← Book details Nida Diyata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 48

Sashe 45

Nida Diyata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaban Sadeeq ya faɗi sosai saboda a duniya abinci mara daɗi ne baya so. Haka suka ci abincin suna zare ido tareda shan ruwa, kuma kowane cokali saika kora da ruwa saboda babu inda zai wuce da kansa. Kwata kwata bashida dadi kamar an wanke kan mahaukaciya!

Sun gamaci sai nishi sukeyi kamar sunyi aikin karfi, “Amarya mun gofe fah, Allah ya saka maki da alheri da duk abinda kikayi mana” Sadeeq yayi mata ba’a.

“Haba dont mention, it’s my pleasure” ta amsa tana yauki, dayake bata ciba so bata san how horrible abincin yake ba. Ba Aminu kawai ba har Naufal saida ya bushe da dariya saboda sun san abinda Sadeeq yayi.

“Amaryar Naufal kina sha’aninki, Allah ya barku tare” Aminu yace yana kyallara ido ma Naufal.

“Amin summa Amin” ta amsa.

A hanyar rakasu sai mashi iskanci sukeyi, “Ashe dama haka kake kwasan dadi, yasa naga kayi fari fat kamar fatalwa. wannan shine kaikayi ya koma kan mashekiya”Sadeeq yace.

“Aikuwa dai, kaso musguna ma Deela babu gaira babu dalili shi ne Allah ya kama ka” Aminu yace.

“Nifa kasan har daina magana yayi min, don kawai ina bashi shawara akan ya bar zancen auren nan. Amma yanzu me gari ya waya ka dawo gida ga wani katon banza ya hakince yana kallon matar ka tana mashi rawa” Sadeeq yace yana kwafa.

“Wallahi na rasa yadda zanyi da ita ne, kamar ta raina nine” Naufal yace a sanyaye.

“Ai babu tantama ta gama rainaka, if not bazata yi haka ba, but ai duk tsuntsun daya kirawo ruwa shi yake duka”Aminu yace.

“Allah dai ya kare” Sadeeq yace. Daga nan suka yi sallama suka wuce.

**********

Soyayyar Abla sai kara zama yake a zuciyar khattab, bata bashi fuska at all. Kullum saidai yazo yayita inda inda baya iya cewa komai. Gashi har yanzu bashida number ɗinta.

Wata rana yana zaune a cikin Office dinsa saiya dauki alwashin yau zai gaya mata abinda ke cikin ransa. Ya tashi bayan yayi Maghreb saiya tafi gidan su Abla.

Maigadi ya fada mashi cewa Abla bata dawowa, dafa kansa yayi yana tunanin inda take sai kawai ya yanke shawara ya tafi gidan gona ya dubata tunda bashida number ɗinta balle ya kira ya tambayeta.

Ita kuma Deela ta samu sauki sosai, ta mayar ma Allah komai saboda yanzu har magana takeyi. Ta murmure sosai har Naufal yana tunanin yayi mata maganar komawa ɗakinta koba komai zai samu abinci sosai.

Tunda yanzu bawai yana samun abinci isarshe bane, Yasmeenah da kanta tace mashi ya rinka cin lunch dinsa a waje saboda bazata dauki nauyi ba.

Missing fadeela yakeyi sosai saboda ko kadan bazata mashi haka ba, dama Hausawa sunce idan baka gode ma alherin da Allah ya baka ba zaka gode ma azabarsa.

Ita Abla daga wajen aiki kai tsaye gidan gona ta wuce saboda Deela tanata mata korafi akan ta watsar da ita. Suna zaune akan gado suna shan fruits salad suna hira cikin dakin Miemie wanda yanzu ya zama na Fadeela.

Fadeela tace mata ta kwana ita kuma tace batada su brush da kayan sawa. “Indai wannan ne matsalar ki karki damu zan baki”

“Allah ya barmin ke matar Yaya”

Wayan Fadeela ya soma ringing sai taga sunar Khattab baro baro akan screen.

“Assallamu alaikum”

“Waalaikumus salam Khattab ya kake ya aiki?”

