← Book details Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 14 OF 40

Chapter 27&28

Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A fusace yareema jawad ya nufi part d'insa, banda tafasa bbu abinda xuciarsa keyi, banka k'ofar shiga part d'insa yyi da k'arfi, bala dake xaune yana kallo ya mik'e a firgice yana duba hanya, ganin yareema jawad a fusace yasa ya tattaro nutsuwarsa yabi shi da idanu, jawad kam baibi takan bala ba ya nufi bedroom. Jikin bala yyi sanyi dan yasan ba k'aramin abune ke tafarfasa ran yareema jawad ba, bai kammala tunanin abinda ya samu jawad ba yaji an sake banko k'ofar, da sauri bala ya juya dan ganin mai shigowa, areef ne fuskarsa d'auke da murmushi, wajen bala ya nufa "ina sarkin rigimar yake?" nuni bala ya masa da hannu xuwa d'akin jawad, dan haka da sauri ya nufi d'akin.


"A tsaye ya taradda yareema jawad, sai safa da marwa yake, bak'in ciki da takaicin zaljameel ya masa katutu a xuciya, tunanin yarda xai ladaftar da ita yakeyi, dole sai ya ganar da ita ynx ba a Qatar take ba a Nigeria take, baisan da shigowar areef ba sai jiyay ya dafa kafad'arsa, yasan waye dan haka yak'i juyowa, wani bak'i yaji xuciarsa tayi ganin areef, duk shi ya jaxa masa wannan b'acin ran, da bai ce xaije duba zaljameel ba ai da haka bata faru ba.


"Haba yareema jawad dan sarki guda d'aya tilo, yareema mai jiran gadon mulki, "cikin lion voice jawad ya bugawa areef wata tsawa," is ok areef, please leave me alone, mai kake buk'ata kuma bayan jawowa dakai aka b'atan rai"harara ya kuma makawa areef sannan ya xauna a gefen bed d'insa, dafe kansa yyi dan jiyay yana sara masa, bayasan b'acin rai shiyasa baya shiga sabgar kowa. Murmushi areef yyi ganin yarda yareema jawad yad'au xafi, dan haka ya yanke shawarar tafia ya bashi waje ko ya samu sanyin xucia.


"Natafi jawad sai gobe"areef ya fad'a bayan ya nufi k'ofa, jawad bai d'aga kansa ba ballantana areef yasa rai xai tanka masa, fita yyi yaja k'ofa. Bala na tsaye bakin k'ofa yakasa shiga d'akin, ganin areef ya fito yasa shi gyara tsayuwa, yallabai mai ya samu uban d'akina, murmushi areef yyi, "kasan jawad d'an rigima ne sai da lallaba, so shida zaljameel ne yarinyar uncle aliyu," nan areef ya kwashe labarin abinda ya faru ya fad'a ma bala, ajiyar xucia bala ya sauke "na gode yallabai, ynx ina xakaje?" gida"areef ya fad'a yana tafia,"ka gaida gida yallabai "ok bala nagode".


"Da sallama bala ya shiga d'akin, yareema jawad bai amsa masa ba dan haka ya nufi toilet dan had'a masa ruwan wanka, bayan ya kammala ya sanar dashi,still yareema jawad bai amsa masa ba dan bayasan magana mikewa ya yi ya nufi bathroom d'in. As usual Bala ya d'aukowa yareema jawad kayansa ya ajiye gefen bed ya nufi kitchen dan had'o abinci.


" Yareema jawad, shirye yake cikin English wears, blue jeans and orange shirt, kansa d'auke da P cap ya bala'in yin kyau, watch d'in dake d'aure a wrist d'insa ya duba, bedside ya nufa ya d'auki phone d'insa da key d'in mota ya nufi parlour, cin karo sukayi da Bala hannunsa d'auke da tray, murmushi Bala ya k'irk'iro "yallabai ga abincin" a yatsine jawad ya kalli tray d'in a hankali ya furta" bana ci Bala"yayi gaba abinsa, Bala kam binsa yyi da ido har ya fita daga parlour d'in.


Fulani maryam ma kam ta tsorata amma ta basar, sosai hankalinta ya karkata ga jawad dan fitar da yayi tasan ya fusata ne, sai dai tasan tunda areef yabi bayansa komai xanxo da sauk'i. Zaljameel kam jitayi kunya ta kamata, cikin ladabi ta durk'usa har k'asa ta gaida Fulani maryam, da fara'a ta amsa mata ta kuma tambayeta jiki, zaljameel jitayi xaman parlour ya isheta dan haka ta nufi bedroom d'inta, sosai ta shiga dana sanin ihun da tayi duk kuwa da cewa ba tana sane bane tsorata tayi, fitar yareema jawad a fusace ta shiga tunawa, omg tasan ihun ne ya b'ata masa rai. Kwanciya tayi a bed d'inta tana kallon ceiling, a hankali bacci yyi awon gaba da ita duk da uwar yunwar da takeji sai taji ta koshi.


Mom da Ammi xaune a parlour suna hirar yaushe gamo, amma hankalin Ammi ya karkata ga jawad, tasan sa da mugun xucia, tasan yana chan yana fushi, a daddafe suka kammala hirar Fulani ta nufi part d'inta da kuyangunta. Aikawa tayi a kira Mata jawad, dan aiken ya dawo da bayanin jawad bayanan, hankalinta ya kuma tashi dan haka ta d'auki phone d'inta ta fara neman layinsa, wayar ya shiga sai dai baiyi picking ba hakane ya k'ara tashin hankalin fulani.


