← Book details Nida Diyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 48

Sashe 5

Nida Diyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tasss ya watsa mata mari, sai ya k’ara dauketa da wani ta ɗaya bangaren, marin daya yanka mata mai sa fitsari a jiki ne kuma dole kaga taurari.

Ni kuma a razane naja da baya dana lura azzalumin mutumin dana haɗu dashi kwanaki ne, “dole a rina wai an sace zanin Mahaukaciya”

Dama suna bashi haushi sai ya lura “Bad Luck” ne a gabansa kuma ga earpiece a kunnenta yasa ko tunani baiyi ba ya watsa mata frustration dinsa.

Tabbas sukuku da mood swings dayake ta samu yau sanadiyar zaiyi gamo da ita ne, bcs duk wanda ya hadu da ita yayi gamo. Idanunshi suka kad’a bcs Bad Luck din dake binta yasa ya fadi ɗazu a bayi.

Karkarwa na somayi bakina sai rawa yakeyi, gumi nake tayi duk na jik’e hawaye sai malalo min yake kamar bakin teku. Baya na rinka ja ina kallon mai zai biyo baya, daɗin abin hankali mutane baya kanmu sabida sunata cin abinci.

“Yanzu dai na tabbatar a jakunan duniya, kinfi kowa jakanci” ya faɗa a hasalce. Tsuru tsuru nayi bance komai ba. Mansura ce tazo da sauri “Kayi hakuri Mallam, Fadeela is very clumsy” “Kambu” na faɗa a raina

Word ɗin clumsy data fada ya bani haushi, bata ganin ya mareni ne? Kuma shine zata bini da zagi “toh saime idan na watsa mashi drink? Yafi karfi ne” Na fada ina turo baki tareda juya idanu duk salon marasa kunya.

“kefa na lura karaman mara kunya ne, kuma samarinki masu fruits basa nan balle su tare maki” ya faɗa sai kuma ya cigaba da sababi “kisan me zaki rinka faɗa kafin ki yaba ma aya zakinta”

Wasu yara suna guje guje sai suka tureni na sake watsa mashi, tasssssss ya sake dauke nida mari saida naja baya. “Dama bakisan ina raga maki bane saboda ke sa’ar k’anwata ce, amma bari na koya maki darasi”

“Daga yau kin gama rashin kunya, ko a mafarki kikaga wasu zasuyi zaki kwaɓe su”

Idanun kowa a kanmu, kafin kace ‘Jack Robinson’ Kowa ya dauki wayar shi anata video. Anata posting a snapchat da Instagram, dama Mallam Bahaushe yace idan ba’a yi faɗa a biki ba baya armashi. Koba komai an samu abin tseguntawa.

Ja da baya na rinka yi hannu na biyu a kunci na, Shi kuma Naufal ya dauki alwashin sai ya shiga jikinta da duka sosai saboda saita yaba ma aya zakin tareda bambance zare da abawa. Abinda yafi bashi haushi ko Ango bai gani ba balle kawai ace ya juya gida.

Damkarta yayi ya k’ara watsa mata mari, “Idan ka kasheta sai ka bani gawarta na mayar ma iyayenta” Abba ya faɗa ranshi a bace.

Sai a locacin ya tuna dasu Abba, sakinta yayi ta faɗi kasa wanwar tana kuka. Hall anata kallonsa ana tsegumi, Sadeeq ya sauko daga high table rai a bace.

Kallon up and down yayi ma Naufal sai yayi nuni ma Amaryarsa da hannu alamar tazo su tafi. Ko k’ara kallon Naufal baiyi ba suke wuce.

Abba hannunshi harɗe akan kirjinsa ya k’ura ma Naufal ido, wannan ɗebo ruwa dame yayi kama. shikuma yana kallon k’asa cikin nadama.

Baban Sadeeq yaketa kallon Fadeela, ajiyar zuciya yayi kafin yace, “Naufal ka ɗebo ruwan dafa kanka saboda if I’m not mistaking wannan yarinyar Grand Kadi ce na Bauchi”

Jikin Engr Hussain yayi la’asar “Dan Kuka mai jawo ma uwarsa jifa” ya ayyana a ransa.

