Sashe 7
Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na nawa kuma, Wai ance da kuturu ka gama lafiya. Namiji ai yaso yaudarata, amma na nuna masa ni 'yar zamanice ai ni naci dubu Sai ceto, nafi gaban a washeni, domin murucin ni kan dutse ce ban fito ba Sai dana shirya. Ke dai ki jarraba Kiran ko kya dace, idan kina da rabo. A Kwai na kirki a duniya."
A ringin na uku, a ka d'auki wayar kuwa, bayan na k'agu da a d'aga.
Muryar namiji a hankali naji tayi min sallama. Muryar bata da d'agawa irin ta maza.
"Dawa nake magana?".
Nace.
"Sunana Sumayya.....
Bai bari na k'arasa ba yace"Ko zaki taimakeni Sumayya ki had'ani da mai layin wannan wayar da kika kira? Tsintar ta nayi a hanya zan wuce kwana ki hudu da suka wuce. Naji sanyin dad'i a raina nace"Wayar tawa ce wallahi yanzu ma kira nayi ko zan dace."
"Kin kuwa dace 'yammata. Zaman wayar ma a hannu na duk ya dameni, so nake na Mik'ata ga mai ita Kawai. Don da na tsinta caji ma babu, Sai da na Sai mata caza Sabuwa na caza ko mai ita Zai bugo, Sai yau a Kayi dace a ka bugo.
Yaya za'ayi ki karb'a?". Nace"Fad'amin in da zan sameka Sai nazo na amsa." Yace" Ba haka za'ayi ba, ke zaki kwatanta min in da kike nazo na kawo Miki, dama fita zan yi. A Wace unguwa kike?" Nace" Ina unguwar Doka"
Yace"Anya na tab'a Shiga unguwar nan?".
"Kai ba d'an garin zariya bane?". Nace da shi.
"Haifaffe ma kuwa." Yace da hanzari. Domin kana d'an gari ai baza'ace ko'Ina kaje ba. Amma dai zan zo, idan na shigo unguwar Sai na tab'aki a layin da kika kira kiyi min jagora, kar na manta. Tare da a bokina suhail zamu zo, tun da shi idon gari ne. Amma ki tanadi ladan tsuntuwafa. Kinsan yanzu ba'ayin aikin da babu in come." Ga zatona da gaske yake.
Nace"Babu damuwa, zan bada idan babu yawa.". Yace"Babu yawa ai. 'yar dubu goma ce Kawai zaki bayar."
Nace da sauri."Dubu goma kuma? Daga nan na barmaka wayar Mana Zai fi, tunda nasan ko Sai da ita za'ayi baza tayi dubu goma ba." Yayi Wata 'yar gajeriyar dariya da ta k'ayatar da ni. Kawai Ina jin a lokacin a cikin salo na raha yake sosai, domin barkwanci da raha basa cikin halayyar Fa'izu a sanina.
"O. K. bari idan nazo ma kashe Maganar." A binda yace Kenan ya datse Kiran kafin ma nayi.
*🏤 NI DA GIDANA 🏤*
*_Littafi na daya_*
*NA*
*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
📱6
_______ Nuriyya duk tana jin mu ni da fa'izu, saboda hand's free nasa . Bayan na kashe wayar tace" Kiji Mu da Mutum. Da har Ina yabon'sa Ina cewa ta fad'a hannun Mutumin kirki,a she duk gayyar tsiyar ce . A bashi dubu goma kamar tasa ce Zai bamu Mu Saya?"
Nace.
"Ke dai rabu da shi, yazo tukun, muga gudun ruwan'sa. Nace a hankali domin tausar'ta.
Cikin a binda baiga gaza rabin a waba, Sai gasu sun kafe babur a kusa da k'ofar gidan Mu da taimakon kwatancen da nayi musu a waya da suka shigo unguwar.
Muna tsaye dama a k'ofar gida nida Nuriyya. Samarin d'aya fari ne sosai, d'aya bak'i. Bak'in yafi sakin fuska da fara'a a garemu. Bayan musayar gaisuwa, farin saurayin ya zura hannu cikin aljihu ya zaro waya gami da ssbuwar caza ya Mik'o Mana. Ni na karb"a cike da godiya.
