← Book details Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 31 OF 40

Chapter 64&65

Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Fara ja da baya tayi tana hawaye, har ta bud'e baki zatayi magana taji takai bango tsaida maganar tayi ta cigaba da hawaye. Tuna abinda Zaljameel ta masa yasa ya ja da baya da sauri yana kallonta fuskarsa k'unshe da tsantsar b'acin rai da damuwa, zuba nata narkakkun idanunsa yayi yana mata wani irin kallo da ta kasa fassara shi, maganar Areef ke masa yawo aka, "Matarka Zaljameel na d'auke da cikin ka a jikinta wanda kace ta zubar" rintse ido yayi, a take yanayin Jawad ya chanja, idonsa ya rikid'e yayi ja, sai huci yake, Zaljameel ya nufa gadan gadan ya fincike hijab d'in dake jikinta, yana k'are mata kallo tun daga sama har k'asa, cikin ta ya zubama ido yana nazari, "Zaljameel cikin waye a jikinki?".

Wani kallon rainin hankali Zaljameel ta masa, ta yatsina fuska, "Haba Ya Jawad mai kake nufi da cikin waye a jikina? Ina da mijine bayan kai?".

Cikin zafin nama Jawad ya tamk'i gashin Zaljameel ya rik'e kam yana huci,. Wata k'ara Zaljameel ta saki dan azaba, ta fara k'ok'arin kwatar gashin ta, kuma ja yayi da k'arfi hakan yasa ta saki hannunsa tana hawaye "Please Ya Jawad" Keep quiet Zaljameel, banson jin magana daga bakin ki indai ba ansar tambaya na zaki bani ba.

"Ya Jawad gaskia fa na fad'a maka, please ka cikani".

D'auke fuskarta Jawad yayi da wani kyakyawan mari, dan a yarda zuciyarsa na bushe tofa zai iya zubar da cikin dake jikin Zaljameel amma ya bama zuciyarsa hak'uri, cika kanta yayi ya fita a room d'in amma sai da ya d'auka key ya rufe Zaljameel a ciki. Zama tayi ta zura fuskarta cikin cinyoyinta tana rusar kuka, "Anya bazata fad'a ma Jawad gaskia ba, ganin sa cikin tashin hankali yafi komai d'aga mata tunani, ji tayi an cire key d'in ya shigo, bata d'aga kai ba ta cigaba da kukan ta, cikin sauri ya k'arasa inda take ya fisgo hannun ta ta mik'e tsaye, bai tsaya jiran mai zatace ba ya ja hannun ta suka fice a room d'in.


Zaljameel batayi yunk'urin kwace hannun ta cuz bata da wani kuzari a jikinta suka fita, parking space ya nufa ya d'auka wata golden Prado ya tura Zaljameel a front sit ya dawo ya shiga motor d'in ya fara driving, ganin ya nufi hanyar fita daga masarautar yasa Zaljameel ta tsure, kallonsa tayi idonta da hawaye, tana son tambayarsa inda zasu amma yanayin fuskarsa bai bata dama ba, hakan yasa ta tsuke bakinta ta cigaba da kuka mara sauti. Gudu Jawad yake kamar mai shirin tashi sama, Zaljameel ta gama tsorata da al'amarin Jawad, ta runtse idonta dan a zahirin gaskia bata tunanin zasu je inda yayi niya ba tare da sunyi accident ba.


A dai dai wani babban hospital Jawad yayi parking, sai da ya harari Zaljameel sannan ya fita yaja hannun ta suka nufi ciki. D'aga kanta tayi taga inda suka zo, ganin Jawad & Zaljameel special hospital tayi rubuce a jiki, a razane Zaljameel ta fara k'ok'arin kwace hannun ta dan tasan tabbas Jawad ya shiga da ita hospital d'in asirinta ya tuno kenan. Dakewa tayi dan taga tsoro babu inda zai kaita, cikin d'aga voice ta fara magana "Ya Jawad leave me let me go," ta fara kokawar karb'ar hannun ta. Bata ishi Jawad kallo ba ya nufi office d'insa da ita, doctors da nurses nata gaida Jawad amma bata so yake ba.


