← Book details Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 29 OF 40

Chapter 60&61

Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Kissing d'inta yake cike da kwarewa,sun dau wajen 5mint Jawad na kissing d'in lips d'in Zaljameel kamar ya samu sweet, cire bakinta yayi daga nasa amma bai cikata ba, hugging dinta yayi yana sauke ajiyar zuciya, dan ba k'aramin d'aure wa yayi ba ya rabu da Zaljameel.

Zaljameel tayi luf a kirjinsa tana maida numfashi, cuz taji bak'on lamari a tare da ita, tunda take babu wanda ya tab'a kissing d'in ta sai Jawad.

Sake hugging dinta yayi yana ji kamar wani zai raba su. A hankali Zaljameel ke dawowa nutsuwarta, da k'arfinta ta tura shi, kasancewar jikinsa babu kwari yasa yayi baya, ya zuba mata sexy eyes d'insa yana kallon ta cike da sha'awarta.


A hankali y fara takowa ya nufi inda Zaljameel ke tsaye, hannu ta d'aga masa!

"Jawad dakata, karka kuskura ka matso kusa dani," tuf ta tufar da yawon bakinta, "Ka rasa abinda zaka mini sai ka zuba mini wannan bakin naka a cikin nawa. Runtse ido tayi cike da takaicin abinda Jawad ya mata." Jawad karka raina mini hankali, na rasa dalilin chanja warka lokaci d'aya, I know what I'm doing, i'm not a small gal I'm matured, so na riga na gane ka, I hate you Jawad, kamar yarda kaima you hate me, banson k'ara ganin ka, kaje ka auri wacce kake so ka huta da auren Zaljameel har abada".

Jawad kam ya zama kamar an dasa shi a wajen, his brain has already stop thinking anything,banda kallonta babu abinda Jawad keyi.


K'ofa ta kalla," Get out Jawad I don't want to see you ".

Bashi da zab'i daya wuce ya fita a d'akin kafin zuciyarsa ta tarwatse, a hankali yaja k'afa ya fita a d'akin.


Bai tsaya yima Mom sallama ba cuz bazai iya magana ba a halin da yake ciki, bai bi takan motarsa ba ya nufi part d'insa haunkalinsa a tashe, dishi dishi yake gani a idonsa a da kyar yaje guda.

Yana shiga bai tsaya ko ina ba ya nufi bathroom, dan ruwa kawai yake buk'ata, jacuzzi ya nufa ya shiga ciki ya sakar ma kansa ruwa,a hankali ya fara dawowa dai dai da har ya fara tuna maganganun Zaljameel, Runtse ido yana jin zuciyarsa na masa rad'adi, a haka ya gama wankan y fito ya baje a kan bed.


Binsa Zaljameel tayi da kallon tausayi, fad'a wa kan bed d'inta tayi ta fashe da wani kuka mai ban tausayi," I'm sorry Ya Jawad, wallahi I love you, you mean alot to me, but ina son tabbatar da soyayyata a zuciyarka ta cigaba da kuka, sai da tayi mai isarta sannan ta tashi zaune, ko me ta tuna ta mai rubutashi da sauri ta nufi wardrobe,shiryawa tayi cikin wani black material, mai ratsin red, d'inkin riga da siket, veil ta yafa ta fita da sauri.


Itama bata bari Mom tasan da fitarta ta wuce da sauri, gidan ta ta nufa.

A hankali ta shiga parlour dan karsu had'u da Jawad, ganin baya nan yasa ta shige part d'inta tana sand'a, tana waiwaye harda tuntub'e a haka ta shige ciki ta saka key.


Zama tayi a gefen bed d'inta ta buga tagumi, Jawad ya shiga uku, wato girman kanshi da izza sun hanashi magana, tsaki taja ta jawo wayarta ta buga ma Zahra, tana fara ringing tayi picking kamar mai jira.


Zaljameel ta bama Zahra labarin yarda sukayi da Jawad,"Zahra kaina ya kulle, need your advice please ki taimaka mini.

Shiru Zahra tayi tana nazarin mafita, cikin sanyin jiki Zahra ta fara magana!

Zaljameel Jawad ya gama dake, ya kuma ruguza miki duk wani shiri da kike yi, karki manta kince tare kukaje wajen parent d'inku ya kuma nuna miki so a gaban so, Zaljameel a tunanin ki mai zaki ce musu su yarda?.


Gumi ne ya karyo wa Zaljameel, tabbas Jawad ya gama da ita, "Zahra solution nake nema please help me".


"Akwai mafita d'aya Zaljameel, amma tana da had' ari, amma idan kika bi yarda na nuna miki to tabbas zakiyi nasara"

"Insha Allah Zahra komai zai tafi dai dai fad'a mini"
korata Zaljameel tayi banji me Zahra tace mata ba.


A tsorace Zaljameel ta fito da ido waje, "Zahra kina ganin hakan zaiyi kuwa?"

"Kwarai kuwa Zaljameel babu matsala"


Ihun murna Zaljameel tayi ta fara had'a kayan ta a trolley.


Jawad tunda ya kwanta ya kasa motsi, a haka Bala ya same shi, cikin tashin hankali Bala ke tambayar Jawad ko lpy amma bai ce dashi komai ba, ya kawo masa abinci yak'i ci, hankalin Bala kam ya tashi ganin Yareema Jawad a wannan hankali, bai ankara ba yaga hawaye nabin fuskar Jawad. Tagumi Bala ya buga dan yasan duk abinda ke damun Jawad ba karami bane.


After one week

Zaljameel tayi doguwar mik'a tayi addu'ar tashi a bacci ta mik'e zuciyarta fes ta shiga bathroom, wanka tayi ta d'auka doguwar riga ta saka, batayi make up ba sai kyalli da fuskarta keyi, rub ta samu ta shafa a face d'inta nan da nan face d'inta yayi ja idonta ya fara hawaye, itama ta k'ara da nata kukan, hijab ta d'auka ta saka ta d'auka trolley ta fita.


A motar ta ta nufi part Fulani tana rusar kuka.


Tana zuwa kofar gida ta fita batare data rufe motar ba ta shiga tana wani irin kuka.


Fulani da mai martaba zaune suna hira sukaji shigowar Zaljameel, a razane suka tashi tsaye suka nufeta, fad'awa tayi jikin Fulani ta kuma fashewa da kuka.


Fulani ce tayi k'arfin halin tambayar ta," Zaljameel meke faruwa ne? Mai ya samu Jawad d'in"

D'ago wa tayi da jan idonta ta kalli Mom, "Fulani babu abinda ya same shi,Fulani koroni yayi gida wai dan ina da ciki, yace sai an zubar ni kuma nace A'a ban yarda ba ina son cikina shine yace nabar gidan.


Mai martaba bai son lokacin daya zube a kujera ba yana salati, Jawad d'in ne yace ki tafi gida" Eh mai martaba shi yace na taho.


Shikenan Zaljameel, kiyi hak'uri, Fulani shiga da ita ciki. Fulani da ta kasa magana dan takaicin abinda Jawad yayi tana kama Zaljameel suka nufi ciki.


KUYI HAKURI DA WANNAN, SAI DA NAYI TYPING MAI YAWA WALLAHI YA GOGE, NA SAKE WANI NE SABODA NA MUKU ALKHAWARI, SAI KUN JINI.

SUMYNBASH CE 💋


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

YAREEMAH JAWAD

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L

(We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers)


A romantic love story
2017

July 2017


Story & written by

SUMAYYA SALEES SADEEQ
Chapter 29 · 0% Book details