← Book details Nida Diyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 48

Sashe 35

Nida Diyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*********
Kwance tashi an kai satin haihuwar Deela, kullum cikin tambayarta akeyi ko tana jin wani ciwo amma sai tace masu ah ah.

Ita kuma sam bata jin komai saidai kafarta daya daɗe da kumbura, sau ɗaya bayanta yayi mata ciwo kuma cikin darene kafin safe ya daina yasa bata faɗi ba.

Dayake kitchen ɗin Anty akwai kananan kwari da kyankyasai, sai Deela ta saka maganin kashe su daga nan ta fita da duk wani kayan kitchen da Anty ta mallaka zata wanke.

Babu yanda Mai aikin Anty da ita kanta Anty ɗin basu hanata ba amma ta kafe, acewarta ai akan kujera zata zauna kuma hannunta suna aiki sosai.
Da taimakon Miemie sukayi tas tareda mopping kitchen komai yayi charasras. Bayan  nan sai Deela ta haɗa masu dambun tsaki wanda yasha alayyahu, yakuwa, gyada, kashi, nama da sauran su.

Kowa yaji daɗin abin saboda a babban paranti aka zuba masu, Abba da Naufal aka zuba masu tare tun dayake ya zo kawo masu katin daurin aurene saiya taras an gama, shine yace bari yaci mai dadi kafin ya tafi.

Su kuma su Anty da Deela tareda Miemie a round tray Babba suka saka nasu, sannan ga kakiɗi a gefe suna aunawa ciki.

Bayan kowa yayi nat ya nare, Naufal ya tafi itama Deela ta kwanta. Wajen sha ɗayan dare sai bayanta ya rike yana mata wani irin zafi.

Zufa ya rinka yankomata ta ko’ina, dolenta ta sauko daga kan gado tana addu’a tareda safa da marwa cikin tsakar ɗaki tareda bankare baya.

Zafi sai karuwa yakeyi wata sa’in kamar ana tsikarinta. Saidai kawai ta tafa hannunta tareda rankamo salati tanayi tana sukurkurta gashin kanta.
Hawaye takeyi tana kokarin matse bakinta saboda bataso ta tashi kowa, wajen ɗaya da rabi sai ruwa ya fara fitowa ta kasanta.

Aikuwa duk wani dauriya datake yi ta daina, kwala ma Anty Saudah kira tayi. Dayake ɗakin Miemie yafi kusa so ita ta riga zuwa.

Abinka da tiles koina santsi yake gashi ɗakin sharkap. Nan take Anty ta haɗo mata kayan haihuwa kamar su zannuwa, auduga, detol, glucose, kayan jariri, pampers, feeding bottle etc.

Ita kuma Miemie tana daga gefenta ta riketa tana kuka, Abba yanada bakin kofa ya haɗe hannu a kirji yana tausayinta. Sai ya tuna da Naufal, zuwa yayi ya dauko wayarsa domin ya kirasa amma yaji switch off.

Ranshi yayi matukar baci amma babu yanda zaiyi, shikuma Naufal daya kaima Yasmeenah katin aure sai Aminu ya kirashi, karban wayar tayi ta kashe.

Acewarta idan suna tare dole yayi respecting ɗinta ya kashe wayarsa, toh tun daga lokacin bai tuna ya kunna ba.

Abba ya tuka motar da aka kai Deela wanda a locacin kuka kawai takeyi, Anty Saudah na yin mata sannu ita kuma Miemie na tayata da kuka tareda fiffita.

Nurses sun karbeta an wuce da ita maternity ward, saidai ba yanzu zata haihu ba zata iya kai 7 ko 8 na safe. Abba bai kira kowa ba yana jiran asuba tayi tukun.

Anty Saudah alwala ta dauro tayi sallah tareda neman mata easy delivery, ita kuma Miemie addu’o’i kawai take to fah mata.

Cikin awa kadan ta canza kaminta sai fizge fizge takeyi tana jefa hannu gashi kuma bayanta kamar zai balle.

4:53am.....

