Sashe 31
Ungozoma Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ga ta ga fatalwa sai ta ji fatalwar ta kai hannu kan gashin kan nata ta ce "Bari na miki kitson ko" "Yau na ga abu banbarakwai wai namiji da suna Hajara, in ba dan fallasa auren bashi ba, ni cewa na yi ki mini kitso ki bar ni mana in yi da kaina, ai guntun gatarinka ya fi sari ka bani, duk da dai na san idan makaho ya ce a yi wasan jifa to ya taka dutsi ne amma dai kai ka fa a? Uwar sarki a doki ai kura ma ta san gidan mai babbar sanda sai dai kamar da gaske wai karuwa ta ga noman an koli" Gwaggo ta fa a a ranta jikinta yana karkarwa jin hannun fatalwar ya ta a gashin kanta, da alama dai da gaske fatalwar kitson za ta mata. "Wa ulna ya naru kuni bardan wa salaman ala ibarahim" Gwaggo ta daddage arfinta ta fa i addu'ar da ake tofawa mutum a wajen una idan ya one ita kanta dakyar ta yi ya i da baki da walwarta ta samu furta lafazin, duk da muryarta tana rawa har da disko ma. Fisgar gashin fatalwar ta yi da arfi sai kuma ta sake shi yadda Gwaggo za ta ji a jikinta. "Wayyo ni a garin nana wayyo ni, ni dodo na yi ya kai autan iya da baba har na fi" Gwaggo ta ara samun nasarar karanto wata wa a daga cikin tatsuniya da ake yi wa yara, yadda jikinta yake karkarwa za ka auka a cikin frezer aka saka ta ta au mugun sanyi amma ba komai bane sai tsoron da take ciki. Suuuu fatalwar ta tafi a kan iska ta tsaya a daidai kan Malam Lawandi da har lokacin yana ta shafar kai da sha ar hanci ganin layi ya zo kansa bai san lokacin da ya ara aimi wajen shafar kai da sha ar hancin ba, ganin tana dab da shi sai ma ya ara ha a wa da walar kunne. "Ai sai an yi sha ar hanci ake wanke fuska sai kuma a wanke hannu sannan a yi shafar kai sai kuma walar kunne ya biyo baya" "Allah bada lada!" "Bari ka gani" Cewar fatalwar tana mi a hannun ta da Malam Lawandi ya ji kamar wani arfe sai uban farata za o-za o, ta shiga shafa masa fuskarsa tamkar dai tana masa wankin fuska. "Iza wa a'atil wa i'eh, laisa li wa a'atiha kazibe, kafidatur rafi'eh, iza rujjatur ardu rujje" Malam Lawandi ya shiga karanto suratul wa i'a cikin kira'ar warshu yana karatun yana kuka. Kuka yake hawaye yana zuba kamar an bu e bakin famfo ga shi har lokacin suna ka ace a cikin babbar rigarsa su duka ukun Audu jin mahaifinsa yana karatu yana kuka sai shi ma ya shiga rusa nashi kukan, saboda an ce wai yi wa kanka hisabi kafin a yi maka, domin shi bai iya karatu ba sai shegen yawo sai gagara ya sa a gaba yau ga ranar addu'a da karatun al ur'ani to shi da bai iya ba. "Yau ni Audu, Aududu an Malam na ga ta kaina, ga shi zan ga abin da ya turewa buzu na i, na yi saki na dafe wai mace ta rabu da mai ku i ta auri talaka, ga shi na ga fatalwar nan ta sako mu a gaba sai in da mai ya are shiga motar mai ta i" Ya fa a yana rushewa da kuka tare da cigaba da tara hawayen nasa kamar yadda yake yi, dan ya fara sarewa tun da ya ga mahaifinsa ma da ya iya karatu ga shi yana yi yana kuka yana ganin kamar ma dakyar ya warto karatun saboda ru u bare kuma shi da cikakkiyar fatiha ma bai iya ba gwara ma wasu abin sai dai in ji ya yi ana fa Gefen Audu ta matsa ta tsaya ta ura masa idanunta da babu wayar idanu a ciki abin da ya ara ru a masa ciki kenan har yana jin tamkar zai fara gudawa, dan zuwa lokacin ya ji fitsarin nasa ya afe da alama ya arar da fitsarin marar ta shi. "Bari a tare maka haway... Tun kan ta arasa fa a Audu ya ce "Na hutar da ke dan Allah ki mini rai" "Haba an samari kyakkyawa ai aiki bai kamaceka ba" Ta fa a