“Alhamdulillahi” sai kuma sukayi shiru na wasu dakikai kadan.

“Dama Anty ina kofar gidane bansan ko Abla na kusa ba kice mata ta fito”

“Eh gata gefena, babu damuwa” daga nan suka kashe wayar. Deela da fara’arta ta soma magana, “Khattab huh! Gaskiya naji dadi sosai”

Hada rai Abla tayi sosai, bata kula Deela ba kuma batada niyyar fita waje yau saboda zuwansa ba karamin takura bane a wajenta.

“Tashi mana ki fita kin barshi a waje, wulakanci bashida kyau dai”

“Saurayin Miemie ne fah!”

“Wani Miemie kuma? Wanda ta rasu ko wata daban, yarinya na ciki kabari kina lakata da wani saurayi. Koko shi Khattab din katako ne da bazai sake aure ba?”

“Nifa bawai wulakanci nakeso nayi masa bane, kawai banaso mutane su ce na kashe sister dina domin in aure saurayinta”

Deela bushewa da dariya tayi sosai. Ashe Anty tana jinsu, a hasalce ta fara magana, “Bada bakinsu zasuyi magana ba, sufa suke kiɗansu kuma suke rawar su. Fatan Alheri kawai zakiyi ki mance da komai”

“Kuma idan zan baki shawara kiji tofa kiba yaron nan haɗin kai, haba sai kace shi kadai yazo duniya, ya gama wahala da Miemie yanzu kema zaki saka mashi ciwon kai”

“Ai kuwa dai, yana kokarin sosai ga shida kamala” Deela tace. Ita dai Abla bata ce komai ba kawai zata yi nazarin abinda suka ce ne. Anty ne ta cigaba da magana, “Sau nawa kuma sai kiga Miemie bata rasu ba an fasa da ita ayi dake... Idan fa shine mijinki babu yadda zakiyi gwara kisan me kikeyi”

Haka ta tashi rai bai so ba ta saka mayafi ta wuce wajenshi, sallama tayi mashi sai suka gaisa. Daga nan tace masa su wuce cikin Falo amma yace ta barshi cikin motar sa.

Sunyi shiru for like 45mins, ita tana wasa da yatsunta shikuma ya kafa mata ido. Dama yaso ya kureta ne yaga ko zatace wani abu amma batayi ba. Tun dayake zuwa wajenta basa kai 30mins, mostly 20mins saiya tafi.

“Saidai na kashe ki amma bazaki ce komai ba” bata amsa ba kawai kanta yana sunkuye da kasa.

“Abla”

“Na’am”

“Inaso idan zaki min magana ki rinka kallona”

“Toh” saidai kuma bata kalleshi ba.

“Abla me kike min haka? banida wani tunani yanzu banda naki.... Please Abla answer me ko zanji saukin radadin danake ji.

“Ni babu abinda nake maka” ta fada a sanyaye, shikuma kaima steering duka yayi.

“Haba Abla ji yanda kike treating dina kamar nayi maki wani laifi, bafa ni na saka ma kaina ba. Allah ya daura min. Though nasan kina tunanin zanyi replacing Miemie dake ne but Wlh komai dana ke jin maki its different”

Shiru tayi kawai tana nazarin abinda yake faɗi, “Abla tunanin me kike yi? Kin tsane ni koh... Meyasa kike min haka?

“Nifa ban maka komai ba tun dazu kace nayi maka wani abu”

“Kamar ya bakiyi min komai ba, shirun nan is killing me. Nafiso ki saki jiki ki rinka mini magana please”

“Toh ai kaima baka magana”

Dariya ya soma, “Haba baiwar Allah ta ina kikeso nayi magana bayan kin haɗa rai....salan ki wanka min mari. Please oooo i like life” Murmushi kawai tayi daga nan saita soma hamma alamun barci.

Wayarshi ya fitoda akan ta karanta mashi lambarta, ita kuma sai ta amsa zata saka da kanta amma yaki, dole ta rinka kiran masa yana yi da kanshi. Saidai kuma idan tace 7 sai yace 5, haka taketa gyara masa har suka gama.

