← Book details Nida Diyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 48

Sashe 30

Nida Diyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Manna mata kiss yayi sai yace, “Toh gani me kika ajiye min”

“Muje kayi wanka sai kazo kaci abinci, yau favorite dinka na girka”

Daga kanshi yayi sannan ya soma magana kasa kasa, “Afuwan babyna Wallahi Aminu ya isheni da yana jin yunwa shi ne na kaishi daga nan saina ci”

Shiru tayi batace komai saboda ta bala’in shaka, gashi har konewa tayi wajen wrapping tuwon. Idanta Saida ya canza kala saboda bacin rai, ba wannan karon bane take abinci yaki ci, yayi yafi a girga amma na yau ya ɓakanta mata rai.

“other half Ko drink ɗin bazaka shaba” ta faɗa cikin muryan kuka.

Shafa bayanta yayi saiya ce, “Ki ajiye min a fridge gobe sai na sha”
“Allah ya kaimu lafiya”
“Amin babyna”

Sun tafi ɗaki har yayi wanka tana goge jikinsa da hand towel, “Other half yau Kaje wannan sabon plaza ɗin ne wanda ke kusa da Apple clinic?”

Datana kallon fuskarshi dataga rashin gaskiya karara ya bayyana. Dakewa yayi saiya amsa mata da, ‘Ah ah, menene ?”

“Babu komai kawai naga kamar motarka ne a wajen”

“NI dama yanzu zan faɗa maki a Gombe na wuni, Zaayi renovating Government house shine mukaje meeting” tabbas akwai zance kamar haka amma meeting ɗin saura sati biyu.

“Oh Allah sarki other half dina nayi maka murna sosai, Allah ya sanya alheri”

“Amin, amma  kema meya kaiki wajen? Inace kasuwa zaki amma shine kika biya wani wajen? A duniya karya yana cikin abinda na tsana Wallahi. Idan kika tambayeni ai bazan hanaki ba, amma dan nuna ban isa ba shi ne kikayi abinda kikaga dama koh?”

Nan take ta firgice yanda taga karamar magana ya zama babba, saukowa gabansa tayi ta rike masa hannu, “Other half Kayi hakuri dan Allah, ka mance na saba biyawa saloon idan zani kasuwa saboda banso nayi fita biyu”

“Toh donkin saba sai akace banajin haushi ko me? Ni dai Karki saki saboda bana san karya”

“In sha Allah Other half bazan kara ba” Daga nan ta hau gado tana shafa masa bayan shi tana watsa mashi kalamai masu dadi.

Dolenshi ya sauko ya biye mata suka fara soyayyar su, suna haka har barci ya kwashe su.

#NiDaDiyata

#TeamFadeela
#TeamNaufal
#TeamYasmeenah

I'm proudly Team Fadeela this time around.

*All Rights Reserved*

💥∂ιмρℓεs[9/2 15:52] Dimples: ©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

💦 Ni Da Diyata 💦

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples

💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦

✨✨✨Page 28 ✨✨✨

*Lesson*

Beware the liar. He lies so much that he forgets the truth. He even finds it hard to accept the truth & ends up believing in his own lies.
MUFTI ISMAIL MENK

Abu Ayub narrated that the Messenger of Allah said: "Whoever fasts Ramadan, then follows it with six from Shawwal, then that is (equal in reward) to fasting everyday." (Sahih)

***********

Washe gari..........

Tun sanda Fadeela ta tashi daga barci bata koma ba, kitchen ta wuce ta fara wanke wake saboda tana sha’awan cin kosai da kunun tsamiya.

Ta gama wankewa saita markaɗa à blender, shima ruwan zafin yana cikin Kettle amma yaki tausa. Wucewa tayi upstairs domin ta kira Naufal ya taimaketa ya duba mata.

Tana isa taji karar wayarsa amma kafin ta karasa ya tsinke,, kuma waya da password balle ta duba. Shikuma yana cikin bayi yana wanka.

Tana zaune a bakin gado tana jiransa saiga wayan ya sake shigowa, da hanzari ta dauka kuma cikin ikon Allah wanda takeso tayi magana dashi ya kira, watau Aminu office.