Gwaje gwaje yasa wata doctor tayi ma Zaljameel na gane idan tana da pregnant, doctor ladi kam bata ga komai ba, ga results kala wajen 4 tayi printing, cuz Jawad bai yarda da test d'in ba har sai da a kayi sau 4, wani kallon tuhuma ya watsa ma Zaljameel, ji tayi kamar tayi fitsari,ga kunya ta lullub'e ta, tsaki Jawad yaja ya kuma kama hannun Zaljameel suka nufi motor, wata unguwa silient Zaljameel taga ya shiga, duk gidajen dake wajen abin kallo ne, daka gani kasan naira ta zauna, a k'ofar wani katafaren gida yayi parking, horn d'aya yayi gate man ya bud'e k'ofar ta sauri yana washe hak'ora, Jawad ya shiga da motor d'in ciki yayi parking. Da gudu gate man ya k'ara so kusa da Jawad ya zube yana kwasar gaisuwa, babu yabo babu fallasa Jawad ya amsa masa.


K'in fitowa Zaljameel tayi tana ta zare ido kamar shege a rabon gado, lol. Fincikota Jawad yayi ya nufi cikin gidan da ita, sai da ya danna password a jikin k'ofar sannan ta bud'e suka shiga k'ofar ta rufe da kanta.


Tsaye Zaljameel tayi tana k'arema gidan kallo, ya bala'in burgeta, yanayin ganin irin na turawa ne, ta shagala da kallon parlour taji an watso mata papers a jikinta, firgit tayi ta kalli k'asa inda suka zube ta kuma kalli Jawad dake zaune a 2cter ya yayi crossing leg yana ma Zaljameel wani irin kallo na kin shiga uku.


Gaba d'aya ya koma Yareema Jawad d'insa na asali, ya manta fara'a ballantana smiling, hankalin Zaljameel fa ya tashi, cike da izza Jawad ya fara magana.

"Keeeeee d'auka papers d'in nan kizo nan" ya nuna mata k'asa inda k'afarsa take.


"Kasan ta kalla ta kuma kalli Jawad, ganin babu alamun wasa a tare dashi, gasu a wani gida da bata son ta ina zata fita ba ballantana ta gudu yasa ta durk'usa ta d'eba ta nufi inda ya nuna mata sai dai ta kasa zama a k'asan kamar yarda ya umarce ta, dan Zaljameel itama akwai izza,hakan yasa take ganin bazata iya zama a k'asan k'afarsa ba.


Ganin bata da niyar zama yasa ya tashi tsaye yana zuba hannu a pocket yana kallon Zaljameel.


Wata iska ya fitar a bakinsa mai bayyanar da takaicin dake zuciyarsa ya fara magana "Zaljameel? Kinyi k'ok'ari sosai a abinda kika aikata, kuma na gane abinda kike nema, tun farko da kin fad'a mini da baki bamu wahala ba"

tsayawa tayi tana kallon sa dan bata gane inda ya dosa ba.

" Zan baki abinda kike nema Zaljameel, ciki kike buk'ata na miki ko, to zan miki kuma ke da gida sai kin samu cikin gaske Zaljameel" yayi wani killer smile ya kashe mata ido d'aya.


Cikin rawar murya Zaljameel ta fara magana "Ya... Ja.. wa.. d! Please karka mini haka, wallahi ni ba haka nake nufi ba, dan Allah kayi hakuri, wallahi na tuba, please ka maidani gida, wallahi zan janye abinda ya fad'a ma iyayen mu " ta fashe da kuka. Dana sanin abinda ta aikata, itakam Zahra ta cuceta data bata wannan shawarar, gashi bata taho da phone ba ballantana ta buga mata waya ta bata wani advice d'in. Upstairs Jawad ya shige ya bar Zaljameel na kuka.


SUMYNBASH CE 💋


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

YAREEMAH JAWAD

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

P.M.L

(We don't just entertain and educate, we touch the heart of the readers)


A romantic love story
2017

July 2017


Story & written by

SUMAYYA SALEES SADEEQ
Chapter 31 · 0% Book details