← Book details Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 38 OF 40

Chapter 77&78

Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Room d'inta ya rakata ta d'auka hijab, da kansa ya sama mata ya d'auke ta chak suka sauka, bai ajiye ta ba sai a gaban prado d'insa, bud'ewa yayi ya saka a ciki ya zagaya shima ya shiga.


Zaljameel ta zuba masa white eyes d'inta masu kama da madara, masu kuma saukar wa da Jawad kasala.

Yana shiga ya saka key zai tada motar ya lura da kallon da Zaljameel ke masa ta gefen ido, juyawa yayi ya suka had'a ido, wani kallo ya watsa mata mai bayyanar da tsantsan son da yake mata, lumshe ido yayi ya bud'e ya sakar mata murmushi.

"Sweetheart wannan kallon fa?sai kace yau kika fara gani na, kinga handsome guy ko? ".

Dariya Zaljameel tayi ta d'auke kai tana murmushi k'asa k'asa," Haba Ya Jawad ina wani handsome anan, kawai dai ina kare yawa ne da kai ". Ta tsuntsire da dariya.


Ido ya fito dashi da alamun mamaki.

" Eyyeh Zaljameel ni kika fad'a ma haka ko? Ba matsala zaki gane cewa ni handsome ne, guy d'in da yan mata ke yayi ".


Dariya suka saka Jawad yaja mota suka fita.


A wani babban mall Jawad yayi parking ya fito, Zaljameel ma ta fito tana kallon mall d'in, ya birgeta sosai, dan tunda tazo Nigeria bata je tayi shopping ba, hannun ta Jawad ya kama suka nufi ciki yana takunsa na k'asaita.


Basket ya d'auka suka fara zagaya wa, bangaren Arabian gowns masu kyau, ga wasu galilas d'inkin dubai ready made, Zaljameel binsu tayi da kallo dan kayan sun mata kyau, Jawad ta kalla shima ita yake kallo, kashe mata ido d'aya yayi,

"Oya mrs Jawad a bata zab'a".


Mak'e kafad'a Zaljameel tayi "A'a ni dai kai zaka zab'a mini".


Murmushi yayi "wannan ai shi yafi komai sauk'i ranki ya dad'e, gimbiya Zaljameel matar Yareema Jawad " Dariya Zaljameel tayi, "Kai mijin Zaljameel Allah ya shirye ka" Ameen "Jawad ya fad'a yana dariya shima.

Nan Jawad ya shiga d'aukar kayan, sai ya kara mata a jikin ta yaga yarda sukayi mata sannan yasa a basket.


Ya mata shopping sosai na kayan sawa, shoes, handbag, jewellries masu kyau, da kayan make up, har sai da Zaljameel ta b'ata rai sannan Jawad ya hak'ura suka bar wajen, suka nufi side d'in chocolate da ice cream suka siya, sai da suka cika basket uku, Zaljameel ta cema Jawad tana zuwa, "Gyada mata kai yayi ta koma baya da sauri. Side d'in hand watch ta nufa, ta zab'a ma habibinta mai kyau da tsada sannan ta taho.


Tana b'ullowa inda ta bar Jawad ta wani ci birki jin k'afarta ta mata nauyi, mai zata gani? Jawad tsaye da wasu kyawawan yan mata, da kagansu kasan kud'i ya zauna, sai wani kwarkwasa suke masa suna fari da ido, shikam Jawad ko kallo basu isheshi ba, amma yana duba gefensa ko Zaljameel ta taho, yana ganin ta kam, ya fara musu murmushi, ya yarda suka gaisa sai dai suma abin ya basu mamaki ganin sun dad'e suna masa magana yak'i responding, amma shine harda murmushi.


Zaljameel kam ji tayi kamar zuciyarta zata fito dan kishi, wani k'arfi taji yazo mata, da saurin ta ta k'arasa, yarinyar dake washe ma Jawad baki Zaljameel ta d'auke ta da gigitaccen mari, bata dawo dai dai ba Zaljameel ta kuma d'auke ta da mari.