Da gangan yayi mata haka duk salon bata lokaci da ita kuma tace wani abu ko babu dadi. Yayi alkawarin kiranta anjima yaji amsar da zata bashi akan batun su.

Nan yayi flashing number dinsa sai yace tayi saving ya gani, Khattab ta rubuta mashi.

“Haba mana, Khattab kawai zaki rubuta. Babu dan Baby ko Sweetie yanda yan mata keyi” dariya kawai tayi tana mamakin yanda he is free and very fun.

“Okay ni bari nayi saving ki ga naki” ‘Haskena’ yayi storing dashi. Nan fuskanta ya canza saboda kowa yasan Miemie ce Haskensa. Dariya yayi saiya ce, “Allah ya bani Haske da farko sai kuma ya dauke mani ita. Nayi dangana shine ya sake bani wata”

Daga masa kai tayi alamun ta gane. Itadai kawai tana tunanin irin amsar dazata bashi anjima ne.

Tana isa daki taga Deela tana gyara drawer, kayan suna ne take sake jerawa da kyau. Daga nan sai suka ga Cd plate da aka yi video covering amma basu kalla ba. Fadeela nata ninke kaya daga gefe ita kuma Abla ta dukufa tana kallo a laptop.

An nuna Miemie sosai saboda ko ina tana wajen kamar MTN, ga shi little One itama sai dariya takeyi. Video din yana kunshe da happy moments sosai.

Ita kuma Deela cin karo da kayan Anty Anisa tayi, “Allah sarki baiwar Allah tana chan port Harcourt” Deela tace cikin ranta. Haka ta gama ninke kayan ta ajiye cikin drawer. Saidai kuma wani abin mamaki bazata tuna sanda sukayi sallama da itaba.

Though kuma dai akwai jama’a gashi kuma ya dade da faruwa saboda kusan wata shida kenan idan baima fiba.

Abla na cikin kallo saita tsandara ihu saboda sledgehammer din da akayi amfani wajen kashe Miemie ta gani cikin video.

‘Haba Abla meye na ihu kamar ba musulma ba, ni duk kin firgita ni”

Hawaye na gangaro mata tace, “Nasan wanda ya kashe Miemie”

Da gudu Fadeela ta karasa wajen domin ta gani itama, Abla tayi rewinding amma Deela bayan mutum take kallo. Gashi kuma bata gane ko wacece ba.

“Abla nifa bangane ba.... Wai waye wannan? Kin ganta ranar suna ne?”

“Eh mana Anty, baki gane.......”

#NiDaDiyata

*Shout out to Lubna Sufyan, Hussaina Ubandiya, Sumy Gaya, Jidda, Feeyah Galadanchi, Taatuh, Rukky Mt, Kharriya, Mrs Chubado, Asiya Ahmad, Basira Sabo, Fulani, Asmeebae etc, Thank you from me to you*

#AinauMardiyah[2/3 11:00] DIMPLES: ©Exquisite Online Writers
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

💦 Ni Da Diyata 💦

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Written by DIMPLΣS
Wattpad @Aynarh_dimples

💦Dedicated to Xaynarb B Idreez 💦

✨✨✨Page 39 ✨✨✨

An-Nawwas bin Sam'an (May Allah be pleased with him) reported: I heard the Messenger of Allah (Sallallahu 'alaihi wa sallam) saying, "The Qur'an and its people who applied it, will be brought on the Day of Resurrection preceded with Surat Al-Baqarah and Surat Al-'Imran arguing on behalf of those who applied them."[Muslim].

*******

Kuka Abla ta fashe dashi ta kasa magana, “Ki fada min wacece mana tunda ke kin ganeta”

“Anty ki kalla da kyau mana, yanzu baki gane wannan Anty Anisa bace?” Ras! Gaban Deela ya faɗi, kara kallon video din tayi kuma lallai babu makawa wannan Anty Anisa ce. Kuka ta barke dashi wiwi saboda bata taɓa tunanin Anty Anisa zatayi haka ba.
Chapter 45 · 0% Book details