Sashe 6
Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwana biyu tsakani da yamma Lis, ina zaune tsakar gida, Kawu sulaiman ya shigo, nayi masa sannu da zuwa, haka ma baba Talatu. Yayi mata sannu da gida. Ya dubeni yace"Sumayya yau Ina tare da Yarima, yace a gaisheki."
Nace"Ina amsawa." Ya wuce yana yin wani murmushi da bansan musabbabin'sa ba. Ni dai nasan babu yarda za'ayi wallahi Fa'izu yace a gaisheni. Mutumin dake bala'in jida kan,sa. Ta Ina ma ya tuna da sumayya, a rayuwa? Shekaru uku fa Kenan da watanni rabona da gama makaranta. Kawai bazan iya k'aryata kawuna bane. Washe garima da Kawu Zai fita Sai yace min.
"Sumayya yau ma zamu had'u da Yarima da k'arfe uku na rana a club, me zance wa Yarima?"
Nace"Bani da a binda zance masa Kawu."
Yace"Kikayi haka baki kyauta ba, Amma shi yace a gaisheki? Amma zan ari bakin'ki naci Miki albasa." Ni dai ban tofa ba. A yar tambaya ce ta soma tsayamin a rai name kawuna yake nufi da son had'a a lak'ata da malam Fa'izu? anya babu wani b'oyayyan al'amari a zuciyar'sa? Ture komai gefe Kawai nayi. Na Shiga dakon jiran'sa ma na ya dawo nayi masa zancen d'an fodiyo, domin ya matsamin da Sai ya turo iyayen'sa a satin.
*🏤 NI DA GIDANA 🏤*
*_Littafi na daya_*
*NA*
*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
📱5
_______ Usman yazo zance wurina, gaisawa Kawai mu kayi, kafin ma muyi nisa da magana, Sai ga Kawu Sulaiman ya dawo. Yana shigowa farfajiyar gidan, Usman ya rusuna ya gaisheshi, cikin tsantsar ladabi. Ni kuma nayi masa sannu da zuwa. Yace
"Sumayya zo na ganki na 'yan mintina. Nace"To, gami da Mik'ewa. Ya kuma waiwayi Usman yace.
"Usman, kad'anyi hak'uri na katse muku hira, yanzu zata dawo."
Ya nuna har a fuska babu komai. Hanyar fita waje yayi, na bishi. Kafin Mu isa ga k'ofar fita yace."Sumayya, Yarima na kawo Miki Ku gaisa. Daga meeting muke na wasan k'wallo da zamu buga da k'ungiyar 'yan boll ta Dolfin, very soon. Shi ya kawoni gida ma a babur d'in'sa, Kinsan nawa ya samu matsala. Sai nace to why not bazaku gaisa ba, ko kuwa.?" Murmushi nayi nace "To, Ancle."
Kawai Samun kaina nayi da fargabar had'uwata da Fa'izu. Gabana ya rink'a fad'uwa ma, Yayin da na tuno d'abiun'sa na cin zarafi da fushi ko yaya aka kuskuroshi. Ban manta komai ba. Shi yasa nake ganin komai ma kamar lokacin da yana koyar damu, kamar zan yi masa kuskure yaci zarafina.
A k'ofar gidan Mak'ocin Mu Alhaji Bilyanu muka sameshi ya jingina jikin sabon Jan babur daya kasance nasa. Hasken fitilar k'erarren gidan mai haske komai ya haskemin shi sosai. Saye yake da Kayan 'yan boll koraye, Amma wandon dogone tissue. Ban tab'a ganin Mutumin da Kayan 'yan boll suka yi masifar yi masa kyau ba, irin Fa'izu. Domin sun k'ara haskaka shi ma. Wani kyau naga ya k'ara da haske da 'yar k'iba ma kad'an, da ta k'ara yi masa kyau fiye da da. Ko har yanzu yana Koyarwar? Kaina na tambaya.
Na rusuna na gaisheshi. Ya k'ara d'aga idanu ya dubeni sosai bayan ya amsa. Ya janye daga jikin babur d'in da yake jingine a jikin'sa ya dubi kuma Kawu sulaiman. Kawu Sulaiman kuwa tsare Mu yayi da kallo ni da fa'izu ya kalleni ya kalleshI, hak'oran sa waje cike da nishad'i da bansan dalili ba. Fa'iz ya dubi Kawu na.
