
Chapter 16 · 0% Book details