← Book details Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 31

Sashe 29

Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

📱23
_______ Kawu Sulaiman yace "Wani irin Zancen shirme da rashin tunani kike haka? auren naki kike wa fatan ya mutu? to idan ya mutun uban wa zaki aura? Ko kina nufin zaki samu Wanda ya kai rabi rabin Yarima a komai? to Yarima zuwa ma zai yi yace ban hak'uri a dai dai ta ki koma. Ga muryar sa ma na fahimci yana cikin damuwa, na a binda ya faru. Kiyi murna Sumayya ma domin na fahimci Yarima yanayi dake. Inda bai damu da ke ba, babu yarda za'ayi yayi haka, har yace yanzun nan ma zai taho. Nafa san Yarima kamar yunwar ciki na. Ni Sam a yanzu, ni damuwar Yarima gareni bata dameni ba, burina Kawai ya sakeni. Na so Fa'iz Zunzurutun SO, Wanda har so nake na saita kaina a gaban'sa kar ya fahimta, amma Ina!, nakan kasa sarrafa kaina sau tari, shi yasa shi da kan'sa ya fahimta, domin Yana da saka idanu na fahimtar a bu nan da nan.
Amma yanzu haka ji nake ko zan rasa Mijin aure a gaba na dawwama babu aure zan iya, in dai Sai da Ancle zan rayu. Mummunan k'azafin da a ka yi min yasa duk son zama dashi ya sanemin, koda kuwa shi yana son dawwamammen zama dani na yafe. Abin kunya ne ma ni a gareni na koma gidan'su da zama, ana yimin kallon mutuniyar banza mai aikata alfasha kuma da k'anin Miji. Koda iya ma gidansu zancen zai tsaya zan Shiga garari, ballantana nasan Sai anyi ta kwaza zancen yayi ta yawo a dangi, tun da dama so ake a b'ata min suna. Ban san Sanda na sake sakin Kuka ba, saboda takaici .

"An cuceni, an zalinceni, Allah ka sakamin" A she zancen ya fito fili bansa ni ba, Sai ji nayi Kawu sulaiman yace.
"Haba Sumayya, kiyi hak'uri mana, tun da dai mijinki yana bayanki menene na d'aga hankali.

Na dubi Kawu nace.

"Kawu ka gafarceni, Allah bazan iya zama da Ancle Fa'iz ba, ka sashi ya bani takarda bazan iya ba Kawu."

Ya zubamin idanu kafin yace "Don Allah Sumayya ki shigo nutsuwarki, komai yayi zafi maganin sa Allah. Wallahi bazan iya yi miki yarda kike so ba, saboda nasan ba zaki sake Samun dacen Miji irin Yarima ba. Kyauta ce, ni'imace, baiwa ce, d'aukaka ce, Samun Yarima a gareki. Kyauta ce mai girma daga Ubangijinki, da dabararki da wayonki, ko wani abin duniya ba zasu tab'a baki ba. Dama wasu lokatan bayi butulci ne da su. basa tab'a sanin ni'imar da Ubangiji yayi musu, sai sun rasa. Kuma misali ma a ce kin rabu da Yarima, Kinsan in da zaki fad'a? Kenan duk in da kika ga matsala Sai ki fito ko? Haba Sumayya! mijinki ya yarda dake ma ai daraje ce babba. Kuma Sai da aski yazo gaban goshi zaki zame zame ladan wahalarki ki yar ? Ina mai tabbatar Miki Yarima ya soma sonki, tun da har yake kok'arin a daidaita ki koma, baya ma duba ga rashin son auranku da mamansa ba tayi, duk da irin Soyayyar da yakewa Momin.
Nace "Kawu, Ancle Fa'iz yana so na koma ne, saboda yasan wa'adin aure na da ya d'iba bai cika ba, so yake Sai ya cika ya sake ni ya auri Salima."

Da sauri Kawu Sulaiman yace "Wannan Zancen shirmene Mara tushe. Tun Yaushe wa'adin auren ya cika amma bai sakekin ba.? ai tun daga lokacin da maman Salima tayi laushi ta sauko ta Shiga zabarin neman Yarima wa'adin ya cika. Dama burin sa Kenan ta sauko ta gane kuskuranta tazo kuma tana rok'on sa ya auri 'yarta, kuma tayin, domin tasha zuwa in da tasan Yana zuwa tana bashi hak'uri da rok'on yazo su sasanta ya auri Salima. Sai dai idan kece bai fad'awa ba."