Bashi ba har Naufal cikinsa yanata kaɗawa saboda kowa yasan cewa ba’a taɓa yaran manyan mutane a zauna lafiya, uwa uba yarinyar Grand Kadi gaba ɗaya. Yanzu yanzu within minutes zasu iya mayar da life dinka miserable.

#NiDaDiyata

*Xeemee you are appreciated, Allah ya bar zumunci*

*All rights reserved*

💥∂ιмρℓεs💥
[8/2 13:23] 💕Ummieekhaleel 💕: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

💦 Ni Da Diyata 💦

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples

💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦

✨✨✨Page 7 ✨✨✨

Abdullah It was narrated that 'Abdullah said: "The Messenger of Allah said to us: 'O young men, whoever among you can afford it, let him get married, for it is more effective in lowering the gaze and guarding chastity, and whoever cannot then he should fast, for it will be a restraint (wija') for him.'"

********************

Sheshek’ar kukanta da sukaji ya dawo dasu hayacinsu, Abba ne ya matsa dab da ita ya fara magana kasa kasa, “kiyi hakuri diyata, insha Allah sai anbin miki hakkinki, nine mahaifinsa”

A hankali na daga ido na kalle dattijon dake magana, kammanninsu ɗaya babu bambanci. Bance komai ba illa rage sautin kukana ina Jan magina a hankali.

Alhaji Sulaiman (mahaifin Sadeeq) wanda yayi shiru kamar wanda ruwa yaci, a sanyaye yaje wajen tubur dinsu inda suka bar Alhaji Musa, shi dama baisan abinda ya faru ba sanadiyar yana waje yana waya.

“Ranka ya daɗe dama wani ɗan matsala ta taso” shikuma Alhaji Musa yace, “Injin dai lafiya?” tare suka koma inda su Naufal suke. Gaban Egnr faɗuwa yayi daya lura da Fuskarshi yayi kama dana Fadeela. Nan kowa yayi tsuru tsuru ana inda inda.

A gurguje mahaifin Sadeeq yayi mashi bayanin abinda ya faru, shiru yayi kafin yace, “Yarinya tashi ki faɗa sunan ki dana gidan ku?” ita kuma Fadeela tana daga ido ta ganshi saita barke da sabon kuka kai zaka zata locacin ake marinta.

“Big Daddy kasheni yakeso yayi wallahi” ta faɗa cikin sigar kuka.

“yi min shiru please, ni shiririta ne bana so” ya fada mata. Tsit tayi bata kara cewa komai ba,

“Ai abin yazo da sauki tunda na gida ne kuma ba matsala sai mu tafi gidan Grand Kadi, though ni banga abin tashin hankali anan ba, tayi rashin kunya kuma ya hukunta ta”

“ Ah ah gwara aje ayi abu cikin mutunci”, shi Abba abinda yasa ya nace su tafi a warware komai baifi akan iyayen Fadeela ba bcs yanzu sai a hana mutum sakat. Yanzu yanzu yaji tace kasheta akeso ayi.

Fadeela ta shiga motar Daddy babba(Alhaji Musa) shi kuma Abba da baban sadeeq suna mota daya, sai Naufal dake baya yana bin su. Yana tafe zuciyar shi yana mashi k’una, wai fisabilillah gidan Bad Luck zaije ya bada hakuri, tun dayake bai taba jiba.

Daddy babba yana tuk’i murna fal a zuciyarshi, shi kaɗai yasan dalilin haka. Sun isa gidansu Fadeela wanda ke GRA, katon gidan wanda komai akwai. Daga su Garden, swimming pool da kuma karamin basket ball court wanda yake da double function as tennis saboda Grand Kadi yana san motsa jiki.

Daga Naufal, baban Sadeeq da kuma Abba saida suka jinjina tsarin gidan, sum sum suka bi bayan Alhaji Sani. Ita kuma Fadeela tun kafin mai gadi ya buɗe kofa ta fito daga cikin mota tabi k’aramin gate ta shiga “Ho sarkin shagwaba” Daddy babba ya faɗa.

