← Book details Nida Diyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 48

Sashe 43

Nida Diyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Am mani mutuwa amma bakiyi min gaisuwa ba, mutuwa fa ba abin wasa ne!”

“Toh ni ina ruwana dan budurwa ka ta mutu? Wallahi banki ba duk wanda ta ganka tace tana so ko cikin ranta ne toh ta gangara lahira” ta faɗa tana hura hanci.

Murmushi yayi mai bayyana bakin ciki, cikin gadara ya bata amsa. “toh saiki zauna gadin duniya idan kina tunanin bazaki mutu ba, kuma mutuwar nan yana kan kowa balle kice banda ke”

“chan ta matse maka” saita barshi wajen ta nufa cikin gida. Shikuma girgiza kai yayi yana murmushi, nan ya tuna da Miemie daya kirata a waya sunsha dariya. “Allahu Musta’an” ya furta a fili saiya nufa Masjid.

*****

Yasmeenah ta rinka hura ma Naufal wuta akan su tafi, ko sallar Magrib da kyar ta bari sukayi. Ita bama zata yiba saboda ana binta bashin azahar da la’asar kuma da kunya kaje gidan mutane kana jero salloli.

Yana dawowa ta mike wai a dole sai ta tafi, kamar kyamar gidansu takeyi taki sakin jikinta, bata lura cewa Deela bata haɗa komai dashi ba amma ta mayar da gidansu kamar nata.

Yaune ake sadakan bakwai amma Abba ya umarce shi akan yayi zamansa, da wata matar arziki ne da tun safe ta tilasta suje.

Haka sukayi sallama da yan gida suka tafi, tun bayan da akayi masu nasiha bai sake ganin Deela ba. Koda ya aika Bilqees ta kirata bata ko kalleta ba.

A Vanilla joints suka tsaya ya siyan masu shawarma, burger da milkshake. Daga nan ya tsaya a Chuchu Stores ya siya bread, milo, Madara, Indomie, sardines da sauran su.

Ita hakima ta hakince cikin mota tana duba Instagram, hotunan celebrities take kallo musamman ma maza tana jindadi hankali kwance. Ya dawo shake da kaya amma ko ta taimaka masa, asalima yi tayi kamar bata san yana jiran ta tayashi buɗe kujerar baya ba.

Haka ya ajiye kayan a kasa saiya buɗe da kansa kana ya sake dauka daya bayan daya ya rinka sakawa ciki. Bayan na saiya zaga ya shiga ya soma tuki. Ko irin ‘Sannu da kokari Maigida’ bata ce ba. Tuki ya soma yana tunainin ko ta daina sanshi ne kokuma kawai iya shege ne...

“Bazaki taimaka min bane kin ganni sai wahala nakeyi” tana yatsina fuska ta dauki ledar Shawarma da burger kawai tayi shegiwarta ciki.

Daki ta shiga ta ajiye, saita buɗe shawarma tana ci. Tanayi tana kallo ko bin kan Naufal batayi ba. Shima ya watsar da zancenta ya nufa Masjid domin yayi sallah isha.

Saida taci tayi nat kana ta wuce hanyar ɗakinta, a locacin tayi wanka tareda daura alwala.Jero train ɗin sallolinta ta soma yi. Ita bata kwana batayi sallah ba amma bata fiye sallah akan lokaci ba, duk dare zatayi abinta.

Wani pink nightgown mai laushin gaske gashida sansti ta saka. Saita saka palms din barci ta nufa hanyar ɗakinsa.

Shikuma ya dawo daga Masjid yaga falo duk burbushin abinci wanda taci ta bari, daukan nasa yayi ya tafi ɗakinsa. Baici ba saida ya kintsa.

Ya gama ci yana shan ruwa daga bedside fridge ɗinsa saita shigon tana masa murmushi, dakewa yayi amma bata damu ba.

Shagwaba ta soma masa, daya mata maganar behaviour ɗinta na ranar saita bashi hakuri wai kawai she is overwhelmed by everything ne. Ba laifi ya sauko daga fushin sa daga nan sukayi kwanta.

After six weeks...