Yace
"Sai ki kula, karki sake yarwa, domin ba lallaine ta dawo ba."
Nuriyya tace da sauri.
"Gaskiyane Kam, domin ba domin mun yi dace da mutanen kirki irin Ku ba, ai da tarasa kenan. Kuna da kirki da karimci gaskiya, don Allah Yaya Sunayen Ku?" Ni Kam naga Zak'ewarta, shi yasa nayi kasak'e ina kallon'ta.
Wannan saurayin bak'in ,shi ya bata amsa.
"Sunana Suhail labaran. Shi kuma sunan sa Fa'izu Bukar.
"Kai Amma Sunayen Naku da dad'i, kamar na larabawa? A Wace unguwa kuke ne.?" Nan naga mai suna Fa'iz d'in ya jefeta da wani irin kallo a sakarce, dake nunin ta isheshi da Surutu. Ni kuwa dama tuni ta k'ular dani na irin wannan shishshigi. Su ya dace su nememu da hakan, ba suyi ba, Sai Mu mata? Domin Kawai ta zubar Mana da daraja?.
Tuni dama na fuskanci wannan Fa'izun d'an ji da kaine da fad'in rai. Tun daga Maganar farko bai sake cewa komai ba. Ko kallon Mu bai sake yi ba, Sai da Nuriyya ta Shiga k'wak'ulen tambaya ga a bokin'sa ya waigeta sau d'aya, kallo ma na raini.
"Zo Mu tafi Suhail, kasan sauri muke yi, kuma ba jiran Mu zasu yi ba.Inji Fa'izun. Inda ya ce masa "To" Amma bai motsaba, saboda Nuriyya da ya soma yiwa kwatancen in da suke dalla, dalla. Bai yi nisan ma da zata gane sosai ba Fa'izun ya sake cewa.
"Idan ba zaka zo Mu tafi ba, ni kaga tafiyata. Bazan jiraka ba wallahi idan ka tsaya, ka taho daga baya." Ya dubeni yace.
"Sai anjima."
Nace"Na gode, Allah ya saka da khairan."
"Amin." Yace bayan ya soma tafiya.
Ganin haka Shima Suhail d'in yayi gaggawar binsa saboda ya fuskanci tafiya Zai yi ya barshi, bayan babur guda suka zo kuma. Bai k'arasa yiwa Nuriyya kwatance ba dai ya tafi.
"Gayun nan sunyi a rayuwa. Musamman ma farin, Fa"iz.Sai dai naga d'an girman kaine da nuna isa , d'an hana ruwa kuma.Abokin'sa ya fishi kirki. Yanason a k'ulla zumunci ya hana.Ya bani haushi fa!".
Nace"Naji dad'in Abinda yayi Miki, haka Kawai daga had'uwar k'addara Sai ki Zak'alk'ale? Wannan halin zub da ajine Nuriyya. Nayi mata tatas, tayi lub. An fa an d'auki lokaci in dai mun had'u Sai tatada Zancen Wai taji ciwon rabuwar Mu da su babu a direshi.
Rannan kuma muna hira tacemin.
"Kinsan me Zuciyata ta ayyanomin yanzu.?"
"Ta Ina zan Sani,baki fad'iba." Nace da ita.
Tace"Zuciyata ke sak'amin, Ina ma Ina cikin tafiya, na had'u da miskilin gayen nan, ai ko bai kulani ba naci riba."
Nace.
"Kin Shiga uku Nuriyya."
Tace"A wani dalilin zaki kiramin masifa?"
Nace a harzuk'e.
"Ai duk a binda Zai damu bawa, musiface, musamman ka kafa rai da a. binda ka tabbatar baza ka samu ba, ko a binda bashi da amfani a gareka. Kin dameni Wallahi da Zancen samarin nan. Wanda kike so d'in kuma Sam ba kya gaban'sa. Idan ba mantawa kikayi ba kina sane, kina ganin yarda ya nuna a garemu. Dama d'ayan kikewa Sai nace d'an dama dama. Kinfi ni sanin ma ruwa ba'sa'an kwando bane. Karki sake yi min Zancen su na gaji."
