← Book details Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 22 OF 40

Chapter 45&46

Yareema Jawad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani doguwar mik'a Zaljameel tayi tana salati, a hankali ta fara bud'e idonta, a zabure ta mik'e zaune ganin gari yayi haske, phone d'in ta dake a gefenta ta jawo ta duba time, ganin lokaci yasa ta fito da idonta waje a tsorace ta hannu tasa ta dafe kanta, omg! Yau wane irin bacci nayi, ace har 12:00 pm tana kwance, zata iya cewa rabonta da bacci irin haka tun kafin a fara shirye shiryen bikinta.

Addu'ar tashi daga bacci tayi ta fara duba d'akin, so take taga alamun Areef ko ya shigo d'akin da tana bacci amma yarda ta kwanta haka tata shi, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ta fara nanatawa a ranta, mai yake shirin faruwa da ita ne, ina Areef yake, kar dai sace shi a kayi. Zuciyarta ta gama yarda da Areef ya b'ata hakane yasa ta d'aura hannu aka ta fara kuka, shikenan ni Zaljameel na shiga uku, Ya Allah ka bayyana Areef, Allah kasa yana hannu nagari, ni kam daria Zaljameel ta bani, ya za'ayi ace sauri kamar Areef ya b'ata.

Kukan da Annah taji shi yasa ta fito daga kitchen da gudu ta nufi d'akin Zaljameel hankalin ta a tashe, murd'a handle d'in Annah tayi ta fad'a d'akin, wajen Zaljameel ta nufa da ke rusar kuka mai ban tausayi, cikin kid'ima Annah ta fara tambayar Zaljameel meke faruwa.


Rungume Annah Zaljameel tayi tana kuka, cikin sheshek'ar kuka Zaljameel ta fara yima Annah bayani cike da shagwaba.


"Annah ya Areef bai dawo ba, tunda aka kawo ni ban ganshi ba, Annah zama nayi jiransa har bacci ya sace ni, yanzu ma na tashi ban ganshi ba, ta sake fashe wa da kuka.


Turk'ashi! Annah tace a zuciyarta, wato dama Zaljameel bata san Yareema Jawad aka aura mata ba? Lallai akwai matsala. Dama tasan Jawad bazai zo wajen Zaljameel ba, saboda ba ita yake so ba dole aka masa. jin Annah tayi shiru yasa Zaljameel d'agowa ta kalle ta, fuskar sharkaf da hawaye, basar wa Annah tayi ta fara tafa hannu,"Kai amma Areef da shiririta yake, ai na zata ya miki waya tun a jiya".

Zaljameel ta tsaida hawayenta ta zubawa Annah ido tana sauraron ta.

Annah ta cigaba "jiya bayan na fita waje sunzo da abokanan sa, ina tsaye ina gaida shi aka masa waya hajiarsa bbu lpy, an kwantar da ita a hospital, to shine fa hankalin sa ya tashi ya fita bai fad'a miki ba.


Ajiyar zuciya Zaljameel ta sauke, wayyo Allah sarki ai bai fad'a mini ba shi yasa hankali na ya tashi, Allah ya bata lpy.

"Ameen" Annah ta amsa.


Annah Zaljameel ta kalla, "Annah yaushe zamu je duba ta?".
Wani zufa ne ya yankowa Annah ta fara magana, "Haba Zaljameel, waya fad'a miki amarya na fita, ai ita kanta mara lpy idan taji cewa kinje bazata ji dad'i.

" Shikenan Annah Allah ya bata lpy "Ameen" Annah ta kuma amsawa.


Annah tabawa Zaljameel labarin nan ne dan ta kwantar mata da hankali, sai dai abinda Annah bata sani ba tarewar Areef a kusa da gidan Jawad, shin Areef da Zahra zasu k'i shiga part d'in Zaljameel ne ko yaya zata kasance.


Wayarta ta d'auka zata kira Areef Annah ta lura, Gimbiya mai zakiyi? Kallon Annah tayi, cikin sanyin murya tace!