Yarinyar ce ta d'ago hannun ta a fuskarta tana mai jin zafin marin da Zaljameel ta mata, idonta duk ya ciko. Wata da suke tare ce ta fara magana wacce daka ganta kasan babu kunya a tare da ita ta nuna Zaljameel da yatsa "Ke yar iskar inace da zaki mari sister ta, dame kike tak'ama?".


Zaljameel ce ta kalli Jawad, ganin ya wani crossing hands yana kallon ikon Allah, yana kuma mamakin kishi irin na Zaljameel da k'arfin halin harda mari, ganin yana murmushi bayan yaji ana ci mata mutinci ya b'ata ran Zaljameel, hannu tasa ta d'auke Jawad da mari ta fashe da kuka ta fara tafiya. Yan matan ne suka bishi da kallo suna son ganin action d'in da zai d'auka, sai ganin Jawad sukayi ko a jikin sa, kuncinsa ta mara ya shafa da hannun sa yayi kissing, da sauri yabi bayan Zaljameel yana kiranta, amma bata bi ta kansa ba, gudu kad'an yayi ya tadda Zaljameel, hugging d'inta yayi ta baya, itakam sai k'ok'arin kwatar kanta take amma Jawad yak'i bata dama,juyo da ita yayi suna facing juna ya shiga goge mata hawayen dake bin fuskarta. "Haba my sweetheart mai yayi zafi haka, kika mari yar mutane,?". Banza ta masa tana harararsa tana kuma jin zafin tambayar daya mata, lalle Ya Jawad, ya raina mata hankali "murmushi yayi, yayi k'asa da murya kamar mai rad'a" kefa ki kace ni ba handsome bane, bayan nasan mata rushing suke a kaina ". I'm sorry dear, ba magana muke dasu ba fa, nayi hakane kawai dan abinda kika fad'a mini d'azu," kallonsa tayi dan ita gaba d'aya ma ta manta da maganar da suka yi,lallai Ya Jawad wato ramawa yayi?.


Kunnensa ya kama,"Baby na idan bakiyi hak'uri ba, ganin ta masa banza ya yasa Jawad ya tafi zai d'urk'usa a gaban ta, da sauri tasa hannu biyu ta taro Jawad, "A'a habibi na hak'ura".


Tashi Jawad yayi da tsananin murna ya rungume Zaljameel "Thanks my baby".


Ji sukai wajen ya dauk'i tafi, cikata Jawad yayi suka fara waiwaye, mutanen da suka gani zagaye dasu suna tafa musu ya basu matuk'ar mamaki, Sosai suka birge mutanen wajen, dan a Nigeria basu t'aba ganin masoya kamar Jawad da Zaljameel ba, ciki kuwa harda wacce Zaljameel ta mara.


Dariya Jawad da Zaljameel keyi, itakam Zaljameel ta rufe fuskarta da hannu saboda kunya, shikam Jawad ko a jikin sa.


Gaisawa da mutanen wajen sukai, sannan Jawad yaja hannun Zaljameel suka nufi yarinyar data mara, cikin jin nauyi Zaljameel ta bata hak'uri, ta hak'ura ta kuma yi dana sanin kula Jawad, sunayen su Zaljameel ta tambaya, d'aya siyama,wacce aka mara kuma khairat, "Wow nice name, can we be friends?" khairat ta tambaya, kallon Jawad Zaljameel tayi, alama ya mata data amince, "why not sister" dariya sukasa sukayi exchanging number, bayan an gama buga musu balance Jawad ya bada atm card aka cire kud'in su, suma khairat da siyama Jawad ya biya musu kud'in suka fita tare.


Sallama sukayi siyama da khairat suka nufi motarsu, Zaljameel da Jawad ma haka.


SU ZALJAMEEL ANSAN KISHIN MIJI 😂😂🤔🤔


SUMYNBASH CE 💋


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

YAREEMAH JAWAD

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L
(We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers)


A romantic love story
2017

August 2017


Story & written by
SUMAYYA SALEES SADEEQ
Chapter 38 · 0% Book details