← Book details Nida Diyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 48

Sashe 6

Nida Diyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kasa ta zauna gefen Daddy tana facing Big Daddy, muryanta k’asa k’asa ta soma magana, sai kayi da kyar kafin kaji abinda take faɗi. “Please alfarma nake nema gurin ku, kunsan cewa tun dana ke ban taɓa saɓa maku ba?

Ina kokarin fulfilling all righteousness a matsayina na yarinyar ku. Banida kamar ku a fadin duniya, dama daga Allah, Manzaninsa tareda sahabbai kune next danake bi.” Gyara zamanta tayi tare da durk’usawa, hannunta biyu a harɗe saita sunkuyar da kanta k’asa, “please kada kuce na aure……”

Tas…. Mommy ta dauketa da wawan mari, “halan nan gurin sa’anki ne ke zaune? don raini ina kokarin k’wato maki hakkin ki shine zaki watsa min k’asa a ido wai ga zance ga magana, dan ace nike sangartar dake”

Ya isa haka Hajia, “ai gwara ta faɗi ra’ayinta amma bazai canza komai ba saboda sai anyi” Big Daddy ya chapke. Ita kuma Mommy ranta ya baci saboda da Fadeela bata fito ba data san yanda zatayi ta ruguza abin, amma yanzu tana cewa kule za’a ce sun haɗa baki ne. Amma tabbas yau saita shiga jikinta da duka, tunda ta ruguza mata plan dinta bcs of her stupidity.

Fadeela tana Sheshek’ar kuka ta koma ɗakinta, shi kuma suka mayar da idan su kan shi, wanda baka ganin komai sai green eyes kawai, “Kanada ja ne?” Alhaji Sulaiman ya faɗa. “Gaskiya kuyi min afuwa, ni inada wanda zan aura kuma alamomin munafiki ne idan yayi alkawari ya saɓa” Mallam rufe mana baki, Abba yayi magana a karo na farko tun bayan sun gaisa.

“Nifa bazan aureta ba” ya fada tareda mikewa, kallonsa kowa keyi “Grand Kadi kayi hakuri akan abinda nayi ma yarka which nasan Baka sani ba, but bazan aureta ba saboda wasu dalili nawa”

wucewa yayi ya nufe hanyar kofa, “Naufal karka bar gidan nan batare da na baka izini ba” Abba ya faɗa mashi amma yayi kunnen uwar shegu yayi ficewarsa. Yana tafe yana haki, “wai Bad luck za’a haɗa ni da ita! Ta kashe ni kenan da bak’in jininta. Sam Sam bazai yiwu ba” yana tafe yana faɗa ma kansa har ya kai wajen motarsa.

Haka ya fito daga cikin gidan su Fadeela sai yayi shawara yaje gurin Mamansa ya shawo kanta ta mara masa baya dukda tana fushi dashi akan yawan zuwa wajen Anty Saudah tareda daukar ɗawainiyan Miemie.

Ya hau babban titi yana tsugaga gudu baji ba gani, kuuuu yayi kokarin taka birki yayin daya lura da ɗan ga ruwa yana tura amalanken sa. left Naufal yayi kokarin zuwa cikin tashin hankali tareda rankamo salati but ashe masu Fruits da kuma balangu suna wajen wanda shi baima lura dasu ba. Saisaita steering dinsa yayi a firgice but sai da yayi Karon rago dasu. Nan take ya sume sanadiyar buga kanshi daya yi.....

Su kuma mutanen wajen salati suka rinka jerowa, daɗin abin kowa ya kauce. Gaggawa aka je bashi, anata dambe da mota da kyar aka fito dashi. Tun sanda aka fara cincibarsa ya farka amma baice komai ba saida aka ajiye shi.

A hankali ya ware idonsa ya rinka kallon wanda suka ceceshi. “Ina fatan babu wanda yaji ciwo?”

“Alhamdulillah babu kowa ya kauce” wani dattijo ya amsa shi.

