Sashe 20
Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru ya ratsa wurin na mintoci, Sai Iskar Sama dake motsi Tana wulwulawa tana bada iska madaidaiciya mai dad'I, sakamakon d'an yanayin zafi da ya shigo a tsukin.
Ko tausayina yaji, Sai kuma ya tausasa murya Maimakon kausasawa da fari.
"Sumayya, ni Banga a binda Zai sa ki rink'a damun kanki ba. Da a ce tun farko na munafunceki, to shine za'ki damu kanki, idan kika ga wani sauyi. Amma haka siddan ki rink'ayimin tuhumar da gangan? Me na yi Miki? Kullum fa Sai na tambayi me kike so, menene damuwarki, amma duk ban fita ba. Kinsan manufar auren Mu, kin a mince, to me yasa zaki rink'ayi min bore bayan anyi.?
Naga shiru ba mafita bace, gwara na fad'amasa burina ko zanyi sa'a ya a mince, daga nan k'ofar farko ta bud'e.
"Ancle nifa buk'atata ka rink'a yagar min lokaci, muna hira ko Yaya, na samu mai debemin kewa. Su khairat da kake cewa muyi hira basu da lokaci kullum suna kan hanyar makaranta, Boko da islamiyya. Dare kuma Kowacce d'akinta take Shiga, saurin bacci ne dasu. Momi kuma kunyarta nake ji, bana iya sakin jiki muyi hira sosai."
Nayi dace yace"To, zan jarraba yarda kike so, Amma fa ni ba ko Yaushe nake son hira ba, karki zamemin BBC, uwar watso kanun labarai. Dariya furucinsa ya bani, har nayi ta fito fili, saboda yanayin da ya furta. Shima Sai naga yayi 'yar dariyar.
"Ke dai 'Yar tawaye ce rigimammiya, mai fuska biyu kuma. Kin rikita mutane da kuka, kuma kin dawo kina yimin dariya ko? Warki ne ni dai dai k'ugun kowa." Yanayin da muke ciki, da yanayin lokacin, ya sanyayamin zuciya sosai. Naso mukasance daren Ranar da faranta ran juna irin na ma'aurata, koda iya hira, amma Ina!.Mikewa Ancle yayi. Nikuma na tuno da a binda nake son ce masa.
Nace"Am, Ancle"
Ya juyo"Ina jinki Sumayya." Nace"Gobe nakeson komawa makaranta. Yace"Sai yanzu za'ki fad'amin?"
Nace"To, na bari, Sai Jibi?"
Yace"No, Kije goben, tunda kin niyyaci hakan.
Daga nan yayi min Sai da safe ya fita. Inajinsa ya b'amemin k'ofar sosai.
Na kuwa kasa bacci. Da nayi juyi, Sai na hango Ancle Sanda ya tsuguna gabana, ya zubamin kyawawan Idanuwan nan nasa masu hasken blue masu kashe gab'b'ai, yanamin surutai a hankali. Gaba d'aya kasa Dai daita nutsuwata nayi a lokacin. Komai nasa mai ruruta wutar k'auna ce, ga ma'abocin kallonsa. Nasan shi a lokacin babu komai a ransa, burinsa ya shawo kaina Kawai.
*🏤 NI DA GIDANA 🏤*
*_Littafi na daya_*
*NA*
*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*___________________________________*
📱17
_______ Ranar Wata alhamis, Ancle Fa'iz ya shigo da daddare ya sameni ni kad'ai a falo zaune nayi shiru. Mutan gidan duk suna saman Momi ana ta shan hira, da kallon TV. Ya shigo ya zauna, bayan nayi masa sannu da zuwa yace" Sumayya Wai zaman kad'aici menene ribar sa? Sai kiyi ta jan jikinki da mutane, kina ware kan'ki why?" Na d'aga idanu na dubeshi bansan me zance ba. Shi duk zaton sa nike jan jiki da mutan gidan, saboda baisan komai da yake faruwa ba. Na yarda a je a hakan, gwara ya zargenin da na zama nice ta farko da zan soma kai masa k'orafi a kan Maman sa da 'yan uwan sa.