Ta kara a kunnenta kafin tayi magana sai taji muryan mace tana magana cikin yauki, “Mine tun dazu nake kiranka amma baka dauka ba”

Mamaki karara ya kama Deela saita cire wayar daga kunnenta ta sake kallo da kyau kuma tabbas Aminu ne.
Mayarwa tayi kunnenta sai taji, “Mine baka jina ne? Hello Naufal!” nan take gaban Fadeela ya faɗi sai tayi maza ta kashe wayar.

Jikinta ya soma bari, tabbas ba wrong number bane tunda ance ‘Naufal’ amma yaushe Aminu Office ya koma mace. Gashi harda kiran mijinta Mine.
Shiru tayi tana jiran shi ya fito daga bayi, yana fitowa sai yaganta zaune. Murmushi ya sakar mata kana yace, “Babyna yadai?”

    Fuskarta babu yabo babu fallasa ta soma magana, “Other half Aminu ya kiraka kuma na dauka amma naji muryan mace saina kashe. Probably wrong number ne”

“Probably” ya amsa saiya soma shafan mai. Dayake yanzu ya kware a iya shararo karya yasa baya girgiza idan yana yi. Tabbas yasan Yasmeenah ne kuma yayi warning ɗinta data daina kiransa idan yana gida amma bataji.

Kallon rainin arziki tayi masa sannan tayi kwafa, dama ta saba dauko masa kaya amma wannan Karon tayi kememe. A duniya rainin wayo yana cikin abinda ta tsana.

Ji yanda yayi pretending bayan harga Allah tasan ba wrong number bane. Ita abinda bata sani ba shi ne ko amsar wayan Aminu tayi ta kira Naufal kokuma itace Aminu ɗin da ake magana kullum.

Suna cikin haka sai wayarshi ya sake kara, toh dama yana hannunta, kallo ɗaya tayi saita lura da Aminu Office ke kira. Cilla mashi wayar tayi kamar zai faɗi sannan tace, “Gashi ya sake kiranka”

Kallo ɗaya shima yayi saiya yastina fuska kana yace, “bazan dauka ba tunda yanzu zani office”

Ita tasan yanada aboki Aminu amma kawai yanzu komai ya chunkuse mata ne. Kawar da tunanin tayi yanzu kafin zuciyar ta ya buga. Ya lura tayi shiru saiya je gabanta ya ɗuka tareda kama mata hannu.

“Babyna meke damunki? Murmushi tayi wanda bai kai ciki ba sannan tace, “Kaina ke ciwo” shafa mata goshi yayi tareda kumatu “Allah sarki babyna, ko na zauna ne nayi jinya”

“Na hutarshe ka” saita mike tayi hanyar kofa harta kusan ficewa saita tsaya tace “Bari naje kitchen”

Saboda bacin rai bata fada mashi kettle ya baci ba, kawai zataje ta daura akan gas. Shikuma dama gaste yake mata saboda koda tace ya zauna awa daya zai kara yace mata ana nemashi maza maza a office.

Dama yau zai raka Yasmeenah Kano karban dinki wajen wani tailor ɗinta. Ita kuma Fadeela tana aiki a kitchen duk ranta yana mata zafi, bata ma lurada suyan data keyi dukta kona.

Haka sukaci ita kokon kawai ta tsakura. Daya lura da yanayinta saida ya tambaye ta matsalarta saita ce masa kanne. Shi kwata kwata baiyi tsammanin ta ɗago sa bane saboda yasanta da nawa a al’amura ta, kafin ta ɗago locacin kila ta haihu kuma dama abinda yake jira kenan.

Harda cewa ta dauko mayafi ya ajiye ta a asibiti amma taki, ce masa tayi idan ta kwanta zataji daidai. Harya kai kofa bata tashi domin ta rakashi ba, juyowa yayi saiya fara magana, “Baby tunda bakida lafiya ba sai kinyi girki dani ba”

“Zaku fita Kuci da Aminu koh?” tayi charab ta tari numfashin sa. Murmushi yayi yana sosa k’eya saiya ce “Eh baby zamu koma Gombe kuma”

“Allah ya dawo daku lafiya” ta faɗa tana mashi kallon tuhuma. Dama ance kukan kurciya jawabi ne kuma sai mai hankali ke ganewa, amma sam bai saka a ranshi ta gane komai ba.

