← Book details Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 12 OF 40

Chapter 21&22

Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

"Xama yyi ya fara breakfast hankali kwance, wayarsa ce ta fara ringing, d'auka yyi ya duba mai Kiran, Peter ne abokin aikinsa, shima doctor ne. Daga wa yareema jawad yyi yayi shiru yana sauraran peter. cikin rawar murya jawad "jawad where are u? Please we need to see u in hospital now" a rikice jawad ya tambayi Peter, "what's happening Peter? Cikin sark'ewar harshe Peter ya fara magana" we have a patient pregnant women, please jawad is an emergency operation need to see u "a rikice yareema jawad ya ajiye cup d'in tea dake hannunsa, parlour ya nufa ya d'auki laptop bag dinsa ya rataya a kafad'a ya dau hanya, gudu yake sosai har ya karasa gate d'in hospital, horn yake ba tsayawa har ya firgita gate man, da gudu shima ya taso ya bude gate d'in. Motar ya fixga ya shige surrounding d'in hospital, waje ya samu yyi parking car d'in ya d'auki laptop bag dinsa yyi cikin da sauri. Office ya nufa ya ajiye laptop bag ya d'auki lab court ya saka, yana fita da sauri suka ci karo da peter, tsorata yyi da ganin yareema jawad a hospital kuma a shirye, kallonsa yareema jawad yyi "ina patient d'in?" jawad ya katsewa peter tunani. Duk wani singing da xa'ayi an gama dan haka yana shiga hand clove yasa a hannunsa ya fara operation d'in, bai d'au wani long time ba yayi nasarar cire baby girl a cikin matar.


"Yana fita ya tarar da mijin matar tsaye a kofar theater room d'in, da sauri yabi bayan yareema jawad yana tamayarsa a wane hali matarsa ke ciki,labari ya bashi matarsa ta haihu kuma baby girl, yyi gaba, ya bar mutun da rawa. Office dinsa ya nufa ya huta kafin yaje wajen director ya sanar masa tafiarsa Nigeria.


"Da kyar director ya yarda da tafiar jawad, dan yace ya sanar dasu ko salary d'in da suke basa ne yyi kad'an ya sanar dasu ko nawa yakeso xasu bashi, a hankali ya warware musu abinda ke faruwa, shima ba asan ransa bane tafiar. Sunyi ciwon rai dan samun doctor kamar jawad abu ne mai wuya.


"Bbu matsala doctor jawad amma ko ya koma yyi kokari ya dinga xuwa, ya amince da hakan ya kuma ji dadin yarda suka nuna masa kauna,


"Xaune yake a office d'in sa yana duba wani file, wayarsa ce tayi ringing, mai martaba ya gani dan haka da ladabi ya daga, sun gaisa nan yake masa tuni cewa yau Friday gobe ne ranar daya kamata ka dawo, "eh mai martaba insha Allah goben xan taho" to shi kenan Allah ya maka albarka "ameen yareema jawad ya amsa.


" A ranar Friday karfe 8:00pm aka hada dinner saboda tafiar yareema jawad, suna so su karramashi, duk doctors d'in hospital d'in sun hallara a wani babban waje da ake ji dashi a London, yareema jawad yyi farin ciki da hakan.


"Karfe 8:00pm yareema jawad ya bayyana a wajen, yyi masifar kyau, suit ce a jikinsa black, sai red longslip, black necktie ya saka, fuskarsa dauke da farin glass wanda ya karawa shigar sa kyau,wani daddad'an k'amshi ke tashi a jikinsa. Da takunsa na k'asaita ya karasa kan high table da aka tanadar masa, nan waje ya kaure sa tafi, raf-raf-raf, cikin farin ciki ya daga kai yana karewa mutanen dasukazo wajen, waxai gani, Zahra zahradden ya maimaita a xuciarsa. Sanye take da wani mini skirt orange,sai karamar riga mara hannu, ta saki gashin kanta a gadon bayanta, xaune take a cinyar wani bature sai wani shafa fuskarsa take tana wani narkewa a jikinsa, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un shine abinda ya nana ta a xuciarsa. A hankali yaji kuncin da yakeji ya bar xuciarsa. Neman yareema jawad akai akan yyi jawabin godia da kuma sallama ga friends dinsa,tashi yyi ya karbi loudspeaker ya fara bayani, dum Zahra taji xuciarta ta buga jin murya yareema jawad, a hankali ta juyo da kanta tana kallon mai magana, shi ne ta fada a ranta, gaba daya ta tsure, Dan tabbas tasan ya ganta, tashi take kokarin yi daga cinyar baturen amma yaki barinta, haushi ne ya kamata ta fara kunkuni, "ynx Idan yareema jawad bai ganni ba wannan sai ya tuna mini asiri" duk abinda take jawad na kallonta yana murmushin mugunta. Da kyar ta samu ya cikata bayan ta masa rad'a a kunne akan tana da uxuri ne, tana tashi ta nufi high table Inda yareema jawad ke bayani, tana wani kwarkwasa da karairaya. Tunda ta tunkaro shi ya xuba mata ido yana kallonta cike da kyama, sai yatsina fuska yakeyi. Gaba daya Zahra tasha jinin jikinta da kallon da jawad ke mata, duba jikinta ta fara yi ko a kwai matsalar daya hango,a haka ta daure ta karasa kusa dashi, bude baki tayi xatayi magana yareema jawad ya tushe hanci yana kakarin amai, security ya fara kira yana nuna Zahra da hannunsa hancinsa da bakinsa a tushe, da sauri kam suka bayyana a wajen suka d'auki Zahra chak suka nufi waje da ita. Baturen da sukaxo yana gani ya basar dan a tunainsa ganin jawad yasa ta rabu dashi, ga kuma irin wulakancin daya mata dan haka ya nuna kamar bai Santa ba.wani murmushi yareema jawad yyi bayan mutanen wajen sun kewaye shi suna masa sannu.


SUMYNBASH CE💋


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

YAREEMAH JAWAD


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


®PURE MOMENT OF LIFE WRITERS


P. M. L. W


A romantic love story
2017


Story & written by

SUMAYYA SALEES SADEEQ
Chapter 12 · 0% Book details