Sashe 9
Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Mama, ai ita k'waryar tasan da 'Yar uwarta, amma Sai ta zab'i bin a kushi. Kenan ita taso taji kunyar. Salima ita ta fara nuna muradin'ta a kaina, duk da tasan wanene ni, me nake dashi. Daga k'ulla a bota da mutunci farkon had'uwa ta mai dashi soyayya. Bazan b'oye ba, wallahI, tun da na had'u da 'yarki mama ta Shiga raina sosai. Amma banyi a zarbabin nuna mata ba, Sai da ta fara. Kinga kuwa 'yarki ta rakito Miki ni. Kuma burin Mutum, ubangiji ke cika masa a Sanda duk yaso. Babu kusa kuma babu nesa. Saboda haka a kowani lokaci, ban fitar da ran cikar burina ba. Kuma bana gaggawa, na barwa mahalicci na ikon'sa a kaina. Salima kuma Ina mai tabbatar Miki bazata rigani aure ba, saboda nasan duk runtsi bazata iya auren Wanda ba ta so ba. Duk tsayin shekaru nasan Sai ta jirani, da ta auri Wanda bata so. Kinfi ni iko da 'yarki, amma nafiki kusanci da sirrikan dake zuciyarta. Babu a binda take b'oyemin. Ba kuma zan iya jiran Salima ba, saboda burin da aka ci mata. Zan yi aure a kurkusa, saboda addini mata hud''u ya halattamin. Zan auro dai dai dani a arzik'I. Ban kuma bar Salima ba,zan aure ta idan damar hakan ta samu a gareni duk jimawa. Bata da laifi, kuma nasan tana Sona. Wannan shine uzurin da yasa zan aure ta. Ba domin haka ba, to Wallahi da na barta Kenan har a bada. Domin bana waiwaye idan nayi gaba, in dai aka nunamin iyaka ta, akan komeye."
Daga haka sallama yayi mata yayi gaba. Bai jira ma me zata ce ba. Amma ya lura maganganun'sa sun kad'ata."
Kawu Sulaiman ba dad'a ba, bai raga ba, Sai ga kakana ya shigo, wato Mahaifin'sa. Da sauri Kawu Sulaiman ya karb'i jakar da take hannun'sa, ni kuma na karb'a daga hannun Ancle. Ya dubemu yace.
"Hira kuke kai da 'yar taka?" Yace"Eh! Baba. Wata magana muke tattaunawa.
Yace.
"Zan kuwa katse muku hanzari kwa k'arasa daga baya. Wata unguwa nake so ka kaini Sulaiman ta gaida Mara lafiya. Dan babban a Minina a ka kwantar a asibiti saurayi babu yarda yake. Ai baburin'ka lafiya yake ko?"
Kawu yace"Ai na gyarashi Baba. Dama matsalar kafireto ne. Yace" To, Muje ka ka kaini. Nan hirar tamu ta datse. Ni kuwa na k'agu naji yarda al'amarin ya Kaya. Da kuma Maganar da Kawu Sulaiman yace za muyi ta musamman.
*🏤 NI DA GIDANA 🏤*
*_Littafi na daya_*
*NA*
*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
📱8
_______ Kwana biyu ne rak tsakani , muka sake Samun sakewar ci gaba da hirar Yarima, wato Fa'izu Bukar. Baba Talatu tana d'akin Baba, wato kakana bayan kai masa bincin dare suna tasu hirar suma.
Kawu Sulaiman Yaci gaba da cemin.
"Sumayya Yarima yana buk'atar aure a kurkusa, domin yace Sai ya d'au fansa. Sai ya maida martani. Yaci alwashin, Sai maman Salima tazo tana rok'on'sa ya auri Salima, kuma Sai ya garata sosai. Yace Sai ta aza kwandon dana Sani a kan'ta tayi yawo dashi ta gaji."
"Idan na fahimci dai dai, auren huce takaici Ancle Fa'iz yake so yayi?". Injini
"Haka ne, Sumayya".
Na sake cewa.
"Ancle har Yaushe Zai samu Wacce yake so cikin gaggawa yayi auren."