Har locacin bata haihu ba illa bakin azabar data kesha, ta kama bakin gado da jikin Miemie harta gaji. Gabaki daya babu wanda ya runsta a cikinsu. Kowa tausayinta yakeyi ga uwa uba mijinta baya wajen.

Bayan sunyi sallah sai Abba ya kira su Grand Kadi ya sanar dasu halin da ake ciki. Cikin minti talatin suka garzayo tunda safe ne babu hold-up.

Mommy na ganin halinda Deela take ciki ta fashe da kuka, Daddy ne ya kwaɓeta akan Fadeela tafi bukatar adduarta akan kukanta. Nan ta shiga mata sannu tana hadawa addu’a.

Har wajen bakwai saura wayar Naufal baya shiga, Abba ne da kansa ya tafi gidansa yaji ko lafia. Kwance  ya riske Naufal a falo yana sharara barci.

Daga alamu tun daya dawo daga masallaci yakeyi. Zungurinsa yayi saiya soma masa magana , “Kai haka zaka bar gidan kayi ta barci sai an shigo anyi maku sata”

Naufal a firgice ya tashi dayaji muryan Abbanshi da safe haka cikin gidansa. Waige-waige ya somayi yana kokarin tantance ko mafarki yakeyi.
Murje idonsa yayi saiya ga Abbanshi da gaske ke kallonsa, “Dama matarka muka kai asibiti wajen ɗayan dare, amma dayake ka kashi wayarka bazaka sani ba” Abba yana faɗi ya nufa hanyar kofa.

A fusace ya figi mukullin motarsa wanda ke kan centre table yabi sahun Abba. Three quater baki ke jikinsa da riga mai guntun hannu amma bai dameshi ba.

Haka ya soma tuki yana tunanin irin pain ɗin datake ciki. Yana isa gaban asibiti yaga su Anty Saudah da Miemie anyi charko charko ana kuka.

#NiDaDiyata

*All Rights Reserved*

#YarinyaMaiDimples
[15/2 22:30] DIMPLES: ©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

💦 Ni Da Diyata 💦

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples

💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦

✨✨✨Page 32 ✨✨✨

It was narrated from Hakim bin Muawiyah, from his father, that a man asked the Prophet(): "What are the right of the woman over her husband?" He said: "That he should feed her as he feeds himself and clothe her as he clothes himself; he should not strike her on the face nor disfigure her, and he should not abandon her except in the house (as a form of discipline)." (Hassan)

************

Karasawa yayi da gudu tareda damkar Miemie yana tambayarta koh lafia. Cikin kuka ta faɗa mashi cewa Fadeela tana cikin labour gadan gadan yanzu.

Anan fa hankalin sa yadan kwanta saboda duk zatonsa mutuwa tayi. Sakin Miemie yayi saiya karasa cikin asibiti, kukan Deela yaji tun kafin ya karasa wajen.

Nurse Anisa take karban haihuwar, middle age woman mai akalla shekaru 35 a duniya. Shekarun ta wajen goma da aure amma bata taɓa koda ɓatan wata ba.

Yasa idan aka kawo mai naguda take jagora tayi, cikin ikon Allah idan tana wajen akan samu Successful delivery.
Da karfin tsiya ya tura kofan har saida ya buɗe, nurses ne suka zo da sauri akan ya fita amma ya kafe babu inda zashi.

An kawo mashi sanitizer dasu hand gloves sai aka barshi a wajen, zuwa yayi da sauri kan gadon datake ya soma mata sannu.

Tausayinta ya kamashi sosai saboda bazai iya kwatanta irin ciwon dake ciba, rike mata hannu yayi yana mata addu’a.

Suna cikin haka tareda taimakon Doctor saita haifa baby girl ɗinta wajen 7:45am. Da sauri ya karba babyn ya runguma tun kafin a gogeta. Karin sallah ya soma yi mata tareda addu’a.

Ita kuma Deela tana daga kwance tana numfashi kadan kadan, an karba babyn akayi mata abinda ya dace sai aka bashi ya fita domin ya nuna masu.
Babyn kyakyawa fara sol kamar Deela saidai fuskarta sak irin na Naufal harda kalan idanun. Yana tafe inda su Mama suke fuskarshi zallan annuri yana walwala.

