← Book details Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 25 OF 40

Chapter 51&52

Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wani kuka ta sake fashewa da shi,"Annah ki taimaka mini ki sa a raba aurena da Ya Jawad, bazan iya zama dashi ba".


Annah jikin ta yayi sanyi, marin da Jawad ya yi ma Zaljameel ya b'ata rai, ai marin mace bashi da kyau ballantana, tana matsayin matarsa, wani dogon numfashi Annah taja ta kalli Zaljameel!


"Wallahi Zaljameel ban san komai game da aurenki ba sai bayan an d'aura auren ku da Jawad, kinsan matsayina a gidan nan, duk da sarauniya Ayshat ta bani dama ta 'yanta ni amma ban daina muku hidima ba, babu yarda zanyi na hana abinda Allah ya tsara, Allah ya rubuta Jawad shine mijin ki,ina me baki hak' uri Zaljameel, tabbas ba'a baki dama ba, sai dai dama budurwa bata da 'yancin zab' ama kanta miji sai dai iyayenta su zab'a mata, Zaljameel, ni na san Jawad na san halin Jawad, dan ko Fulani maryam bazata fad'a mini halin Jawad ba, xan sanar dake hanyoyin da zaki bi ku zauna lpy, ki kuma shawo kansa, Jawad namiji ne, namiji kuwa yaro ne a hannun matarsa, ke zaki yima Jawad sabuwar tarbiyya Zaljameel, ke zaki d'ora shi akan hanya kuma dole yabi"

Shiru Annah tayi tana kallon Zaljameel data zuba tagumi tana sauraron ta. Murmushi Annah tayi ganin yarda Zaljameel ta bada attention tana sauraron ta, hakan ya bawa Annah damar cigaba da magana. "Zaljameel bani kunnen ki kiji" matsowa Zaljameel tayi Annah ta mata rad'a, wani shu'umin murmushi Zaljameel tayi tama Annah godia.


Mik'ewa tayi ta nufi bedroom d'inta,a parlour ta tarar da Nawal ta gama kukan ta ta b'ige da kallon cartoon harda tuntsira dariya, tana ganin Zaljameel ta mik'e tayi wajen ta da gudu suka shige ciki.

Annah kam dad'i ya kamata ta shawo kan Zaljameel, sai dai abinda Annah bata sani ba, yayin da take bama Zaljameel shawara a kunne a yayin Zaljameel ta tuna da nata idea d'in,tayi watsi dana Annah, hakan ne yasa ta murmushin jin dad'i.


After one week


Tunda ga ranar da Jawad ya mari Zaljameel basu k'ara had'uwa ba, cuz ya fara zuwa hospital, hakan yasa ya shiga damuwa ya kuma fara tunanin taya ya zai had'u da sunshine d'insa.


Zaune yake a office d'insa na alfarma, yayin da sanyin Ac ke kad'ashi,sanye yake da maroon suit gashin kansa ya sha gyara sai kyalli yake, glass cup a gaban sa wanda aka zuba masa hot coffee a ciki, sha yake kamar baya so dan tunanin Zaljameel ya hanashi sukuni, zuciyarsa na azalzala shi akan yaje ya nemi forgiveness d'inta, a hankali ya furta no.. It will never happen, ace na bama Zaljameel hak'uri ai na siyama kaina raini, zan cigaba da jurewa har ranar da Allah zai sanya mata sona a zuciyar ta".


Zaljameel zaune a parlour, sanye take da Arabian gown peach colour da taji stones, tayi rolling kanta da light blue veil, tayi make up sosai a fuskarta, jikin ta sai tashin k'amshi yake kamar kullum, tayi wani fresh da ita dan Annah na matuk'ar k'ok'ari akan Zaljameel tana kuma k'ara kwantar mata da hankali, hakan yasa Zaljameel ta saki jikin ta tayi dan ki'ba abinta.


Tsaye take ta bama door d'in parlour baya tana kashe selfie, sai chanja style take yi tana kama waist da hannu d'aya tana d'auka pic d'in, tayi kyau sosai, sai da ta dauki yakai 50sannan ta fara k'ok'arin hak'ura dan ta fara gajia, tana kashe selfie na last ta duba pic d'in wa zata gani! Ya Jawad tsaye da phone a hannunsa d'aya hannun da briefcase, Murmushi a fuskarsa, a pic d'in amma Zaljameel na juyawa ya had'e rai, mak'ala phone d'in yayi a kunnen sa ya fara magana "Bala mai yasa kake hakane, sau nawa kake so na fad'a maka," tsaki ya ja ya kalli Zaljameel data yi mutuwar tsaye, a hankali taja k'afa ta fara tafiyarta mai d'auke da jan hankali,duk wani sassa na jikin ta kad'awa yake yi.


Ganin ta fara tafiya yasa Jawad ya daka mata tsawa," keeeeee..... Zaljameel zo zo nan "tsayawa tayi chak amma bata juyo ba, hakan ya hassala Jawad, cikin zuciyarsa ya fara magana" Anya Zaljameel bata ganshi ba kuwa lokacin da yake kallonta? "rasa amsar tambayar yayi hakan yasa ya cigaba da magana.