"Kawu yace"Maganar a ce Sai ya samu Wacce yake so bata taso ba Sumayya . Karki manta fa Yarima wato Fa'izu a cikin soyayya yake bai fita ba. Bai daina son Salima bafa, suna tare har yanzu. Amma bai fad'a mata a binda maman'ta tayi masa ba. Yasan kuma bata Sani ba. Yace ko Salimar bazata San zai yi aure ba, Sai ya basu katin gayyata".
Nace.
"Amma dai Zai tashi hankalin Salima Gaskiya.Zai kid'imata ainun. Daga Sama fa zataji komai, Bayan yasan suna son juna."
Kawu na yayi murmushi.
"Ai hakan shine muradin'sa. Mahaifiyar Salima tana mugun son'ta kamar rai. Idan kuwa hankalin Salima ya tashi, ta Shiga tashin hankalin da bata tab'a zato ba, to fa neman a gaji maman nata zata tafi na ceton 'yarta. Kuma dole Sai wurin Yarima".
Kawu Sulaiman yasa Wata siririyar dariya.
"Yarima yasan takan tsiya".
Ni kuwa jagale nayi Ina kallon'sa.
Yaci gaba da cewa.
"Satin da ya wuce, na sameshi wurin training. Bayan ya gama nace masa me a ke cikine yanzu.
Yace min har yau bai nutsu wurin Samun Wacce Zai aura ba. Yace yanason yarinya mai Hak'uri da hankali da addini ba Ballagaza ba. Domin Sai da mai irin wannan kyawun halin Zai cimma manufar'sa ta a binda ya himmata cikin nasara.
Amma Wai a bokan'sa suna ta kawo masa tayin mata da suke ganin sun isa a sosu, bai je ya gan'su ba. Kuma ana ta kawo masa hotunan 'yammata kyawawa a cewar'su. Hotunan yace baisan a dadi ba, tun da ko bud'awa ma bai yi ya gaggan'suba.
Na tambaye shi me yasa.
Yace shi ganin hoton mace bazai gamsar da shi da komai ba. Ya ganta a zahiri, yayi kuma hira da ita, tanan zai San ta can can'ta.
Nace masa, yanzu idan aka kawo Maka ita kaga tayi zaka aura? Yace min.
Maganar Wai a ce tayi min ma, baya cikin tsarina, kuma bana kwad'ayin hakan, saboda nasan ba za ta tab'a yi min d'in ba ne. Sai dai Kawai na aureta saboda wad'ancan halayya idan na tabbatar tana da su.
Kawu Sulaiman ya dubeni sosai yace.
"Sumayya kin yarda dani?" N'a gyad'a kai, cike da mamakin furutan'sa. "Na yarda da kai fiye da kowa Ancle."
"Akwai Abinda zan umarceki kika sayi min Sumayya?"
Nace"Sai Sab'on mahalicci dai?".
Yace"To, Sumayya Ina so ki auri Fa'izu, wato Yarima."
Na kad'u k'warai da jin furutan'sa, na kuma gaza cewa komai Sai sunkuyar da kai.
"Yarima ya bani zab'in na samo masa irin Wacce yake nema in dai Ina da iko. Ni kuma ke Zuciyata ta halarto min, kina da irin wad'annan d'abi'u, kuma ke kad'aice a bar iko na a duniyar nan. Kina da irin wad'an nan d'abi'u da Yarima ya zayyano, har ma da k'arin wasu kyawawan da bai Sani ba. Ke kika dace da auren irin Yarima, Amma je da shi baku Sani ba. Kuma nasan ko kun Sani, bazaku yarda cewa kun dace da juna ba a d'abian'ce tun da kowa a bai bai yake kallon d'an uwan'sa. Kiyimin alfarma Sumayya ki a mince da auren Yarima. A Kwai dalilai da yasa nake yi Miki Sha'awar auren'sa. Sai kin amince zan fad'a Miki, kuma ba yanzu ba, Sai dab da auran."
Jikina yayi sanyi, na lalubo k'arfin hali nace.