Bakina ya mutu saboda rashin Samun hujjar mafaka, amma fa Zuciyata tana nan daram, banason zama da Ancle Fa'iz.
Yace "Tashi ki Shiga gida, kuma karki kuskura, ki fad'awa kowa a gidan me ya faru. Kice unguwa zaku da Yarima kika biyo gaishe su, saboda nasan kika fad'awa Baba Talatu,Sai ta fesawa Hajiya Mariya,Sai suzo a kwab'e lamarin Maimakon gyara. Ki gyara fuskarki, ki kuma a jiye jakarki anan kar su d'ago komai."

Baba Talatu tana tsakar gida tana Shara da na shiga, ganina ta jefar da tsintsiyar tace "Ke kuma lafiya da duku dukun nan?. Daga bayana naji muryar Kawu yace" A sibiti zasu je idanunta ke ciwo, ba kiga ma yayi jajawur ba.?"

Ta dubi fuskata tace"Ai kuwa gashi nan har kumburi ma yayi, Allah ya sawak'e nace "Amin."
Kawuna a Kwai kwanyar dabara da wayo, nace a zuci.

Kakana yana d'akin sa, na Shiga na gaisheshi, Shima irin tambayar Baba Talatu yayi min, na kifeshi bai bai. Gaba d'ayan su, suka Sani a gaba, cike da murna da hira. Zuciyata a cushe take da k'unci, haka na rink'a daurewa ina biye musu, domin kar su fahimci Ina cikin damuwa. Baba Talatu ta gewayeni da Kayan Karin kumallo. Ga yunwar Ina ji, amma yak'i shiga. To rashin walwalata ya soma tonamin a siri, saboda sun San halina yarda nake buwayar su da tsokana da wasa, Sai suka jini nayi Lak'was Sai hira Sama Sama.
"Sumayya babu a binda ke damunki?" Inji kakana.
Na k'agi fara'ar dole.
"Zazzab'i Sama Sama ke damuna, amma tun da zamu a sibiti sai su bani magani."
"Allah, ya sawwak'e." Suka had'a baki tare.

********

Kawu Sulaiman ne, ya shigo yace "Sumayya mijinki ya iso, fito Ku tafi." Kamar na Saki ihu Amma na daure gudun b'acin ran Kawu na, da rufa a sirin da yake so a sirrinta.
Nayi wa tsoffina sallama suna ta shek'amin albarka da addu'ar Samun lafiyar larurorin da na d'orawa kaina.

Ancle Fa'iz da shi nayi tozali, saboda yana fuskantar k'ofar Shiga d'akin hard'e da hannu a k'irji. Shirt ce a jikinsa ruwan makuba mai dogon hannu mai Lin's.Sai wando, trouser da ya dace da shirt d'in duk da kalar ba iri d'aya ne, amma sunyi masa d'an Karen kyau, kamar ko yaushe a bin a halittar ne, mai yarda da hakan, Sai Wanda yaga my Ancle kawai. Mun had'a ido, amma fuskarsa babu annuri, ko sakin fuska Sam. Hakan ya nunamin cikin damuwa yake sosai. Ni kuma hawaye ne suka soma zubar min, Ina gogewa suna sake zubowa, Ina gani yanata kallona da Ina kukan, Sai kuma ya kau da kai ya dubi Kawu Sulaiman.

"Sulaiman wannan a bu da ya faru nine sanadi, Wallahi Nike da alhaki, saboda haka yanzu kaina nake ta tuhuma da zargi."

