← Book details Nida Diyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 48

Sashe 31

Nida Diyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Toh kun san sunanta ko wani abu game da ita” ta tambaya. Wani daga cikin su yaje ya dauki wani takarda daya kunsa sunarta da address dinta.
Acewarsa tazo cikin motarta shine zasu fita a motar Oga sai aka bashi address ya mayar mata nata. Jumy taji dadi sosai saita dauki dubu talatin ta basu zasu raba akan dubu shida shida.

Dama aikin dubu ashirin ne a wata toh gashi sun sami kwantan shi, nan suka rinka godiya suna shi mata da albarka. Dadin zance suka faɗa mata yau Naufal baizo aiki ba jiya ma tun goma daya fita bai koma ba.

Tana zuwa ta fayyace ma Deela komai daya faru, kuma tace mata tanada wani uzuri a gabanta amma gobe bayan Naufal ya fita sai tazo suje suci kaniyar karuwarsa.

Deela taji dadi sosai kuma tayi Na’am da shawarar. Batayi girki ba saboda tasan bazai ciba, sauran kokon ta take ta sha sai wajen yamma tayi Indomie da sardine.

Wajen yamma su Naufal ana Kano Anje shoprite da Yasmeenah ana kallon wani sabon American film ‘XXX return of xender cage’ anayi ana shan ice cream da popcorn.

Dama tun safe suka karba ɗinkin kawai ana holewa ne. Siyayya ba kadan ba tayi saida kuɗi sukace Allah ya isa kudaina kasheni haka.

Waya akayi ma Naufal wai an kawo motar Deela daga Cotonou, dayake baya garin sai yace kawai a kaimata dukda birthday ɗin shigarta 21 saura kwana uku.

Shi a dole yayi abin arziki ya bata early birthday present, da farko har zata mayar masa da abinshi amma saita tuna raba mugu da makami ibada ne.

Shikuma sai kallon waya yakeyi yana jiran yaga ta kirashi ta fara kwarara mashi addu’a amma sai yaga wayam. Haka ya hakura da tunanin kira sai ya mayar kila batada kati ne, yanzu yana kyautata zaton ta saka English wear mai rikitarwa tareda saka turaren wuta tana jiran sa.

As expected wajen goman dare ya koma gida, Deela tana jin karar motarsa ta kashe wutan ɗakinta tareda kwanciya abinta. Yana shigowa bai ganta ba sai tausayinta ya kamashi sosai saboda yasan ciwon ne ya sakata a gaba.

Yana zuwa ɗakinta yaga harta kwanta, zuwa yayi yana shafa fuskantar amma ta rinka mashi magagin karya. Dole yaje ɗakinsa ya barta, basuyi wani Chatting sosai da Yasmeenah ba saboda ya gaji sosai gashi kuma ranshi baya mashi daɗi Deela babu lafiya.

Washe gari.....

Dankali da kwai ta soya mashi, dukda yana hanata akan batada lafiya amma taki ji. Ita kawai badan shi takeyi ba sai dan Allah.

Batayi mashi maganar motar ba shine ya gaji da shirun ya tambaya. “Eh dama naga an kawo mota amma bansan na menene ba?”

Kanne mata ido yayi yana dariya,”Babyna zatayi birthday dole na fito da ita”

“Ai ashe zaka tuna?”

“Meyasa bazan tuna ba?”

“Naga yanda kuke fita sosai aiki da Aminu ne yasa banyi tsamanin zaka tuna ba?”

Shiru yayi ya cigaba da shan Coffee ɗinsa saboda kamar magana ta gaya mashi. Har mota ta raka shi daganan ta sake kallon nata.

Venza ce 2016 model kuma kana gani kasan tasha kuɗi. Wajen 10am Jumy tazo tana zuwa sai taga mota a parking lot. Cikin mamaki ta tambaya Deela kona waye shine tace ai shiya turo jiya.

“Dauko mayafinki mu shiga ciki muje muci ubanta” dama Deela ta iya tuki saboda takan tuka motar Mommy.