Musamman Momin sa da yake ji da ita matuk'a.
Na daure nace"Kasan fa ni kunyar Momi nake ji."
Yace da sauri "Kinga do Allah ki daina irin wannan gidadancin. Kunyar lafiya? Shike nan Sai kice lalllai Sai dani za'kiyi sabo, ni da ba mazaunin gida ba? Ki gyara wannan hali naki please."
Nace "To". Laifin da ba nawa ba na amsa. Naci sa'a ranar ya zauna wurina, ya d'an d'ebemin kewa, nafi zaton tausayi na bashi, na kad'aicin da nake ciki babu kowa.
A hankali, a hankali kusanci da jituwa ya soma Shiga tsakanina da Ancle Fa'iz. Mukan jima muna 'yar hira, musamman da daddare, Saboda lokacin yafi zama a gida. Ya kan jima a falona, amma kallo yafi yawa a kan hira.
Ancle Fa'iz baya son kowani film Sama da kallon boll , Sai film d'in china. Dole na koyawa Zuciyata son,su duk da bana k'aunar ganin su, basu dameni ba. Amma har kud'i nake sawa na sai C D, saboda shi. Duk da Shima d'in yana sayowa. Duk wani a bu da na san ya naso, tanadar'sa nake yi na tarbeshi da shi, saboda sa'ar da na samu yana shigowa falona ya zauna.
A bin dai da bayaso nake yi, shine narka da shagwab'a. Narka da shagwab'a nake yi masa muraran cikin Mu'a mala ta da shi, musamman idan Ina son yayi a bu yak'i. To shi kuma wannan ce ba ya so, domin bayan k'orafi har hantarata yake yace
"Ke tafi can ki bani wuri, bani son tab'ara. Wani lokaci ya cuno baki yace. Duk Sulaiman ne, ya sangartaki ya shagwab'aki saboda mugunta, domin yasan gidan wani za kije bashi zaki k'warzaba ba.
Wani zubin kuma ya kance "Bari dai na baki wuri ba dani ba wannan tab'arar, Wanda ya sangarta ki, shi zai iya d'auka. To nan na kaishi gargara Kenan, domin ficewa yake ya barni. Duk da bayaso, ni kuma ban daina ba, domin ni kuma ta haka nake so na Shiga jikinsa da zuciyarsa Mu shak'u. To daga baya ma Sam daina k'orafin yayi da ya gaji. Sai dai yayi min shiru, yayi ta danne dannen wayar sa, ko ya shareni ya d'ora idon sa a kan TV, ko ya lumshe ido kamar mai son yin bacci. Idan na kai shi bango kuma ya mik'e kawai ya Fice, Sai yak'i shigomin kuma Sai yayi min ban iska na wani lokaci, ranar da na kai shi gargara Kenan.
Ban ja baya da komai ba, saboda damar da na samu daga gareshi, nayi ta shigo masa da abubuwa iri iri,duk da ina shan kyara, wani zubin, banayin zuciya, domin kuwa ni mai nemace kuma wataran bazai yi ba.
Wata sa'ra dana d'auka, idan zai yiwa kan'sa a bu, Sai nace Sai yayi min, ko munyi tare. Yana da wani a bin yanke farce mai kyau, duk ranar juma'a yake yanke farce da shi. Na kance ya kawo nayi masa Sai yak'i. Ni kuma Sai na takuramasa nace Sai yayi min ban iya ba da kaina. Farkon randa na soma damun sa da magiya, ya jefomin kallon tara saura kwata yace.
"Wai da can wa yake Miki? Ko domin Samun wuri? Nace"Baba Talatu ce. Yanzu kuma bani da kowa Sai kai Ancle, ka taimaka." A ranar fafur yak'i yi min. Amma daga baya ya soma yi min, saboda bak'in naci. Ni bana zuciya, Sannan ga binbinin magiya da kwantar da kai, ta haka naci nasara kan Ancle da murd'ad'd'en halin'sa.
