Chapter 37&38
Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Zama tayi a gefen Mom ta d'aura kanta a kafad'ar ta, hannun Mom ta kama ta rik'e a nata.
"Mom meya sameki?"
Shiru Mom tayi ta fara tunanin maganar da sukayi da Dad,
"Aysha munyi magana da Jawad, mun kuma sanar dashi maganar aurensa da Zaljameel"
Nan Dad ya labarta mata yarda sukayi, Mom kam gaba d'aya bata ji dad'in hakan ba,sai dai family d'in basu da al'adar auren dole, sun fi so kowa ya fitar da wanda xai aura.
"Sarki mai mirabus ba baiji dad'in shirin da iyayen sukayi ba, amma shi bashi da wani buri daya wuce yaga auren Zaljameel da Jawad.
Ajiyar zucia Mom tayi ta kalli Zaljameel," Baby na wannan kwalliyar ina zaki? "
Rufe fuskarta tayi tana murmushi,
" Mom hajiar Areef ce ta damu naje mu gaisa "
" Ok ke dawa zaku? "
" Nida Nawal "
" A'a Zaljameel, ba zaki je ke kad'ai ba, kinsan ke jinin sarauta ce, akwai kuyangu daya kamata su rakaki, bari muyi magana da Fulani "
" Ok Mom " Zaljameel ta amsa ba dan ranta ya so ba, dan bata son bac'in ran Mom.
" Mom ce ta kira Fulani ta sanar da ita maganar zuwan Zaljameel,
"Eh gaskia taje amma shawarar da kikai ta zuwan ta da kuyangu yayi, dan sarauta ba k'arya bace, zan tura miki Annah da yan mata guda biyu"
"Ok Fulani"
Sallama sukayi Mom ta zauna tana nazari.
Sallama Annah tayi a cikin parlour,Mom na zaune, cikin ladabi suka durkusa k'asa suna kwasar gaisuwa. Da sauri Mom ta mik'e ta nufi inda Annah ke durkushe, hannu biyu tasa ta d'agota, fuskarta d'auke da fara'a ta kalli Annah.
"Haba Annah, maiyasa kike haka, ai ni yarki ce bai Kamata ki dinga durk'usa mini ba"
Murmushin jin dad'i Annah tayi,kanta a k'asa ta fara magana
"Tuba nake ranki ya dad'e amma durk'usawa miki ya zama dole, a matsayina na baiwar ku"
"Baiwa? Annah kina so kice mini har yanzu ke baiwa ce a masarautar nan?"
Murmushi Annah tayi, "Sarauniya Aysha ni baiwa ce kuma a baiwa zan mutu"
Cikin hassala Mom ta fara fad'a, "Gaskia Yareema Jawad ya bani mamaki, shin bashi da labarin kece kika renesa har ya girma?"
Ganin yarda Mom ke huci yasa Annah ta fara bayani cikin ladabi," Sarauniya Yareema Jawad ya bani duk wani gata, ya kuma yi iya k'ok'arinsa wajen ganin ya y'anta ni amma nak'i dan bani da burin daya wuce na kyautata muku, dan kun mini hallaci, idan na yarda kuka y'anta ni zanji kamar na zama kai d'aya daku, ni Kuma bana fatan haka a rayuwata "
" Annah ni Aysha na miki alkawarin zan y'anta ki, kuma zan cigaba da yi miki kallo a matsayin uwa ba kuyanga ba"
Annah ce ta fara hawayen farin ciki, ita dama Allah ya sani jinin ta ya had'u dana Aysha, dan ta kasance bata dauki dunia a bakin komai ba, kuma bata tak'ama da mulki da daular da take ciki, a ko yaushe mai arziki da mara arziki nata ne.
"Godia nake ranki ya dad'e Allah ya raya miki zuria"
"Ameen Mom ta amsa"
"Ina gimbiyar take" Annah ta tambaya tana murmushi.
"Tana d'akinta" Mom ta musu nuni da hannu. Cikin sauri yan matan biyu suka nufi d'akin Annah ma tabi bayansu.
Da sallama suka shiga d'akin, Zaljameel zaune a gefen bed d'in ta, ta lula duniar tunani, jin sallama yasa ta amsa, a hankali ta juyo da kanta, ganin bak'in fuska yasa ta mik'ewa zaune, da gani bbu tambaya sune kuyangun da za'a had'a su tafia tare, ba laifi sunyi.
Bajewa sukayi a k'asa suka fara gaishe ta, "An gaishe ki gimbiya Zaljameel, yar wazeeri jikar sarki, takawarki lafia"
Sosai Zaljameel abin ya bata daria, au dama abinda suke cewa kenan, gaskia rashin jin hausa ya sata a matsala, daria take sosai harda rik'e ciki, tunanin shirmen data dinga yi take.
Annah da sauran bayi kam sun bi Zaljameel da kallon rashin fahimtar dariar da take musu, to ko dai Zaljameel tana da matsalar kwakwalwa ne ba'a fad'a musu ba, cikin dauriya Annah ta fara magana. "Tuba muke ranki ya dad'e ko zamu iya sanin dalilin dariar nan? "
Kallon Annah tayi, ji tayi tsohuwar ta shiga ranta, cikin murmushi da kuma maganar ta cikin yaren hausa da bata gama kwarewa ba ta fara magana.