Tun daga lokacin, na samu lafiya ta daina yi min Zancen. Amma Bansan cikin Zuciyarta ba ko tana sak'awa.
A daren ranar dai Alhaji Rabi'u yazo ya matsamin lamba na Sai na bashi dama ya turo iyayen'sa Yasan matsayin'sa. Sayayya fal yayi min kuma. Yace ya kuma gaji, ko yin ko bari yana son Sani. Nace ya bari, zanyi magana da kawuna.
Kafin ma na fad'awa Kawu Sulaiman, da Nuriyya k'awata tazo, ta rikirkita min lissafi.
"Wallahi ni nafi Miki Sha'awar Alhaji Rabi'u, bawai domin yafi Usman kud'I ba. Alhaji Rabi'u yafi Usman shekaru da gwagwarmayar sanin wahalar aure da juriya da sanin darajar iyali. Kefa kika ce zaune yake da matarsa lafiya, gashi kince yana yabon matar Sama. Mai wannan ai Sai namiji na gari. Shi kuwa Usman baki da misali a kansa da zaki samu tabbas, Sai kin Shiga zaki gani. Kuma kin tab'a cemin kin tsani kiyi aure ki fito a rayuwarki, ba kyason zawarci ko aure sau biyu. Tun da haka ne, dole kiyi taka tsantsan wurin aure, kar Kibi son zuciya. Tun da su duka sun yarda da karatunki da aiki da zakiyi to kar kibar Alhaji Rabi'u, shi ya dace dake. Kinsan maza irin su manya suka auri budurwa, ba k'aramin tarairayarta suke ba da nuna mata soyayya."
Na Shiga rud"ani, domin cikin maganganun'ta a Kwai a bin dubawa ko ba duka gaba. Bata gushe da yi min hud'uba ba, Sai da ta cusamin auren Alhaji Rabi'u, naji shid'in Kawai zan aura. Shi yasa banji fargabar sake tunkarar Kawu Sulaiman da Zancen ba, duk da nafa kaimasa Zancen Usman yace na saurare shi. Idona ya rufe.
dubana yayi cikin 'yar fusata.
"Wai ke Sumayya me kike nufine? Maza biyu kike so ki aura, ko menene k'udurin'ki?"
Na duk'ar da kai zan soma magana ya katse.
"Fad'amin wakike so da Gaskiya,Alhaji Rabi'u ko Usmanu?".
"Alhaji Rabi'u." Nace.
Jinayi gaba d'aya ya k'aryatani.
"K'arya kike yi, Shima ba son'sa kike yi ba."
Ni kuwa nace me zanyi, idan ba kallon'sa ba.
"Tun da kika tsaya ruwan idanu tsakanin Alhaji Rabi'u da usman, ya nuna su duka ba wani so na hak'ika kike musu ba. So guda d'aya ne tak! Kuma ba'a yin ruwan ido a cikin'sa. Da kina son Usman, ba zaki dawo daga baya kice Alhaji Rabi'u kike so ba. Kuma da Alhaji Rabi'u kike so, tun farko shi zaki zab'a. Nafi zargin cusa miki ra'ayin'sa a kayi.
Ya sauke numfashi a hankali, ya dubeni.
"Bazaki auri d'aya daga cikin'suba, domin duk basu dace dake ba. Wanda ya dace dake a dabi'ance zai zo nan kurkusa in Sha'Allah. Zaizo, kuma kafin yazo zaki ga alama ta sanarwa ko nuni na hannunka mai sanda, ke dai sa idanu."
Cike da Mamaki na dubi Kawu, amma kaina ya d'aure ban fassaro komai ba, a fuskarsa ko a kalamun'sa.
"Zan sallami Usman da Alhaji Rabi'u da kaina. Babu ke babu su, ko a hanya, kinji na fad'a Miki. Na sake jadda da Miki, ko ki yarda ko karki yarda basu dace dake ba. Bayan ba son'su kike ba, kuma bani da garanti a kan'su. A ido Kawai nake ganin'su, tunda babu Wata huld'a da take Shiga tsakanina da su. Ina so ki darje Miji Sumayya ko domin maraicinki kinji."