"kiransa zanyi Annah"

Kirjin Annah ne ya buga ta kalli zaljameel!
"Aa Zaljameel, ni dai a gani na karki kirashi, saboda bai kiraki ba, ina tunanin yana wani abun ne shiyasa kika jishi shiru, amma nasan duk inda yake hankalin sa yana kanki Gimbiya Zaljameel".


Sanyar yar ajiyar zuciya Zaljameel ta sauke ta d'auke phone d'in a kunnenta ta fara k'ok'arin tashi a bed d'in, yatsina fuska tayi jin cikin ta ya murd'a she's feeling hungry, Annah ta kalla!.

"Annah yunwa nake ji" baki Annah ta washe, Gimbiya Zaljameel ai dole kiji yunwa, gaskia kinsha bacci, dubi har rana tayi"

Sake kallon window Zaljameel tayi, rana ta fito ta haske dunia.

"Ai break fast d'inki ya kammala sai ki yi wanka kizo kice"

"To Annah" mik'ewa Zaljameel tayi ta nufi toilet, sai da ta d'au wajen 30mint tana wanka sannan ta fito d'aure da towel a kirjinta, mirror ta nufa ta fara shafa, light make up tayi ta nufi gefen bed d'inta ta duba kayan da Annah ta zab'o mata, wani swiss lace ne, mai tsadar gaske, an mata d'inkin riga da siket, sun kama ta sosai, sun bayyanar da tsantsan kyan Zaljameel, d'auri ta kashe ta d'auki chewing gum mai k'amshin pineapple ta zuba a bakinta ta na tauna a hankali,dining area ta nufa. Nan ma yaji kayan alatu ya tsaru iya tsaruwa.


Tana fitowa kuyangu suka fara bajewa suna gaishe ta, da sakin fuska ta amsa musu! parlour d'in ta k'arema kallo shima ya tsaro, an mishi decoration har yaso ma yayi yawa,ko ina fes sai kamshi dake tashi. murmushi Zaljameel tayi dan tana son taga ko ina tsaf kuma tana son k'amshi.


Kuyanga d'aya taja mata kujera ta zauna cike da k'asaita, d'aya kuma tayi sarving nata abinda take so, bayan ta k'oshi ta nufi parlour ta zauna kuyangun ma suka zauna a k'asa.


Yareema Jawad Zaune a fada gaban mai martaba, sanye yake da wani yadi irin shara sharan nanAsh colour, kansa da hula sumar sa ta kwanta luf, yayi kyau sosai.

"An gaida Yareema mai jiran gado" bai kalli inda suke ba bai kuma ansa ba! ya gaida sarki cikin kulawa mai martaba ya ansa, a hankali ya fara magana irin ta sarakuna.


"Yareema Jawad na kira ka ne dan in sanar da kai ya kamata ka karb'i hospital d'in nan dana sa aka gina maka ka cigaba da kula dashi, dan dama na rabo ka da London dan ka taimaka wa talakawan mu ne".

Mamaki bayyane a fuskarJawad ya kalli sarki!

"ranka ya dad'e dama an gina hospital ne?"

"Eh Yareema nasa an gina hospital ansa masa sunan kai da Zaljameel, J&Z special hospital"

Ji yayi gabansa ya fad'i jin sunan Zaljameel beautiful face d'inta ya bayyana a fuskar sa, wani smile yyi sannan ya gyara zama ya kalli sarki!

" Nagode mai magana, Allah ya k'ara girma da d'aukaka"

"Ameen" Sarki ya amsa, fadawa ma suka amsa.

Tashi yayi bayan sun gama magana da sarki nan da one week zai fara zuwa aikin.


Tafe yake ya nufi part d'insa Bala na biye dashi, phone d'insa da ke hannun Bala ta fara ringing, Bala ya duba yaga Areef, cikin sauri ya d'aga dan kar ya katse, ya mik'awa Jawad, karb'a Yareema yayi ya kara a kunnensa.


"Ango! Ango! Ango na amarya"

Areef ya fara tsokanar Jawad, murmushi Jawad yayi wanda sai da beauty point d'in sa suka lotsa ya fara magana!.