"Kamar Yaya Yarima?"
Yace "Sulaiman tun farko na rufeka, amma na fad'awa Sumayya, ta yiyu ta fad'a Maka. Na auri Sumayya da Wata irin k'udurtacciyar manufa, bada zuciya d'aya ba,da nufin burina yana cika zan saketa, ta auri Wanda take so, amma ban yarda wani a bu ya ratsa tsakanin mu ba na auratayya, saboda waccan niyyar. Shi yasa yanayin zaman namu ya fallasa kan sa, kowa ya fahimci ban d'auki Sumayya da daraja irin ta matar aure ba, tun da manyan hak'k'ok'in auren na saryar, kuma ko a jikina. Wannan dalili yasa kowa ma a gidan yake mata a binda yaga dama, ta zama taka haye. Wasu a bubuwan ma gaskiya ina gani a nayi da basu dace ba, amma Sai na kau da kai, ko kuma nine ma zan yi a binda bai dace ba, a cikin zamana da ita, duk tunani na na wani lokacine tun da rabuwa zamu yi a gaba kad'an. Wannan babbar matsala ma da ta faru, nine umda na sanadi, domin da Ina kwana d'akin Sumayya, Khalifa yama isa ya shigo?"

Kawu Sulaiman ya gyad'a kai na gamsuwa. Ni kuma sunkuyar da kai nayi, saboda jin kunyarsu su duka.

Shiru ya ziyarci wurin na sa'oi Sannan Ancle Fa'iz ya tausasa murya yana mai kalloni yace.
"Sumayya ki yafemin, nine sanadin jefaki a matsalar nan. Nina jawo a ka cutar dake, kuma ba halina bane, ban kuma niyyaci hakan ba,k'addara da tsautsayi ne." Kukan da na kasa tsaida shi yasa ban iya amsa masa da baki ba, Sai gyad'a kai.

Kawu yace " Komai ya wuce Yarima, kuma ai anyi mai wuyar tunda ka fahimci kuskuren.kuskuren ka d'aya ne, daka d'ora auren ka na sunna kan Wata gurb'atacciyar manufa da niyya, shi yasa dole a tarar da abin k'yamata.Duk da haka kana birgeni Yarima, saboda gaskiyarka da fad'enta ko da kuwa a kanka ne.

Ancle Fa'iz Yace "Son zuciya nabi Sulaiman, ba dole na karb'I raddin b'acin ta ba.Buk'atata Kam ta biya, amma kuma ta yayi momin manyan matsalolin da na rasa ta Ina zan fara wurin warwaresu. Yayi shiru Sai kuma naga ya d'aga kai zuwa ga kallon silin Sama, ya lumshe idanu, ya rage sauti yace a hankali. "Da nasan zuciya ta zata jarabtu da wannan a bu, da ban aikata a binda nayi ba. Nayi nadama ta k'arshe."

Muna jinsa Sarai ni da Kawu na, amma ni ban fahimci me yake nufi ba.
Ya bud'e idanun a hankali
"Sulaiman zanyi gyara a kan duk b'arnar da na jawo ta afku, ka samin idanu Kawai. Ina so Sumayya ta koma d'akin ta kuma a yanzu, Kayi min alfarmar nan."
Sai gani nayi Kawu Sulaiman ya Saki murmushi. "Shi yafi komai sauk'i hakan, Sumayya cikin ikonka take fa, ka tuna. Amma fa ka kula sosai wurin zartar da komai kayi a hankali, kar ka b'ata ran Momi."
"Na gama da wannan fannin Sai k'arashe Sulaiman. Idan a Kwai wani mahaluk'I a Duniya da yake iya lallab'a Momi, da jawo ra'ayinta da sanyayar mata da rai, to nine na farko. Kafin na taho na sarrafa Zuciyarta da wasu kalamai ta sauko, Sai dai na k'ara bik'i idan na koma."
Sosai Kawu Sulaiman ya nuna farin ciki, ya dubeni yace "Tashi Ku tafi Sumayya."
Ai kamar yace na b'arke da kuka .

"Wallahi bazan iya ba, bazan iya tozali da kowa na gidan ba, Kayi min aiikin gafara Kawu bazan iya Zaman auren nan ba"

Ran Kawu Sulaiman ya b'aci,ya tasomin da hargowar wani irin fad'a kamar zai bugeni, Sai Ancle Fa'iz ya dakatar da shi.

"Don Allah barta haka, kar ka k'ara firgitata, ita Yanzun a bar tattashi ce da lallab'awa.
Chapter 29 · 0% Book details