Baki iya sannu da zuwa ba baki iya k'arbar briefcase na miji ba? Ya fad'a fuskarsa a had'e.


A hankali ta juyo ta kalle shi,eyes to eyes sukayi da Zaljameel for some minutes! Wani far Zaljameel tayi da ido tayi wani shu'umin murmushi duk da k'irjinta na bugawa dan bata san abinda zaije yazo ba ta fara magana!


"Eyyah ya Jawad, laifin ka ne da baka fad'a mini tun wuri kana da buk'atar hakan ba, so yanzu gaskia bani da time d'in wannan cuz baya cikin agender na na yau da kullum, ina ganin ka tara next time" Murguda masa cute mouth dinta tayi ta bar wajen da sauri kar tasha bugu.


Mamaki bayyane a fuskar Jawad akan maganar da Zaljameel ta fad'a masa, ko a mafarki bai tab'a tunanin Zaljameel ta iya magana haka ba, lallai sai yayi da gaske, in ba haka ba raini zai shiga tsakanin sa da Zaljameel.


Bedroom d'insa ya nufa ransa a dagule.


Zaljameel na shiga d'akin ta ta lek'o taga ko Jawad ya bi bayanta, ganin bashi yasa tayi saurin zura key ta nufi bed dinta ta kwanta tana murnar abinda tama Ya Jawad, tasan yarda yake dan girman kai da jiji da kai yana chan ya hassala, wata dariya ta fashe da ita, "Ya Jawad" ta furta a hankali, ji tayi sunan ya mata dad'i hakan yasa taji tana sha'awar sake kiran sunan, "Ya Jawad" ta sake maimaita wa, shiru tayi kamar mai nazarin wani abu sai kawai ta d'auka wayarta ta fara ganin pictures.


Pictures ta gani nata birjik da ita da Ya Jawad, yarda tayi fara'a haka shima, babu wanda zaiyi tunanin ba tare suka d'auka ba, sunyi kyau sosai, tsayawa tayi tana kallon face d'in Jawad, murmushin da yayi ya k'ara ma fuskarsa kyau, cikin zuciyarta take magana!

"Dama Ya Jawad ya dad'e da shigowa parlour amma bata ji shigowarsa ba?"

Zuciyarta ta bata amsa,!

" Yeah Zaljameel ga alama kin gani a pic "

" To murmushin mai yake yi?" maybe da fara'arsa ya shigo aka yi sa'a kika d'auka pic d'in".

Yes.... Hakane ta fad'a tana kuma kallon pic d'in,sallamar
data ji yasa ta d'aga kai dan ta tabbatar.


"Zahra" Zaljameel ta fad'a da karfi ta mik'e tsaye, bata bari Zahra ta k'arasa shigowa room d'in ba ta tare ta da gudunta!" Zahra where are you?, Zahra ina nemanki ina son a warware mini dalilin aurena da Ya Jawad da kuma dalilin daya hana aurenki da shi ".


Kallonta Zahra tayi tana murmushi, ohhh... Ni Zahra, Zaljameel dama haka Mom ta koya miki ki dinga karb'ar bak'i, Zahra ta fad'a tana rik'e baki. Kunya ce ta kama Zaljameel, hannun Zahra ta kama suka zauna a kan sofa,Zahra yi hak'uri, na dad'e ina son ganin ki muyi magana amma na rasa wannan damar, gani nake kamar zaki tafi baki bani amsar tambaya ta dats why kika ga na fara tambayr ki".


"Babu komai Zaljameel ykk?"

" Zahra ba lafiya ba, Zahra ya akai Ya Jawad ya zama mijina shi nake son sami" zama Zahra ta gyara ta fara bama Zaljameel labarin yarda akayi. Mik'ewa tsaye Zaljameel tayi "A'a Zahra, gaskia baki fahimta dai dai ba,babu son ya Jawad a zuciyata, Zahra mai yasa kika hak'ura da farin cikin ki saboda ni, wane hallacci na miki a rayuwa da kika mini hakan,sai dai kash, na so ace kamar yarda ku kayi tunanin ina son Jawad ace da gaske ina sonsa, kuma naso ace da gaske shima yana sona ". Zama tayi tana shartar hawaye, cikin sanyin jiki Zahra taja Zaljameel jikin ta ta fara lallashi," Zaljameel mai ya faru tsakanin ki da Jawad a dan zaman da ku kayi da har kika yanke masa hukuncin baya sonki".


Tun daga ranar da aka kawo ta ta fara bama Zahra labari har zuwa yau, shiru Zahra tayi tana nazarin labarin Zaljameel, Murmushi Zahra tayi ta kalli Zaljameel............


Ku biyo ni dan jin mai Zahra zata cema Zaljameel 👂🏻👀


SUMYN BASH CE


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

YAREEMAH JAWAD

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L

We don't just entertain we touch the heart of the readers.


A romantic love story
2017


July 2017


Story & written by

SUMAYYA SALEES SADEEQ
Chapter 25 · 0% Book details