“Amma Mallam kai ɗan rainin wayo ne, dan wulakanci zaka hau titi kayi ta zura gudu kamar na ubanka” Wani matashi ya faɗa

“Toh wallahi ba zanyi asara ba, ko a bayani kuɗin Fruits ɗina kona tada zaune tsaye yanzu yanzu” ya faɗa yana zaro ido tareda lakwansa baki.

Shiru Naufal yayi saboda yasan duk me ya faru dashi laifin shi ne, iyaye ba abin wasa bane. Bazai disrespecting dinsu hankali kwance ba. Gaskiyar Mallam Bahaushe ne daya ce “Rashin bin maganar iyaye hatsari ne” gashi abin ya zama mai hatsari physically ba a baki kawai ba.

Su kuma su Abban Naufal shiru sukayi kunya sai ɗawainiya dasu takeyi. Mommy ce tace, “naji yayi maganar wani abu ya faru, halan lafiya?” Nan Abban Naufal da kanshi ya labarta masu daki daki abinda ya faru.

Mommy shiru tayi kada ta tozarta Daddy ace matarsa batada kintsi yasa bata k’ara cewa komai ba. Amma bazata yarda ayi auren nan ba, bata taɓa jin inda aka ɓare gyaɗa aka tsinci mota ba.

Su Engr bada hakuri suka kara yi kuma fuskar Grand Kadi a sake. Shi kuma Alhaji Musa yace hakuri ɗaya zaiyi idan aka sa Naufal yayi auren nan. “Kar ka damu, nima auren nake so yayi tuntuni amma yaki. Aiko gawarsa ne sai an daura” Engr ya jaddada.

Grand Kadi har mota ya rakasu ana raha. Shi dai bashida abin cewa, duk abinda Big Daddy yace shi za’ayi. Saboda matsayin shi yafi karfin haka a wajen shi, yayi mai hallaci sosai a baya saboda haka bazai watsa mashi k’asa a ido ba. Ita kuma Mommy idanta ya cika fal da hawaye, kullum addu’a take Allah ya ba Fadeela miji mai tausayinta amma gashi za’a haɗata da wannan gwaskar.

Haka Naufal ya wuce wajen motarshi domin ya dauko masu kudi. Dama yayi withdrawing kuɗin dazai lik’i ne. Dubu goma sha biyar yaba mai Fruits su rage asara, sai yaba mai nama dubu goma. Shi kuma mai ga ruwa aka bashi dubu ɗaya da ɗari biyar, sauran mutanen wajen su uku ya basu dubu ɗaya ɗaya.

Haka ya koma motarshi datayi damaging, glass sun farfashe handle din kofa ya lankwashe. Komai dai babu kyan gani, ya shiga ya fara tuk’awa sai motar tanata hayaki tareda k’ara kamar Vespa. Tafiya yakeyi kamar bayayi saboda bashida maraba da kunkuru. Kowa kallonsa yakeyi yana kwafa bcs duk ya ishesu.

Abban Naufal ya kira Anty Saudah a waya yaji ko Naufal na wajenta amma tace rabonta dashi tun kafin yaje dinner. Abba ya rasa a inda Naufal ya koya mugun ɗabi’a amma ya dauki alwashin anyi na farko anyi na karshe. Zuwa gida yayi ya wuce bayi kai tsaye yayi wanka, daya fito saiya saka wani Ash jallabiya haka.

Daukar jaridar Daily Trust yayi ya wuce Varenda yana jiran shigowar Naufal, zama yayi a kujerun wajen saiya ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya. Baya ma gane jaridar kawai k’afarshi yana karkarwa.

Sannu a hankali Naufal ya rinka gungura motarsa har gidansu, k’aran ɓararan motan ya sanar dakowa gashi nan zuwa, ga kuma hayaki kamar ana gobara. Yana zuwa mai gadi saida ya leka ta karamin gate yaga waye kafin yagane Naufal ne.

Shikuma Naufal tunanin shi ɗaya yazai yi da annoban ta, wai ace daga zuwa gidansu har ya kusa mutuwa, ina ace inuwar su ɗaya.

Yana isa parking lot ya ajiye motarsa zai wuce BQ inda ɗakinsa yake. Sam baiyi tunanin zaiga kowa war haka daren nan.