Inshut yau ya kara jindadin yanda yayi mata karya dazu kuma bai girgiza ba, kanne ido ɗaya yayi saiya furta a fili “Kai Naufal bakada dama”

yana tafe hanyar gidansu Yasmeenah yana Nishaɗi tareda sauraron wakar Young Alhaji na Nomis G.

Ita kuma Deela kifa kanta tayi a kan dinning tayi kuka san ranta, wai yaushe yaushe da shiryawa da shi harta  gundureshi ya soma kallon wata.

Upstairs ta wuce dakinta domin ta dauki wayarta, kawarta da suka tashi tare Jumaimah ta kira a waya akan tazo gidanta yanzu yanzu. Within hour ɗaya ta iso. A falo ta riske Deela ido yayi sutu sutu ya kumbura.

Bata iya karasa sallama ba ta wulla jakarta kasa tareda rugawa wajen Deela. Rungumota tayi saita soma magana da sauri sauri “Deela meya faru? Dukanki yayi?”

Rushewa da kuka Deela tayi dama abin nema ya samo wai matar falke ta haifi jaki. Jijigata Jumy tayi saida taga ta rage kuka sannan ta kuma tambayarta “Deela my dear kin ruda ni, kiyi wa Allah ki faɗa min saboda hankalina ya huta”

Cikin muryan kuka ta soma magana gwanin ban tausayi, “Tunda nake ba’a taɓa min rainin hankalin da Yaya Naufal yake minba” Daga nan tana kuka ta fayyace mata komai da komai duk abinda Naufal yakeyi wanda duk bata lura ba sai yanzu.

“ni nama rasa me zance Wallahi” Jumy ta faɗa tana jinjina ma kokarin Fadeela. Daga nan saita ce, “Toh yanzu me zakiyi? Zaki tambayesa ne ko me?”

“In tambayesa? Wallahi karya zai shirgo min. Aini tun karyan dayayi min dazu  na firgita dashi”

“Okay ki bani nanda awa biyu Deela, zan nemo maki waye asalin Aminu. Office ɗin su zani nayi masu hadarin kudi dole su faɗa min wake zuwa wajen mijinki”

Murmushi Deela tayi saboda taji daɗin shawarar. A kwance Jumaimah ta bar Deela kana ta wuce bank ta ciro dubu hamsin. Kai tsaye office ɗin Naufal ta wuce.

Masu gadi suka tareta suna mata magana akan inda zata da sauransu. Murmushi tayi saita yi parking motarta daga gefe saboda hanya ne.

Sannu a hankali ta fito daga cikin motarta taje inda suke, murmushi ta sakar masu kana ta gaishe su. “Da alheri nazo wajen nan bayin Allah” saita zuge jakarta ta kyallara masu kuɗi su gani.

Dama su biyar ne, hudu suka soma washe baki daya kuma fuskarshi babu yabo babu fallasa.

“Dama tambaya nakeyi”

“yarinya Allah ya sa mun sani”

“Kunsan Arc Naufal Hussain”

Noke noke suka farayi basaso suyi magana, data lura da yanayin su sai tayi murmushi kana ta kara matsawa kusa dasu, “Kar kuji tsorona, niba muguwa bace kawai wasu abu ke faruwa a office ɗinnan shine nake so na sani”

“eh mun sanshi, lafiya koh?”

“Bansani ba ko akwai wata wanda ke yawan zuwa wajen shi ?”

“kice mai shigar arna” Daya daga cikin su ya chapke. Daga nan suka soma magana akanta, kowa na faɗin magana marasa daɗin ji akanta.

Jumy taji dadi sosai koba komai Fadeela ta kace mata tsara tunda ita  ba mutumiyar arziki bane.
Chapter 30 · 0% Book details