"Na tunane a tym d'in da nazo Nigeria bana jin hausa, danaji ana magana irin wanda kuka yi yanzu dan razana da rashin sanin abinda ake fad'a har suma nayi"
Yan matan biyu suka fara tushe bakin su, dan yanzu suma Zaljameel ta basu daria, ganin yarda take gurbatacciyar hausa amma tana ta iya hausa.
"Allah sarki uwar d'akina gimbiya Zaljameel, ina tayaki murnar iya hausa" cikin jin dad'i ta amsa ma Annah da nagode.
Cikin sauri Annah ta sanar da Zaljameel zasu gyara mata kwalliyar ta, bbu musu ta yarda suka fara shiryata, cikin mintina kalilan Zaljameel ta fito cikin alkyabba mai bala'in tsada da kyan gani, tasha ado sosai, tsaye take a gaban mirror tana yaba kyan da tayi, tana kuma jinjima su Annah .
"Ranki ya dad'e kinyi kyau" murmushi tayi ma Annah dan bama ta kalli sauran yan matan ba, ita tsohuwar ce kawai ta mata.
Wayar Areef ce ta shigo, cikin sauri a cikin yan matan ta dakko mata, karb'a tayi murmushi tayi da sai da beauty point dinta ya luba, tsantsan kyanta ya k'ara bayana.
"Hello my Queen kin gama shiryawa gani a kofar gidan ku"
"Na gama habibi sannu ka da zuwa"
" Yawwa amaryar Areef"ji tayi kunyarsa ta kamata, shiru tayi tana daria k'asa-kasa.
A gurguje suka fito bayan Annah ta koyawa Zaljameel irin tafiar da zatayi, ba tare da b'ata lokaci ba Zaljameel ta iya, ita kanta yana yin tafiar da takeyi a yanzu ta birgeta.
A parlour suka tarar da Mom, sallama sukayi mata suka fita, a wajen Areef suka tarar da Nawal, dan haka ba b'ata lokaci Areef yaja suka tafi.
Kyakkawar tarba hajiar Areef tayi masu, dama an tanadi kayan ciye ciye, da shaye shaye, kamar yarda Annah ta fad'a ma Zaljameel kar taci komai aka bata haka tayi. Shigowar tayseer cikin parlour tana way yaja hankalin su, har Zaljameel.
Sanye take cikin wani material black, dinkin fitet gown, kayan ya kamata kamar a jikinta aka d'inka shi, siririn veil ta yafa hannunta d'auke da jaka, daga ganin alama daga unguwa ta dawo.
"Hajia ta I'm back" abinda tace kenan ta wuce ciki ba tare data kalli inda su Zaljameel suke ba.
Sosai hajiar Areef ta had'a ma Zaljameel tsaraba, sukayi sallama Areef ya maida su gida.
Egypt
Yareema Jawad zaune a dakinsa na hotel yana tura ma Zahra kwatancen inda zata same shi a Egypt, a ranar zata sauka.
Ya matsu tazo su wuce Nigeria, dan bashi da burin daya wuce ganin Zaljameel. Sosai Zahra ta gane kwatancen hotel d'in, dan Egypt ba bakonta bane tana zuwa shakatawa.
Waya ta mishi tana reception, ok yace mata ya kashe wayar. Waya yayi ya sanar da zuwan Zahra ya kuma bada umarnin a bata key d'in d'akin da yayi mata bucking, ranta bai so ba taso ace a daki d'aya zasu zauna da Jawad, ta karb'i key d'in ta nufi room d'in.
Wasa wasa bbu Yareema Jawad bbu alamunsa, tunda yaji ta je room d'in daya kama mata yyi switching phone d'insa. Har dare bbu Jawad tayi ta ta kiran layinsa amma shiru, zama tayi taci kukanta ta gode Allah, wato dama Jawad so yake ya wulakantata shi yasa ya kirata. Haka Zahra ta kwana bata ga Jawad ba, shi kam yana daki ya dasa tunanin Zaljameel har bacci barawo ya daukesa.
Washe gari
Yareema Jawad sanye cikin suit red and black, tsaye yake a gaban mirror yana kallon Kansas, sauri yayi ya d'auke kansa daga mirror dan pic din Zaljameel ke masa gizo, ya rasa wane irin so yakema Zaljameel, kamata ace yanzu ya hakura da tunanin ta, d'akin da Zahra take ya nufa cikin takunsa na kasaita.
Zahra najin knocking ta fito jikinta na rawa, tana bude masa ya wurga mata wani kallo da tasha jinin jikinta, kallon kanta tayi, sanye take da sleeping dress iya gwiwa, kanta bbu dankwali gashinta baje a gadon bayanta, cikin hanzari Yareema Jawad ya juya zai bar wajen Zahra ta rike hannun sa.
SUMYNBASH CE💋
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
YAREEMAH JAWAD
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
©pure moment of life writers
P.M.L
A romantic love story
2017
July 2017
Story & written by
SUMAYYA SALEES SADEEQ