Bata iske kowa a falo ba sai motsi dataji a kitchen, da sauri ta haye upstairs kafin a risketa a fara mata tambaya. Su kuma su Naufal da Abbanshi sannu a hankali suka rinka bin Daddy babba har cikin Main parlour. Suna isa ciki sunyi Sallama sau wajen uku saiga Mommy ta fito tana gyara zaman gyalenta tareda amsawa.

“Abbansu Fadeela Kaine tafe?” ta fada fuskanta dauke da fara’a. Shi kuma ya murmusa sai yace, “Eh nine Hajia, kuma tafe da manyan baki nake” sai a lokacin ta mayar da hankalinta wajen su Naufal, fuskanta a sake tace masu sannu da zuwa. Wucewa tayi kitchen ta jero abinci akan tray saita kawo masu suci. “Bismillah mana” Daddy babba ya faɗa, su kuma Naufal mutuwar zaune sukayi saboda sun tuna idan mutum zai cuce ka saiya bari kun sake kafin ya ɗana maka tarko.

Upstairs mommy ta wuce domin ta kira Daddy, basuyi minti 5 ba sai gashi sun dawo tare. Zama yayi akayi gaisuwan mutunci, shi dai Daddy babba baice komai ba, gabzan abinci ya rinka yi yana santi tareda jinjina ma girkin mommy tunda ta iya sosai a matsayin ta na professional Chef. Daga bisani yace, “Ai tare muke da Diyata” Grand Kadi(Alkalin Alkalai) ne yace, “wanne daga ciki?”

“Auta nake nufi, sarkin shagwaba” yana kaiwa nan ya fara dariya. “Ban masan ta dawo daga bikin ba” Mommy ta fada. Shi dai Big Daddy saida ya cika Gizzard dinshi kafin yayi gyaran murya, gaban Naufal ne yayi mummuna faduwa. Dama tun yau abinda yake samu kenan but na yanzu ya ninka sau dubu.

Gyara babban rigarsa yayi, falo yayi tsit kowa naso yaji mai zai faɗa, “Da Alheri nazo” murmushi yayi wanda shi kadai yasan ma’ana shi, kowa kawai kallonsa yakeyi. Naufal duk ya k’agu yaji mai zai faɗa, “Dama batun auren ɗiyata ne da mijinta gashi kuna kallon shi” ba su Daddy ba har Abban Naufal saida suka mayar da idonsu kanshi.

Shi kuma zare ido yayi yana nuna kansa da ɗan yatsa, da kyar ya iya bude baki yace, “Da ni kuma?” kwarai da gaske, kai muke nufi Alhaji Sulaiman ya chapke. Shi dai Alhaji Hussain baice komai ba, ya bar ma Allah komai. Idan auren zai zame mashi rufin asiri ba’a tozarta shiba to gwara ayi.

“Yanzu dama akwai wanda aka ajiye ma Fadeela ta aura amma shine ba’a sanar dani ba? Kun kyauta min kenan? NI DA DIYATA amma sai ayi abu ba’a shawarce niba. Idanun Mommy fal da hawaye take magana cikin k’aramin murya.

Grand Kadi zaiyi magana sai Big Daddy yace, “bazan canza magana taba, dole ayi bikin nan. Badun ina san Fadeela ba da nasa ayi bikin nanda 6 weeks but zan k’ara mata wani 6 weeks din kunga ya kasance 3 months kenan sai ayi proper gaisuwan iyaye da kuma biyan sadaki”

Shi dai Naufal tunda yake bai taba ganin something that is absurd ba Kamar yau, “ya mare yarinya, maimakon a hukunta shi sai aka bashi ita a matsayin mata. Bai taba ganin inda aka ɓare gyaɗa aka tsinci mota ba.

Daga alamu sun gaji da annoban data ke jawo masu ne shi ne ake so a mak’ala mashi, amma bazai yiwu asha fate ranar sallah ba” Ranshi a bace ya ɗaga green eyes dinshi wanda idan ranshi ya baci yana glimmering, zaiyi magana sai ga Fadeela ta fito tana kuka.
Chapter 5 · 0% Book details