Fadeela ta soma samun sauki sosai, har yanzu bata magana amma ta rage yawan kuka kamar yanda ta mayar ibada. Kuma tana ɗan murmushi koda sau ɗaya ne a rana.

Kullum cikin addu’a take a zuciyarta Allah ya bayyana mata ɗiyarta. Har tayi arba’in ta soma sallah da kanta tana rok’on fita daga cikin matsalan.

Naufal da kanshi ya dauko mata donkey, paints dasu sauran kayan masu painting. Taji daɗin abin sosai saboda yanzu batada wani sana’a sai shi.

Kowa yana murna yadda ta fara mayar ma Allah komai ta dauki dangana. Yakan zo dubata sau biyu, da safe idan zashi office sai kuma da yamma idan ya dawo kafin ya wuce gida.

Ta ɓangaren aurenshi da Yasmeenah kuwa babu abinda ya canza. True colour dinta ya bayyana sosai, samsam bata da kunya ko kadan. Gatada tsiwa yana cewa kule zata ce chas.

Abinda ke bashi haushi shine rashin iya girkinta. Kwata kwata bata san yadda ake sarrafa ɗanyen abinci a mayar daffafe ba. Kawai managing yakeyi saboda bayaso ya tsinka ta wajen iyayen shi ya rinka cin abincinsu har su gane.

Sau da dama yakan kira Abla ko Bilqees suzo tayata aiki duk a zatonsa hannunka mai sanda yake mata, ita kuma bata san wannan ba suna zuwa take naɗe kafa ta fara kallon Korean series ta barsu su kadai cikin kitchen din.

Gajiya yayi da ɗabiarta ya hanasu zuwa , dama suma basa santa at all. Ta rinka daka masu ihu kenan kamar yaranta, abin yafi bama Abla haushi ita dake sa’a da ita.

Ita Abla ta gama Nysc ta soma aiki a Ministry for Women affairs, ita kuma Bilqees za'a shiga 300l.

******

Shikuma Huzaifah baya kwana uku cikarkiya baije ya duba Yasmeenah ba, shakuwa ne sosai ya shiga tsakanin su. Kullum cikin tambayarta yake ko tanada wani matsala wala na kuɗi kona Naufal.

Tun tana ɗari-ɗari dashi harta sake mashi sosai. Musamman yanda idan zaizo yakan kawo su shawarma da chocolate wata rana harda ice cream da kasarshiyar kaza.

Sukan sha hira sosai tana jin daɗin company ɗinsa, Hilal dai bai taɓa zuwa ba amma sauran yan uwanta duk sunje wasu sau daya wasu kuma biyu.

Naufal ya nuna bacij ransa a fili amma bataji ba, sau da dama abin ya jawo masu tashin hankali amma tace bazata daina sake mashi ba.

Thou bai taɓa shiga ɗakinta ba amma bata kiba idan tayi wanka sanye da towel tazo falo suna hira tayi shafa da kwalliya...

Sau da dama tana ba shi kanshi Huzaifah labarin irin faɗan da sukayi da Naufal akanshi, ‘sis kina wuta fah, wallahi bakida dama’ yake cewa.

Wata rana suna cikin hira ya ce, ‘yanzu kina samun ciki kika haihu kema za’a maki kishiya’

“Akan me za’a min kishiya”

“Konine matana ta dauki ciki cikin early years ɗin auren mu to zan mata kishiya dole”

“Kai daban mijina daban!””

“We are all guys, kuma tunanin mu daya ne. Idan zan baki shawara ki dauka toh ki bari nan gaba saiki haihu”

Ajiyar zuciya yayi yana kallonta,yana ganin kamar maganar shi ya fara tasiri cikin ranta saiya soma magana da full confidence babu inda inda, “nifa dan uwanki ne bazan cutar dake ba, mufa maza bama son takura kuma kinsan tara yara ba karamin takura bane”

“Shikenan zanyi tunani” ta faɗa a sanyaye.

“Da yafi maki Lil Sis”

Murna fal cikin ranshi saboda hakkunsa ya kusan fara cinma ruwa, wani smug kallo kawai yake mata ta gefen ido kuma yana kara ma jikinta kallo.