" Areef ya a kayi ne? Ai banyi tunanin zaka kirani yau ba dan nasan ana chan ana kwasar soyayya"

Areef da ke zaune a parlour sa Zahra Rungume a kirjinsa ya k'ara matseta a jikinsa, yana daria," Ha Jawad ai kaima kasan fad'a b'ata baki ne ya Amarya Zaljameel? Sai da Jawad ya d'auke wuta ya saci kallon Bala dan yasan bai maga Zaljameel ba, amma kuma bai san dalilinsa nayin hakan ba.

"Tana lpy"

To ka gaida ta, dama ina son fad'a maka ka shirya zamu je gaisuwar surukai da yamma, "Surukai?"

"E surukai "

" Gaskia Areef baka da hankali, Mom da Dad d'in zanje gaisarwa, gaskia bazan iyaba, sai dai na raka ka mu gaida Alh Zahradden "


" Ok bbu damuwa tunda ka zama dan kanka, su d'au yarsu su baka kace baka zuwa ka gaida su, ka shirya kawai malam dole muje "

Shiru Jawad yayi jin hakan Areef ya kashe wayarsa dan yasan Jawad bazai ce ya yarda ba zashi ba, amma shirunsa ya tabbatar masa daya gamsu.


Alh Zahradden suka fara gaisarwa sannan suka nufi part d'in su Zaljameel.


Mom zaune a parlour ita da Nawal! Nawal nata zuba mata rigima sai an kaita wajen Zaljameel, tana cikin bata hak'uri akan ta bari anjima zata sa akaita, sukaji muryar Jawad! Da gudu Nawal ta nufeshi tana

"Oyoyo Uncle, wallahi sai ka tafi dani gidan ka naga Aunty Zaljameel, sai hawaye"

D'aukarta yyi yana share mata hawaye, "haba Nawal! Indai akan zuwa ne to karki k'ara kuka dake zan tafi"

Peck ta bashi a kumatu "Thanks my Uncle, dats why i love you".

Sauke ta yayi ya nufi cikin parlour dan Areef da sauran Friends d'insu har sun zauna.

Bajewa yayi a k'asa ya gaida Mom kansa a k'asa, kunyar Mom yake ji,bayan sun gaisa suka yi sallama suka tafi, tare da Nawal.


Zaljameel zaune a main parlour d'in gidan tana duba pic d'in biki, sanye take da wani material green colour d'inkin doguwar riga, ta amshi jikinta, high neck aka mata duk boobs d'inta a rabinsa a waje yake, d'auri tayi emergency, jikinta na tashi k'amshi.


Muryar da taji ta nufo parlour yasa numfashinta ya kusa d'aukewa, bata gama tunani ba taji sallamar sa a parlour ya shigo hannun sa rik'e da Nawal,Zumbur tayi ta mik'e tsaye tana kallon bayan Jawad ko zata ga Areef ya shigo, kallo d'aya ya mata ya d'auke kai ya nufi part d'insa, da gudu Nawal ta nufi Zaljameel da tsanin farin ciki, gaba d'aya tunanin Zaljameel ya birkice, to mai Jawad yazo yi part d'in ta,? wata zuciyar tace wajen Areef yazo, Areef d'in da bayana nan ta sake tunani! To ko ai koshi yayi ya d'auka masa wani abu, "Yeah hakane ma, ai ko shi yayi" zuciyarta ta gasgata hakan.

Rungumar da Nawal ta mata ya dawo da ita tunanin ta, nan ta fara murna ta kuma kama hannun Nawal suka shiga ciki dan bata b'ukatar sake had'uwa da Jawad.


SUMYNBASH CE💋


🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

YAREEMAH JAWAD

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮


©PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
P.M.L


A romantic love story
2017


July 2017


Wannan page d'in naki ne maman khady, Allah ya bar k'auna ya kara zumunci 👌🏻❤


Ina mik'a gaisuwa ga yan pure moment of life writers, kungiyar da bbu irin ta, Allah ya kara had'a kanmu ya k'ara mana son juna, Allah ya k'ara mana basira ameen. #ana tare💋.
Chapter 22 · 0% Book details