Yareema jawad a wani katafaren garden, wanda yaji kayan fruits da korayen bishiyu, xaune yake a k'asa kan grass carpet, iska mai sanyi da dad'in k'amshi na kad'awa, sosai yaji dad'in xamansa a wajen jiyay duk bak'in cikin dake ransa ya yaye, nishad'i yakeyi. Sai daf da magrib ya bar garden d'in ya nufi wani babban mall, a lokacin ya tuna da phone d'inshi daya bari a car d'in, dan haka da sauri ya d'auka ya duba, 50 missed calls ya gani a raxane ya danna dan ganin waye, Ammi ya fad'a a bayyane, gaba d'aya hankalinsa ya tashi, xuciarsa ta damu tasan abinda ke faruwa Ammi ta masa wannan missed calls d'in , juya kan motar yyi dan bayajin xai iya xuwa mall d'in.


Wani wawan gudu yakeyi a titin burinsa ya ganshi a gida, yana isa gida kam part d'in Ammi ya nufa, tun daga parlour ya fara kwala mata kira, Ammi! Ammi! Ammi, sauri tayi ta mik'e ta nufi parlour jin muryar jawad, dama xaune take ta buga uban tagumi tana tunanin inda jawad ya shiga da yakasa d'aga kiranta. Tana fitowa ta rungumeshi, had'e da sauke ajiyar xucia, kuyangunta kam tuni sukayi waje dan basu guri, breaking hug d'in yareema jawad ya yi ya kama hannunta suka xauna a 2cter dake parlour n."Ammi na mai yake faruwa naga missed calls d'inki da yawa?" Kallon sa Ammi tayi bata gano b'acin rai a tare dashi ba sai damuwa, hakane yasa ta gane ya sakko daga fushin da yayi. Murmushi tayi "bbu komai jawad kawai na aika a kira mini kai akace baka nan, shiyasa na nemeka naji a ina kake" murmushi yyi had'e da kama hannunta "my Ammi ki daina d'aga hankalin ki haka, I'm not a small boy, kuma na manta phone d'ina a mota that's why banga call d'inki akan lokaci ba" ok my jawad, please ka dinga yayyafawa xuciarka ruwan sanyi, ka rage saurin fushi bashi da amfani kaji"gyad'a kai yyi, ya gane inda maganarta ta dosa amma ya share. Watch d'insa ya duba jin kiran sallah magrib, dan haka ya mik'e yayi ma Ammi sallama ya nufi masjid.


After two weeks


"Yareema jawad yayi tafia xuwa Egypt dad d'insa ya turashi ganin lapiar company d'in su dake chan. Areef kam ya samu damar xuwa gidan dan samun had'uwa da zaljameel, yau ma kamar kullum, tafe yake cikin motarsa sanye yake da manyan kaya, shadda milk colour kansa bbu hula k'amshi mai dad'i ke tashi a jikinsa, driving yake cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, wani wani Bash Bakery ya shiga ya siyo snacks da ice cream, tsarabar nawal ce dan yasan tana san ice cream and yaga yanayin shakuwarsu da zaljameel. Direct part d'in su zaljameel areef ya nufa, xaune suke a bakin swimming pool suna wasa da ruwa, "nawal inasan na iya hausa gashi kema naga baki iya sosai ba ballantana ki koyamin" daria nawal tayi "wallahi kam my aunt, nima ba iyawa nayi sosai ba sai dai na fiki" daria suka saka, "ok haka kikace ko?" yeah" nawal ta fad'a," gashi uncle jawad bayanan daya koya miki "shiru zaljameel tayi jin sunan jawad, ok dama guy d'in nan baya nan, ai naxata fushi yayi shi yasa naga ko wajen mom baya xuwa." Assalamu alaikum "sallamar areef ta katse musu hira, da gudu nawal ta mik'e ta nufe shi tana murna, uncle areef oyoyo, ledar hannunsa ya saki a k'asa d'aga ta yyi chak yana daria." Nawal yan mata, kin girma sosai "daria tayi" haba uncle dubani fa "hancinta areef yaja ya sauke ta, hankalinsa ya karkata ga zaljameel da duk ta dururuce, sanye take da English waers riga mara hannu sai igiya da ake d'aurewa a wuya rigar iya gwiwa ce, sai tree guater pencils gaba d'ayansu pink colour ne, a kame suke a jikinta,gashinta xube a gadon bayanta. Wani mugun yawu areef ya had'iya, zaljameel ta gama tafia da imaninsa, jiyay sha'awarta ta kamashi, areef kam dama bbu dama a wannan fannin, sai dai ko jawad bai san yana harkalla da mata ba, sirrinsa ne shi kad'ai.


Sumyn Bash ce💋


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

YAREEMAH JAWAD

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


Pure moment of life writers

p. m. l. w


A romantic love story
2017


July 2017


Story & written by

SUMAYYA SALEES SADEEQ


Nan gani nan bari, Idan kaji wane ba banza, ina kuke yan'uwa yan PURE MOMENT OF LIFE WRITERS, yabon gwani ya xama dole, gaskia tsarin ku dana novel din ku abin birgewa ne, Allah ya kara kaifin basira ya kuma kara had'a kanmu ameen, much love sister ❤
Chapter 14 · 0% Book details