*******
Babbar nasarar da na samu, tasa na k'ara k'aimi. wani lokaci ni da shi a falona, na tsiri tsifa saboda ganin arhar damar ga Ancle Fa'iz. Da. na soma nace "Ancle don Allah tayani tsifar kai."
Ko kallona bai yi ba, a fusace yace"Sumayya kina nema fa ki raina ni da yawa. Nine ma zan yi Miki tsifa?." hakuri na bashi a nan, saboda naga ya d'auka da zafi.
Ban daddaraba wani lokaci muna tare muna kallo na sake tsirar tsifa. Ina cikin yi nace. "Wash!. Ya waiwaye ni."Me ya faru?" Nace"Wani ciwo ne a yatsana da naji, garin tsifa gashi ya yanki wurin"
Yace"Garin Yaya kika ji ciwo?"
Nace "Jiya ne Ina yanka nama".
Yace" Sannu, ya kamata ki rink'a kula."
Na faki idon'sa nayi murmushi. Nace "Ancle don Allah ka tayani, kaga gobe mai kitsona zata zo, kuma ciwon hannu na bazai barni na k'arasa tsifar ba. Please za'ka tayani my Ancle?"
Yace
"Sai dai nayi Miki aski, ni shi na iya Kawai."
"Haba dai aski. Yaya zan yi aski Ina mace dani." Naci gaba da marairaicewa. Yace"Sumayya Wai ni bawan kine kome?"
Na fik'e murya irin ta d'a,a nace" Haba! Haba!!. ai ko a shirin wasan kwaikwayo, dole a ce da Mijin iya Baba. Darajojinka sun girmi haka tuni, Mijina."
Ya sassauto, domin naga ya d'an Saki fuska. "To, nawa za'ki bani na Lada?"
Na marairaice "Haba, my Ancle. Ina Daughter guda sukutum Sai na biya"
Yace "Idan baza'ki biya ba, to kisa Hak'Uri kuwa."
Na Shiga magiya da naci da shagwab'a duk dai, babu shirI ya fizgi kibiyar dake nake mik'a masa cikin fusata "Wannan Yarinyar kin fiye matsin lamba Wallahi, kuma guda d'aya zan Miki, daga shi babu k'ari. Daga d'aya Sai da a ka tafi uku, kuwa, saboda naci na. Amma yanayi yana dunguremin kai. A raina fad'i nake, aje a hakan, naci nasara, tun da ka samu, kazo hannu, hakan yake kuwa tayani tsifar ya zame masa k'ara'I. Ina shan dai sababi, amma Sai na jure.
Wani lokacin littattafan makaranta na na kan kwaso nace ya koyamin wasu a bubuwan. Zai koyamin na gane, amma Sai nace bangane ba, domin Mu ja lokaci. Sai Nasha fad'a kafin ya sake. Duk Ina yin haka ne domin na Shiga jikinsa, da rayuwar sa, Mu k'ara shak'uwa. Kuma bana yarda na zauna nesa da shi, ko tazara kad'an bana bari, jikin sa dab nake rakab'uwa in dai ya zauna. Farko randa na soma yi masa hakan, matsawa yayi. A wayance muna hira na kuma matsowa jikin sa. Sai yace min.
"Wai duk wadatar wurin nan Sai kin matsamin Sumayya?" Murmushi nayi, nayi masa Farr da ido nace"To, ya kake so nayi? bani da kowa yanzu da yafi kusanci dani Sama da kai. Idan ban rab'u da kai ba, Ina kake so naje?"
Bai tsinkamin ba, ya maida kallon sa ga mutuniyar tasa, wato boll. Wannan damar tasa na sake shigar da Wata. Sai muna zaunen, Sai na rink'ayin layin baccin k'arya, Sai nayi luuu! na zubo jikin, sa, har sau uku Ina yi, yana d'an tureni. Nan ma da fari yayi k'orafi yace"Wai menene haka ne Sumayya?" Nayi firgigit Ina mitstsike idanu.
"Me ya faru? Menene Ancle.?" Kamar bansan komai ba nayi. Mik'ewa yayi yace "Na lura kora da hali kikemin. Bari na tarkata na barmiki wurinki kafin kiyi min kora da kara."