Mai aikin Mommy watau Anty Husna ta soma guda tana faɗin anyi mata kishiya. Kowa yaso ɗiyar kuma ɗaya bayan daya suketa dauka ana mata addu’a.

Koda aka bama Miemie tace su gama dauka saboda itace karshe, duk sun dauka daga ABBA da Grand Kadi kuma tasha addu’a daidai gwargwado.

Daga nan sai Miemie ta dauka ta fara kallon ta, har ranta take jin san yarinyar komai about her is so innocent and fresh.

Shima Naufal yanada ga gefe yana wasa da ita, baiji kunyar surikansa ko irin kunyar ɗiyar fari. Mama ce tace a kawo ta za’a bata glucose tasha.

Daga shi har Miemie basu so ba amma babu yanda za ayi. Ana cikin haka saiga Deela an fito da ita tana taka kafa da kyar, ji yake kamar yaje ya dauketa amma kawai ya barshi.

Kowa sannu yake mata har aka kaita ɗakin da zata huta kafin a sallame su. Anje an kwantar da ita tareda kara mata ruwa, su Doctor saida suka jinjina kokarin ta.

Tana kwance kowa yana cikin dakin, Anty Saudah ta haɗa mata ruwan shayi cikin Katon kofi wanda yasha madara.
Kamar madaci taji amma dole tasha, ita har locacin bata kalli meta haifa ba saboda kunyar iyaye. Tadai san kawai mace ne ɗiyarta, gashi babyn sai barci takeyi balle tayi kuka ta sake jin muryanta.

Tana kwance a haka barci mai dadi ya dauketa, bata farka ba sai wajen sha ɗaya lokacin ruwan da ake kara mata ya kare. A hankali ta buɗe idonta taga yan barka birjik cikin ɗakin saboda baima isa mutane ba.

Su Jawahir ana rike  da babyn lokacin, “Malama saiki tashi ki bata Nono tun dazu sai wani barci kikeyi kamar wanda tayi aikin wahala” ta faɗa tana dariya.

Sinna kanta kasa tayi batace mata komai ba saboda tana bala’in kunyar su Mama da Anty Saudah, “Woow Maman Baby” Jawahir tayi exclaiming saita koma gadon inda Deela take domin su gana.

Su kuma su Naufal  sunci Abinci sunyi nat saboda Bilqees da Abla sun kawo breakfast daya isa kowa. Doctor ta kira Naufal yayi signing takardun sallama.

Nurse Anisa tayi masu sallama kuma tace zata rinka zuwa duba su bcs little one tanada shiga rai sosai.

Ya basu kudi sosai fiye da bills ɗin haihuwa kuma an umarce Deela ta dawo nanda kwana biyu saboda aga lafiyan jikinta. Ita kuma Mai aikin Anty ta daura garwan ruwan zafi ana jiran Deela ta dawo tayi wanka.

Darbejiya masu kyau da kwari  aka tsinko kuma saida ruwan ya tausa sau uku kafin aka juye a wani katon baho. Hajia Rabi matar Big Daddy tayi mata wankar da kanta.

Tun Deela na ihu don azaba harta hakura ta daina. Nishi sama sama kawai takeyi, ita kuma Mama tayima baby wanka sau bakwai tareda gyarata tsaf ta saka mata kaya.

Deela na fitowa daga wanka Jawahir ta taimaka mata ta shirya tsaf cikin wani atampha kore dinkin a shape na riga da zani. Tayi ras abinta sai kamshi takeyi sabuwar mai jego.

Ta kowane bangare nuna mata kulawa akeyi, ko su samɗa da Jumaymah sun zo. Ita kuma Mansura bata samu daman zuwa ba saboda tana Abuja.

An gama abincin rana inda akan dafa tuwan semovita da miyan karkashi wanda aka barbaɗa yaji da kuma man shanu. Ga nama jaɓa jaɓa saboda kowane loma saika hada dashi.
Chapter 35 · 0% Book details