Yau sanye take da blue crazy jens wanda yasha yanka ta wurin cinya da gwiwa, saita haɗashi da chiffon top mara hannu. Yana kallonta yana haɗiye miyau saboda kwanan nan bashida wani katabus sai tunanin ta. Ko barci yanzu gagaranshi yakeyi saboda yanda take masa yawo cikin rai.

Yasa saiya zo ya ganta yake jin daɗi, saidai inda abin yake zuwa mashi da sauke tana bashi free show din jikinta koba duka ba amma yana samun banza. A hankali zai koya mata sanshi harta rabu da mijinta ta koma mashi.

Ita kuma abinda Huzaifah ya faɗa mata ya soma mata yawo a cikin kanta, tabbas akwai kamshin gaskiya a tareda zancen saboda gashi Fadeela bata gida kuma ta lura tun kanta haihu take chan gidan. Ita yanzu duk wani hanya da zata bi ta malleke Naufal take nema, idan rashin haihuwa zai zame mata mafi saukin toh shi zata bi.

Yanzu idan Naufal ya dawo zata faɗa mashi suyi tsarin iyali, sai wani zuciya ya raya mata cewa gwara tayi abinta ita kaɗai babu wanda ya sani.

Chuchu Stores and Pharmacy taje ta siyo contraceptives kala kala na kamfani daban daban. Haka ta rinka shan abinta bada sanin Naufal ba.

Three months later........

Koda Naufal yaga batada ciki bai damu ba saboda Fadeela itama haka tayi kafin komai ya daidaitu mata. Bashida wani buri daya wuce ya tara iyali sosai, gashi har yanzu ba’a ga Pha’eexah ba.

Saidai IG baban Khattab yace har yanzu suna kan case din baza’a huta ba sai anga karshen abin. Shikuma Khattab ya koma bakin aikinsa yanayi sosai.

Sunyi kacha kacha da Lili har yayi sanadiyar barinta gidan su, yaji dadi sosai saboda yanzu yana samun ya wataya.

Saidai har yanzu zancen wata budurwa kuma baiyi ba. Bayada lokacin kallon wata ‘yamace kuma. Soyayyar Miemie yana nan fal cikin ransa kamar basu rabu ba, ya rasa inda zaiyi da irin abun.

Wata rana yana zaune cikin office ɗinsa, wayarsa ya dauka yana kallon screensaver ɗinsa wanda hoton Miemie ne bai cire ba. Kawai daukar mukullin motarsa yayi saiya nufa gidan gona.

Ya shiga anyi gaisuwan mutunci da Anty da kuma Deela, yanzu ta murmure ta soma magana sama sama tunda dama surutu ba ɗabi’arta bane.

Shiru yayi baice komai ba, ya rasa Dalilin zuwan shi gidan.

“Lafiya dai koda wani matsala ne?”

“Lafia lau Mommy” ya amma yana inda inda.

Suna cikin haka saiga Abla ta shigo cikin falon tareda sallama. Deela da fara’arta ta daga ta kalleta “Wata sabon gani, Abla kin share ni”

“Ba haka bane Momyn Pha’eexah, Boss dina tayi tafiya zuwa Abuja yasa nike komai a office. Wallhi Yanzu banida wani isarshen time”

Zama tayi akan Couch na 2 seater Kusa da Fadeela, “Ina wuni Anty?”

“ina gajiya Abla ya aiki?”

“lafiya ya gida?”

“Alhamdulillah, yasu Mamanki?”

“Duk kalau suke”

Suna gaisuwa amma attention ɗin Khattab yana kanta, tabbas itace ke masa sukuku cikin rai kuma dalilinta yazo gidan nan. Soyayyarsa da Miemie yayi zurfi yanda bazai iya maye gurbinta da wata mace ba amma ya rasa gane dalilin da yana jin wani iri idan yayi tunanin Abla.

“Ina wuni Khattab” Abla tace, dayake yayi zurfi wajen tunani saida ta sake maimaitawa kafin ya amsa.

“Lafia lau” ya iya cewa saboda yadda zuciyar sa yake gudu da sauri. Mikewa yayi ya tafi.
Chapter 43 · 0% Book details