"Ancle bani da Uban da ya fika yanzu. Zaka iya zartar ma da hukunci a kaina a duk San'da kaso, ko bansa ni ba. Amma idan kafiso kaji daga bakina ne, to na amince"
Sai da na daure iya dauriya domin farantawa Wanda ya fikowa so'na da son farin ciki na, amma ba domin raina na son auren Yarima ba. Auren da na tabbatar bazan tsinci ribar komai a cikin'sa ba, face k'ask'anci, bayan rashin rabauta da soyayya irin Wacce nake buri a aure, nasan Fa'izu da murd'ad'd'en halin'sa,mai iyawa da shi bazan babu ba, amma Sai Wacce taci hak'uri ta tada kai dashi, har tayi guzuri. Ma'ana mai hak'urin gaske.
Kawu ya cika da farin ciki Mara misaltuwa game da a mincewa ta. Albarka kuwa nashata kwando kwando.
Na kasa danne amma tambayoyin dake tayi min zallo a zuciya ta nace
"Kawu, Ancle Fa'iz fa ya sanni tsayin zamani, bai nuna yana da muradin Irina bafa"
Yace"Na fiki sanin haka."
Ganin bai d'ora ba kan haka na sake cewa.
"Na Sani, kuma kai ma ka Sani Ancle Fa'izu baya Sona, kuma nasan bazai tab'a Sona ba."
A cewar Ancle.
"Na yarda yanzu Kam baya son'ki.Saboda bashi ya nuna ma muradi a kan'ki ba. Bai kuma hakarto kima cikin macen da Zai yi auren huce takaici ba. Amma hakan bashi yake nunin Bazai tab'a sonki ba. Ko bai soki yanzu ba , Zai iya son'ki nan gaba. Idan kuma bai sokin'ba to Bazai wulak'antaki ba Sumayya. Saboda kina da d'abi'u irin na mata na gari. Kuma irin'su basa tozar'ta a gidan aure.
Yaja dogon numfashi.
Ki kwantar hankalinki. auren'ki da shi ba lallai bane. Jarraba sa'a ta zanyi na k'OK'arin had'a auren ki da shi, saboda Sha'awar hakan, da ganin dacewar hakan. Yarima kaifi d'aya ne. Bashi da shayi, ko jin nauyi na b'oye a binda ke cikin zuciyar'sa. Zai iya cewa ya amince da aurenki, Zai kuma iya cewa Sam bai a mince ba. Saboda haka ki tsaya a k'ila wa k'ala."
Jin haka na d'an samu nutsuwa. Dabara ta fad'omin. Daren Ranar ko bacci ban samu ba ko na awa d'aya. Addu'oi nayi tayi da nafilfili kan aure na da Ancle Fa'izu kar yayiyu. Rashin yiyuwar dai yace baya ra'ayin Sumayya a aure. Da wannsn niyyar nayi ta addu'a.
Nasan cewa Fa'izu yafi gaban a ce ba'a son'sa. Amma Ina! nasan ko kusa bazamu dai dai ta bane. Saboda irin sanin halin'sa da nayi lokacin da yana koyar damu. Ni burina nayi auren soyayya mai dad'i da kwanciyar hankali, kuma d'orarre. Ta ya ya kuwa Zuciyata zata so irin wannan aure? ai daraja kan daraja irin ta Kawu Sulaiman Kawai zan yarda na aureshi, duk da nasan makomar bazata yi min kyau ba. Amma duk da haka bazan iya bad'awa kawuna k'asa a idanu ba. Bazan iya ba.!
Na had'a Kayan miya Ina sauri zan markad'a a blender, saboda kar su d'auke wutar. Kawu Sulaiman na gani ya shigo kichean, a binda ba sabon'sa ba. Nace"Sannu da zuwa my Ancle."
Cike da wani farin ciki da bansan musabbabin'sa ba yace"Sannunki da aiki shalelen Ancle. Kin ganni har tsakar kichean ko?
Kafin na samu amsar bashi ya zarce.
"Sumayya Yarima ya amince da auren'ki. Abinda bani da tabbas d'in yiyuwar'sa, Yarima ya tabbatar min."