← Book details Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 24 OF 40

Chapter 49&50

Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

A gigice Zaljameel ta d'aga kanta hannun ta dafe a kumatun ta, hawaye ne masu zafi suka fara zarya a fuskarta, tunda take bata tab'a ganin anyi mari a gaban ta, amma yau ita aka mara, kuma ba Mom ba ba Dad ba, Jawad wanda Mom d'in ta ta bata labarin irin k'aunar da yake mata.

Cikin dauriya Zaljameel tace, "Marina fa kayi Ya Jawad?"

A hassale ya kalle ta," An mare ki d'in, ko zaki rama ne? "ya cigaba da magana.

Keeeeee.... Zaljameel kike ko wa? Daga rana irin ta yau karki kurkura ki sake gangancin fad'an magana, wanda ya fiki ma yayi kad'an ballantana ke da wata hausar ta kamar an mata dole sai tayi, yana kaiwa nan ya ja tsaki ya fice a d'akin ransa a mugun b'ace.


Fad'awa bed d'in ta tayi ta fashe da wani irin kuka na ban tausayi, mai yasa parent d'in ta suka mata haka, wane irin laifi ta musu da suka hanata Areef suka d'aura mata aure da Jawad ? mai yasa Anna tayi mata k'arya?.

Duk tambayo yin nan Zaljameel ta rasa ansar su, hakan yasa ta tashi ta nufi parlour inda taji muryar Anna da Nawal.


Yareema Jawad na shiga bedroom d'insa ya saka ke ya zauna akan sofa ya dafe kansa da hannu biyu, tuna marin da yama Zaljameel yayi da hawayen daya zuba a fuskarta saboda shi. Runtse ido yayi yana jin zuciyarsa na tafasa mik'ewa tsaye yayi dan jiyay zaman ya gagare sa, hannun sa ya kalla, yana jin kamar ya cire hannun, wannan hannun shi ya mari Zaljameel! Sunshine d'insa,no...... Ya furta da k'arfi ya sake zama a sofa yana mai da numfashi, yayi dana sanin abinda ya aikata,a hankali ya mike ya nufi bathroom.


Annah tsaye a kitchen tana had'ama Zaljameel dinner, ita da Nawal sai hira suke, ji sukai an bankad'a kofar kitchen d'in, a firgice Annah ta juyo, ganin Zaljameel da hawaye a fuska yasa kirjin Annah ya buga, barin abinda take yi tayi ta nufi Zaljameel hankalinta a tashe, zub'ewa Zaljameel tayi a k'asan kitchen d'in ta zauna dab'as, Annah na zuwa ta lura da fuskar Zaljameel da tayi ja ga kuma alamar hannu, abinka da farin mutum. Cikin kid'ima Annah ta durkushe gaban Zaljameel tana tambayar ta wanda ya mareta,Nawal ma zama tayi a jikin Zaljameel ta fara kuka.

"Gimbiya Zaljameel waya mare ki?"

Cikin sheshek'ar kuka Zaljameel ta fara yima Annah magana!

"Annah, dama Ya Jawad aka aura mini ba Areef ba?" Dam kirjin Annah ya buga ta kalli Nawal da hawaye ya wanke mata fuska "Nawal je parlour ki zauna gamu nan zuwa" Badan ranta yaso ba Nawal ta nufi parlour tana share hawaye.


Gumi ne ya tsattsafowa wa Annah ta, bata damu ta share ba ta fara bayani, "Eh Zaljameel shi aka aura miki"

"Annah dake aka Had'a,baki aka aura mini Jawad, Anna mai yasa baki fad'a mini ba na nemi yanci na tun kan a d'aura mana aure da azzalim.......Anna bata bari Zaljameel ta k'arasa ba ta rufe mata baki, Allah ya huci zuciyar Gimbiya, karki manta Jawad mijin ki ne yanzu, magana irin wannan bata dace ki fad'a masa ba, ina jiye maki fushin Allah.


Kallonta Zaljameel tayi cike da tuhuma,"Annah da wane suna ya kamata na rika shi banda hakan?, Anna tunda aka haife ni ba'a tab'a marina na ba sai yau da Ya Jawad ya mare ni"


Shiru Annah tayi, "Jawad d'in ya mare ki,?" E Annah "Zaljameel ta fad'a ta d'aura hannun ta a fuskarta tana tuna saukar hannun Jawad a fuskarta.


KUYI HAKURI DA WANNAN ZAN MUKU TYPING MAI YAWA INSHA ALLAH.


SUMYNBASH CE💋


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

YAREEMAH JAWAD

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L


A romantic love story
2017


July 2017


Story & written by

SUMAYYA SALEES SADEEQ


Kuyi hakuri my fan's, akan jina shiru da kukayi kwana 2, hakan ya faru ne sanadin uzuri da ya sha kaina, duk da ban gama ma amma wannan page d'in naku ne dan sanya ku nishadi.💃🏻 Ilysm ❤
Chapter 24 · 0% Book details