“Mallam zo nan” Abba ya faɗa fuskarshi babu wasa. Sum sum Naufal yaje waje, tun yau abubuwa mara misaltuwa ke faruwa dashi, yanzu a gajiye yake yayi likis. Yana isa ya ɗuka kasa alamar girmamawa.

Abba baiyi wata wata ba ya wanka mashi mari kyawawa guda biyu. “Faɗa min daga inda kake ka shigo min gida cikin dare kamar ɓarawo?” kanshi duk’e baice komai ba, shiru kawai yayi yana tunanin irin marin da zai rinka dauke Fadeela dashi. Saboda aurenshi zai zamo mata bak’in canji a rayuwarta.

#NiDaDiyata

*All rights reserved*

💥∂ιмρℓεs💥
[8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

💦 Ni Da Diyata 💦

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples

💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦

✨✨✨Page 8 ✨✨✨

*A LESSON*
The Holy Prophet(SAW) said, "Stop doing everything during the ADHAAN(calling of prayer), even reading the Holy Quran, the person who talks during the Adhan shall be deprived of saying the KALIMATUSH-SHAHADA when he or she is about to die! May Allah guide us...

*********

“Dama na danyi wani  k’aramin hatsari ne” Naufal ya amsa ma Abba still yana ɗuk’e a kasa. Shiru Abba yayi na wajen 5 minutes yana tunani irin halin Naufal. Ajiyar zuciya yayi abin duniya ya isheshi sai yace “Wato sabon alkawarin daka dauka ma kanka kenan koh?’’

“Yanzu bazaka  barni na sha ruwa a garin Bauchi ba koh?  Idan an hanaka mutuwa sai ka suma. Shi kenan yanzu dan na haife ka banida sauran kwanciyar hankali a tareda ni kuma. Kana abu kamar k’aramin yaro.”

“Wai tsakani da Allah Naufal mena rageka dashi da kake so bakin cikin ka ya kasheni. Haba mana! Bafa kai kaɗai na haifa ba balle kamin haka, idan ka gaji ne sai kayi min bayani na yafeka a cikin yarana then we can call it a day”

“Kayi hakuri dan Allah Abba Wallahi bai kai zafin haka ba, tsautsayi ne kawai aka samu. Kuma wanda nayi hatsari a gefen su ko qurjewa basuyi ba” Naufal ya faɗa yana tunanin yayi abin arziki. “Ai bakayi gwaninta ba, daka kashesu ne saina san ka cika namiji” Abba ya amsa.

Ita kuma Bilqees ta tashi karatun TDB saboda tanada test saita ji hayaniya a varenda. A hankali taje taga ta lek’a sai idonta yayi arba dana Abba. “Zo nan” ya faɗa ita kuma ta fara jan k’afa duk takaici tace a hankali “I don dieooo.... Meya kawoni wajen nan” haka taje wajen Abba ta durkusa “Gani Abba”
Kallon sama da kasa yayi mata saiya ce, “kije ki tada Abla da Maman ku sai kuzo ku sameni gabaki ɗayan ku a falo” ya faɗa tareda kallon Naufal alamar harda shi.

20 mins later....

Duk suna zaune a falon Engr, Mama da Naufal ke kan one one seater, su Abla ana k’asa ana turo baki. Mama tana ɗan jijiga kafarta ta cika tayi fam. Ita bata ga dalilin da za’a tasheta cikin tsakar dare ba?  Wani zuciya ya raya mata ai aikin Anty Saudah ne. Tsaki tayi a ranta sannan ta faɗa “Nayi maki nisa mahaifiyar mahaukaciya”

“Abba gamu mun zo” Abla ta sake maimaitawa a karo na biyu. “Ai na ganku since niba makaho bane” shiru ya k’ara yi wanda Fallon baka jin komai sai motsin jaridar dake hannunsa. Kafarsa ɗaya akan ɗaya yana karkaɗasu, shikuma Naufal bai taɓa gajiya kamar na yauba. Kwakwalwarsa sai chaji yake yi a hankali don komai yayi masa zafi.
Chapter 6 · 0% Book details