A hanya suka dauke Mansura aka wuce da ita, suna isa kofar gidansu Yasmeenah sai suka tsaya a bakin gate wai ayi masu iso da ita. Daya tambayesu sunar su sai Jumy tace ace mata Naufal ne.

Yasmeenah tana zaune tana kallon wani tsohon Comedy The big bang Theory Sai akace Wai Naufal yana jiranta. Dayake bata expecting ɗinsa sai bayan la’asar saboda yanada aiki sosai.

Daga ita sai leggings da t-shirt kai babu kallabi ta ruga a waje saboda dama tana missing ɗinshi. Tana fita gate bata ganshi ba sai wasu mata uku. Tambayar maigadi tayi sai yace ai sune suke nemanta.

Tana karasawa tareda magana, “Bayin Allah daga ina haka..?” bata karasa ba Fadeela ta dauketa da mari, zatayi magana saita sake kai mata wani.

Hannunta biyu a kunci tana mamakin meya faru da ita, sai a locacin suka kalle juna kuma sun gane cewa sun haɗu a saloon.

“me na maki da zaki mareni?” Ta tambaya.

“ni bazan ce ki daina kula mijina ba, kawai nazo nayi maki bushara ne bcs kin kawo kanki gidan wahala. Saina nuna maki iskanci ba karuwai irinki kawai suka iya ba.”

Anan Yasmeenah ta hasala, “Dama akan Naufal kika mareni shine na tsaya kallonki, wallahi zaki san wa kika mara?” Saita nufa Deela. Jumy ce ta mauje mata baki da jakarta.

Nan take jini ya barke, kukan kura ta sakeyi saita koma kuma anan Mansura ta samu nata rabon tareda wanka mata mari. Da gudu maigadi ya shiga tsakani tareda korar su Deela.

Sun tafi murna fal Ransu koba komai sun girgizata, sun koma gidan Deela a inda Jumy da Mansura sukayi mata sallama suka tafi.

Ita kuma Yasmeenah kiran Naufal tayi a waya tana masa kuka akan matarsa tazo da gayya sun fasa mata baki. Yayi mamakin yanda ta sani amma wannan bashi ke gabansa ba.

Zuwa yayi gida ko shiga da motarsa baiyi ba kawai yayi parking a waje saiya shiga ciki, motsi yaji a kitchen da alamu tana ciki.

Zuwa yayi wajen baiyi wata wata ba saiya haska mata mari, “Wayece ki dake matar da zan aura?” yana huci kamar mayunwacin zaki.

Hannunta akan kumatu tana hawaye, cikin muryan kuka ta soma magana “Nika mara? Wallahi ka mari aurenka”

#NiDaDiyata

*All Rights Reserved*

💥∂ιмρℓεs💥
[10/2 18:21] Dimples: ©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

💦 Ni Da Diyata 💦

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples

💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦

✨✨✨Page 29 ✨✨✨

*Lesson*
"FASBIR SABRAN JAMILAH". Patience is one of d most beautiful attributes one can ever have, It makes one listen, understand, forgive, forget, endure and move on in life. May Almighty Allah in His Infinite Mercy and wisdom uphold our faith in Him and may HE grant us d best of this world & d best of hereafter. Ameen

********

Sai a lokacin hankalinsa ya dawo jikinsa, jikinsa yayi la’asar sosai. Dama yasan saurin hannunsa wata rana zai kaishi ya baro, daɗin abin Fadeela tanada hakuri kuma yasan zata yafe masa.

Magana ta cigaba cikin kuka, “Duk Meka min à duniya bazanga laifin ka ba! Don ka ganni cikin gidanka ne” saita kashe gas dama ta daura ruwan miya ne.

Zuwa tayi zata rastashi ta wuce, sai yayi kokarin kama hannunta. Da sauri ta kwace tareda nuna masa yatsa tana hawaye, “This is the last time da zaka mareni” sai tayi hanyar upstairs abinta.

Shikuma yasan ya tabo ta saboda bai taɓa ganin tayi haka, koda yaci zalinta bata nunawa, burinta bai wuce ta kyautata masa ba. Haushin kansa yayi saboda ya bar shedan yayi tasiri a rayuwarsa.

