← Book details Ungozoma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 31

Sashe 2

Ungozoma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Page 1 Dare ya tsala, ko ina tsit kake ji babu abin da yake tashi sai kukan tsintsaye da karnuka. A can cikin akin Gwaggo Ramma ita ce kwance a kan gadonta na kara irin na mutanan da in nan tana shirgar bacci sai aran munsharinta da ke tashi a akin tamkar an sha ewa zakara wuya. Mai Gari ma da yake can yashe a kan tabarmar kaba yana sharar nasa baccin ya aga kan nan nashi sama baki a bu e sai sakin munsharin yake a gefe aya yana sakin tusa a kai -a kai saboda alalar da suka ci da rana sannan ita suka ara ci kafin su kwanta. Juyi Mai Gari ya yi a cikin baccinsa ya ji wani uban wari da ya durfafi hancinsa hannunsa ya kai ya bu e mayafin da ya rufa da shi sabo da sanyin da ake zugawa, jim ka an cikinsa da ya kumbura ya shiga ara ulululuuuu bakam ya tashi a 360 ya yi jifa da abin rufar sai gashi a zaune hajaran majaran yana jefa idanu a cikin duhun akin warin da ya ha akin ya sanya shi sanya hannu biyu ya toshe hancinsa. aran tusar Gwaggo Ramma da ta saki guda biyu a jere su ne suka daki kunnuwansa a take cikin Mai Gari ya cigaba da hautsina wa. "Kayyasa! Bar ganin ka tara ka kiyayi mai nema, ta i sinasir wannan tusa da kike yi Ramma kamar an rufe mutum a akin mushe duk kin ha aki da wari" Cewar Mai Gari a fili yana ara danna hannayensa a hancinsa jin warin tusar tasu gaba aya ya ha akin. Hannu ya kai ya sakarwa Gwaggo Ramma wani e a wabrin afarta a ki ime ta tashi ta zaune mazaunanta sai kuwa aran wata tusar ya fito darrrrrr. "Subhanallahi! Ni Ramma a cikin masai (Toilet) Nake ko a ina? "Ta furta a fili jin warin akin ya game ko ina. "Babu wata masai a cikin akin ki kike haba! Ina dalili duk kin kumbura mini ciki tun da na tashi da aran fitar iskar mazaunanki na fara cin karo tamkar ana sace iskar tayar motar tifa duk kin hargitsa mini cikina... Kafin Mai Gari ya arasa maganar da yake yi fitowar wata atuwar tusa mai cike da mugun ara ta masa shamaki da sauran maganar da yake son fa a, da kallo mai kamar harara da kuma ka raina mini hankali Gwaggo Ramma da ta kunna tocilan ta bi Mai Gari dan sai yanzu ta tabbatar da cewa ashe dai ba ita ka ai ta cika aki da wari ba har da shi. Kunya ce ta sanya Mai Gari ya auke kai dan a halin da ake ciki ma yanzu wata tusar ce take son fito masa amma yana ta ya i da ita a kan kar ta su uce ta fito dan haka sai ya shiga murtsika mazaunansa a kan tabarmar kabar da yake zaune wacce ko arzi in shimfi a bata samu ba. Amma cikin rashin sa'a duk arinsa na ganin ya danne tusar nan haka ta ringa arin mahaukaciya da arin nasa har dai ta samu nasarar fitowa tare da bada wani sauti da ya sanya Gwaggo mi ewa tsayi ba tare da ta san hakan ko ta shiryawa hakan ba dan ita dama a tsorace take da gidan nan da suka tare a jiya, wanda taku ka an za ka yi daga gidan ka je katangar ma abarta da yake ma katangar ba wani tsayi ne da ita ba idan kana daga tsaye kana iya hango kaburbura, wannan dalilin ne ya sanya aran fitowar tusar Mai Gari hautsila an hanjin cikin Gwaggo Ramma. A take cikin nata ya wani birkita sai ita ma ta saki tusar et, lokaci guda ta ji wata gudawa ta matso ta. "Na shiga uku ni Ramma, in banda abin majinyaci na mai magani ne, yanzu a cikin daren nan anya kuwa zan iya zuwa bayi, in sauke nauyin cikin nan nawa, gashi kuma gudawa bata da ha uri ko mis ala zarratan idan ta taho dole ne sai mutum ya tsiyayar da ita sannan zai samu salama... Kafin ta dire maganar da take yi a zuciyar ta Mai Gari ya zabura ya mi e tsaye a can gefen tabarmar da ya kwanta ya hangi tashi tocilan in dan haka bai yi asa a gwiwa ba ya kai hannu ya auka da sauri ya juya ba tare da ya bi ta kan Gwaggon ba ya nufi hanyar fita daga akin dan shi a yadda yanzun nan gudawar ta matso shi ba ya jin ko minti biyu zai iya jurewa ba tare da ya yi kashi ba dan haka ya aura aniyar ficewa ya riga matarsa shiga bayi sabo da ya san kaf gidan dai bayi aya ne kuma ya san matsawar Gwaggo ta riga shi shiga bayin nan sai ta Allah dan ya san zai iya sakin kashin na a wando kuma abon kunya ne a ce shi Mai Garin GUMURZU ya yi kashi a wandonsa. Gwaggo kallon Mai Gari ya suri fitilarsa ya