tana kai hannu ta shafo fuskar Audu. "Baba dan Allah ka bani addu'a ko ta korar she anun mutane ce ba sai ta she anun aljannu ba, ni ko addu'ar saka tufafi ce ma ka bani, dan Allah Babana Allah dai ya maka albarka, Baba ka bani addu'ar shiga kabari in za a saka ni a ciki in yi dan kar in yi fatalwa in ke tsorata mutane in na mutu" Audu yake ta fa a a gigice dan duk ya fita a hayyacinsa saboda tsabar tsoro. "Wa alfaya sayyidaha ladal baab, alu ma jaza'u man arada bi ahalika su'an illa an yusjana au azabun aliim" Malam Lawandi da ba ya ma fahimtar maganar an nasa Audu yake janyo ayar da bai fara daga farkonta ba, shi kansa da za a saka masa wu a a wuya bai ma san a wace sura take ba ya sai ji ta zo masa a bakinsa ne. "Ba zan iya ba Baba, ya kake fa a mini karatun kamar kana mini ori, kai da za kake fa a da aya da aya amma ka kamo aya mai wahalar fa a dan Allah ka fa o mai saukin fa a ko ni ma na ku uta" Ya fa a yana kuka yana karkarwa dan har lokacin hannun fatalwar yana kan fuskarsa tana share masa hawayen. "Ma agne anhu maluhu mawakasab, sayyasla naran za ta lahab, wa mar'atuhu hammalatal ha ab" Malam Lawandi ya cigaba da karanto duk ayar da ta zo bakinsa. "Zan bige kar ka bige birin kano azumi ne. Baba ka je gida ana nemanka rabu da ita yale ta ashin miya ne babu" Audu da ya samu nasarar fa ar wa ar tashe da ake yi da azumi ya fa a yana kuka. "Wayyo Audu na sani ana nemana dama, to ka san dai halin da muka tsinci kanmu a ciki, amma na san dama dole a bu ace ni a gida musamman Zuwai da Talatu masu na uda amma babu yadda na iya ne fa an da ya fi arfinka wasa kake mayar da shi" Malam Lawandi da jin Audu ya ce Baba ka je gida ana nemanka karaf a kunnensa dan tunaninsa ko fatalwar za ta sallame shi ta ce ya tafi. Audu bai ma san ana yi ba wai kunu a ma ota, shi fatansa kawai ya zo kan ga ar fa ar wani abu wanda zai sa fatalwar ta auke hannunta daga fuskarsa kuma ta matsa daga wajensa ko ya daina jin tashin hankalin. "Ma ji ma gani wai an rufe tsohuwa da ranta " Gwaggo ta fa a a ranta jin Malam Lawandi yana neman hanyar ku uta. "Assalamu alaikum, alaikum, alaikum a wannan rana. Za ki auki ayansu, ayansu, ayansu a wannan rana, wane ayan kike so kike so, kike so a wannan rana za na baki INGOZO, INGOZO, INGOZOMA, sai ki ha a da Baba da Baba da Baba a wannan rana, ni kuma sai ki bar ni, ki bar ni in tafi gida" Audu ya faro wata wa ar dan ya samu fatalwa ta yale shi ya tafi. "Ka ji wal uba, wal uba, wal uba a wannan rana, sai dai ka bada ubanka, ubanka amma ba da ni ba" Gwaggo ma ta fa a cikin baitin wa ar da Audu ya yi. "Wallahi ba ni ba, ba ni ba , ba ni ba a wannan rana" Malam Lawandi ma ya kar i baitin dan ganin ya janye kashin kajin da suke son ya a masa. "Ku ka ai za ta auka dan kuntsufa a wannan rana" Audu ya fa Fatalwar dai ba ta ce komai ba ta dai auke hannunta daga fuskar Audu ta yi gaba wato ta fara zagayowa ta bayansu, Audu kuma wani sanyi ya ji a ransa dan tunninsa fatalwar ta ji da in wa arsa ne, kuma ta auki shawararsa za ta auki Gwaggo Ramma da Malam ta tafi da su shi ta yale shi. A NAN NA KAWO ARSHEN FREE PAGES MAI BU ATAR SHA ATAWA DA LABARIN UNGOZOMA HAR ARSHE ZAI BIYA 500 TA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SHAIDAR BIYA TA 09013181851 KAR KI BARI A YI BABU KE DAN LABARI YANZU AKA FARA ABIN DARIYA YANA GABA SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO LD7 WPS Office Normal Times New Roman Times New Roman Calibri Calibri !%),.:;>?]} $([{ 363768c9100b45a89efc1e45d7efe972