Barin gidan yayi saboda ya bata dama ta sauko, idan yaso anjima zai bata hakuri yadda zasu fahimce juna.

Wayarsa yayita kara kuma Yasmeenah take kiransa.
Kashe wayarsa yayi gabaki daya saboda yasanta da raki, yanzu hankalinsa baya jikinsa gwara yayi dealing da mace ɗaya tukun idan yaso gobe zaije wajenta.

Deela tana hawa upstairs ta dauko wani zungureriyan akwati tareda buɗe drawer ɗinta. Zuba kaya kawai takeyi tareda tunanin zuci. Saida ta gama saita fara tunanin inda zata.

Tasan cewa Mommy bazata barta ba sai kawai ta yanke shawaran zuwa gidan gona. Nan take ta ɗebo takalma da duk wani abinda zatayi amfani.

Rufe gidan tayi saita bama Maigadi key idan Naufal ya dawo saiya bashi. Cikin sabon motarta ta shiga saboda bazata bar masa ba.

Tana isa gidan gona taga Miemie a garden chairs da Khattab, su da farko basu ganeta ba saida ta sauko tayi hanyar boot tukun.

Da hanzari suka tashi domin su taimake ta, “Anty kin dawo nan da zama ne?”

“Eh Miemie”

“Ke kuma babu gaisuwa babu komai kin rufeta da tambaya” inji Khattab.

Daga nan suka wuce cikin gida.
Sun isa cikin falon sai aka gaisa yadda ya dace, locacin Anty Saudah tana daki sai Miemie taje ta kirata.

Bayan tazo an gaisa, sai kuma Khattab ya tashi wai shi zai tafi kuma Miemie tazo ta rakashi. Daga nan Anty Saudah ta soma mata kallon tuhuma. Kallon kasa ta somayi kana tace, “Aiki yayi mashi yawa sai goman dare yake dawowa tun safe, kuma ganida ciki. Yasa nace bari na dawo nan har na haihu”

Shiru Anty Saudah tayi saboda tasan bashi bane kaɗai dalilin, sai dai kawai taji daɗin yanda bata koma gidansu ba ko wajen Mama da abin ya tabarbare.

Mai aikinta ta kira taje ta gyara mata wani daki tareda canza zanin gado. Fadeela taji daɗi sosai yadda Anty batayi mata binkice ba dukda tasan karyan takeyi.

Bayan an gama gyaran ɗakin saita wuce domin ta huta, daɗi taji sosai saboda yanzu bata da wani aiki sai bin gado ko hira. Sam bata kewar Naufal asalima haushin sa takeji.

Wayarta ta dauka ta kira Mommy da Jawahir sai ta faɗa masu Exactly abinda ta faɗa ma Anty. Mommy tayi faɗa sosai akan dalilin da bata dawo da rainon gidanta, ita dai bata hakuri tayi.

Tasan yadda Mommy ke san Naufal, yana zuwa sau ɗaya zata ce ta bishi.

8:30 pm....

Biyawa yayi Vanilla joints tareda Oasis ya siyo kaya shak’e da leda, yana isa gida yayita bugawa amma ba’a amsa ba.

Komawa yayi wajen mai gadi ya tambayesa koba mutum ne. Anan ne ya mika masa key wai an bashi dazu ya mance bai bashi ba.

Shiru yayi ya rasa me yayi zafi da ta tafi gida amma ya dauki alwashin Ko’ina taje saiya dawo da ita. Haka ya shiga cikin gidan gwiwa babu kwari.

Washe gari Fadeela bata tashiba sai wajen 9am saboda ta kara barci bayan tayi sallah. Tana fitowa su Anty na kan dinning suna karin kumallo saita zauna itama tareda dasu.

Ana cikin haka saiga Naufal ya shigo, kallo ɗaya tayi masa ta watsar saita bar dinning ɗin gaba ɗaya. Shikuma yazo ya dauki Anty Saudah aje bikon Fadeela sai yaga motar Fadeela a parking lot.
Chapter 31 · 0% Book details