nufi ofar fita sai zuciyarta ta raya mata cewar shi ma kashin zai je, dan ta san a yadda yake da tsoro kamar farar kura babu abin da zai fitar da shi daga akin a daren nan sai dai kashi, dan ta ji yana tusa kuma ta tabbatar bayi zai yi wa dirar mikiya, wanda hakan kuma tamkar ya i zai yi da rashin fitowar nata gudawar wani kallo ta yi wa bayan ko iyar rigar sanyin jikinsa kafin cikin azama ta yi taku biyu ta rafko asan rigarsa, Mai Gari jin an ri e masa rigarsa sai da ya ji tamkar ya saki ihu dan ya ji kashinsa daf yake da fitowa gashi Ramma za ta masa cikas in fitowar kashin a kan lokaci. "Wallahi in dai bayi za ka shiga sai dai ka jira har in shiga in fito dan kashina yana bakin boda daf yake da hantsilowa babu abin da ya fi kamata da kashin nawa sai dai ya ji shi a cikin duniyar masai(Toilet) " Cewar Gwaggo Ramma cikin sababi. Mai Gari ji ya yi bashi da arfin yin magana dan yana bu e bakinsa gani yake kashin ne zai zubo dan haka a hankali ya juyo ya fuskanci Gwaggo Ramma ya aga hannu biyu ya fara mata maganar bebaye dan ba ya so ya bu e bakinsa gudawar ta fito bai shirya ba.Wata uwar harara Gwaggon ta jefa masa ta ja rigarsa ta mayar da shi gefe guda dan bata jin tana da ishashshen lokacin da har za ta tsaya kallon zancen bebayansa bare har ta gane mai yake so ya fa a mata. "Kar ki mini haka Ramma" Cewar Mai Gari cikin ra a-ra a dan ba ya so ya bu e baki sosai kashin ya zubo. Ai kuwa cikin rashin sa'a maganar da ya yi duk da ya yi ta ne cikin ra a amma sai dai kashin nan ya yi masa barazanar fitowa, da sauri ya saki fitilar hannunsa ya kai hannu biyun ya dafe mazaunansa saitin mafitar kashin dan yana ganin hakan shi ka ai ne salama a gare shi na hana fitowar kashin ba shiri. Gwaggo kuwa ko ta kan Mai Gari bata bi ba, ta bu ofar bakam ta fice a sukwane tana fatan Allah sa dai ta kai har bayin ba tare da gudawar ta zubo ba bare har ta ata zaninta, takalmin ma afa aya ta saka ayar kuma bata samu damar sakawa ba tsabar yadda kashin ya matse ta a hannu ta auki afa ayar takalmin. Cikin gudu-gudu sauri-sauri ta tasamma hanyar da za ta sada ta da bayi da yake da an tazara daga aki zuwa bayi. Salele da shi ma kumburin cikinsa ne ya tashe sa yadda lokaci guda ya ji gudawa tana neman hanyar fitowa bai yi wata-wata ba ya kunna fitilar wayarsa mai madannai ya bu ofa ya fito burinsa kawai ya gan shi a cikin bayi, yana fitowa ya saka takalmansa a baibai da gudu ya tafi sai da suka kusan cin karo da Gwaggo da ke nata saurin mai ha e da gudu tana ri e da afar takalmi a hannu da kuma fitila, ganin ita ma ta doshi hanyar bayi mamaki ya rufe shi, kafin ya dawo daga mamakin ya hango Kakansa Mai Gari shi ma ya taho da gudu hannayensa dafe da mazaunansa shi ko arzi in saka takalmin ma bai samu ba. "Bala'i yau ake yinta wallahi sai dai ku hau layi bayana dan babu wanda zan aga wa afa ya shiga bayin nan sai na shiga" Cewar Salele a zuciyarsa yana ara aga afa ganin Gwaggo da gaske neman rigaye shi zuwa take yi. Gwaggo da har wani numfashin gajiya take saukewa sai dai ganin ta kusa urewa hanyar bayin gudu sai kawai ta an ji da i a ranta, amma kuma tana dab da ofar bayin kawai sai ganin Salele ta yi kamar wanda ya diro daga sama ya shiga gabanta zai shige cikin bayin. Wani irin zaro idanu ta yi tare da bu e baki ta shiga cewa. "Salele ka yi uwarka da ubanka da muka kawo su duniya, kai kuma suka kawo ka duniya kar ka shiga bayin nan wallahi idan ka shige ka shiga ha ina kai hatta da alhakina wallahi ka auka dan ko afar takalmi aya ban samu zarafin tsayawa saka wa ba duk dan in je in sauke nauyin cikin nan nawa... Kafin ta kai arshen maganar Salele da ko kallo bata ishe shi ba, burinsa ya je ya tsugunna, haka ya shige ya barta a bakin ofar, dan duk saurinta ya riga ta arasawa. A hankali ta ago afafunta ta baro bakin ofar sabo da wani wari da ya far wa hancinta, ga aran gudawar Salele hakan ya tabbatar mata kashin ta yana dab da zubowa. Jin hakan sai ta ha afafunta ta matse su ta an sunkuya duk dan ya i da gudawar kar ta fito. Mai Gari da shi tsabar ru ewarsa bai hangi Salele ba ma yana arasowa ganin Gwaggo a sunkuye sai ya ji ransa fari al dan haka ya nufi ofar bayin gadan-gadan. Yana shirin afkawa sai ya jiyo
Chapter 2 · 0% Book details