"Kasan Sai yanzu na ganeta Sulaiman? ai da ban fahimci Wacce kake ta kwatantamin ba, saboda d'aliban da yawa ,ko na Santa, ko sunan'ta iyanzu mantawa zan yi, an fa jima da yawa. Na manta sunan ta dai, amma na ganeta a ido. Sanin monita nayi mata na Class 6 B ko?.Tabbas baka da mantuwa Malam Fa'izu. Zuciya ta ta kimsamin.
Na gyad'a kai, Sannan na kai dubana ga Kawu Sulaiman, na kuma dire kan Yariman nasa . Carab Sai muka had'a idanu kuwa. Sai yayi murmushi ya maida kallon'sa ga Kawu Sulaiman. Zan iya cewa shine farko da nata b'a ganin murmushin Fa'izu gareni, a iya sanin da nayi masa. Cikin tausasa murya yace.
"Sumayya, ai ban tab'a sanin ke Jinin Sulaiman bace. Da nasan hakan, Atleast ai da kinsamu kulawa irin Wacce ta dace. A Kwai a minci da girmamawa tsakanina da Ancle d'inki. He mean so much to me. Ina ganin k'imar'sa da shi kan'sa baisan iya feeling d'ina ba game da hakan. Nima yanzu Ancle d'inki ne Sumayya kinji ko?"
Na sunne kai k'as cikin murmushi nace"To".
Ya maida hankalin'sa kan Kawu Sulaiman kuma.
"My man, Ina cikin sprising fa yarda k'addara take ta had'ani da wannan Daughter taka, bayan mun rabu. Sau uku Kenan fa. Three times Sulaiman. Ya nuna yatsun'sa uku yana nuni da shi.
Ni Kam sak'e sak'ena nake, Ina ganin kamar a majigi komai ke faruwa. Malam Fa'iz ke tausasa harshe yana fad'amin wad'annan kalaman? Dama ya iya tausasan kalamai a she?
Kawu Sulaiman ya duba yana mai cewa.
"Farko ta yarda wayar'ta na tsinta, ta kira layin mu kayi magana ta kwatan'ta min gidan nan na kawo mata. Kasan ban tab'a zuwa gidan nan ba Sai yau ai da tun a ranar na d'au haske, domin Sai yanzu komai ya dawo min. Tabbas nan gidan nazo na kawo mata waya. Bayan watanni mun sake had'uwa da Sumayya a makaranta nayi teaching d'inta, Kenan a malamin ta nazo. Yanzu kuma Bayan shekaru uku mun sake had'uwa da ita ta dalilin ka. Me hakan ke nufi Sulaiman, da sanadi ke ta had'ani da 'yarka"? Murmushi Ancle d'ina yayi yace.
"Da walakin goro a miya. Kuma ruwa baya tsami banza. Idan kaji gudu kuma to da magana.
Fa'izu baice wa kawuna komai ba, game da furucin da yayi, face dubana da ya sake yi yace." Karatu kike yi ne Sumayya?"
Nace"Eh".
"Da kyau, kin birgeni. Ki daure ki zurfafa karatu, kici moriyar sa tun da kIna da k'wak'walwar fahimta. Ina yi miki fatan alkhairi da nasara."
"Na gode Ancle." Na fad'a cikin wani nishad'i da naji ya bak'unci zuciya tashi guda. Gani nake tamkar ba Fa'izun da na Sani bane. Wannan yafi wancan kyawun Siffa ma da ake ta kwarorato, kuma halinsa ya canza wurin sanyi da sauk'in kai. Amma dai tabbas shine, tun da gashi mun tuna baya ma. Albarkacin Kawu Sulaiman naci. Zuciyata ce ta fad'amin.
Fa'izu yace da Kawu na."Zan tafi Sulaiman dare ya soma, don Allah goben ka fito da wuri, a yi training, kasan wannan wasan na farko ne sai mun nuna k'wazo fa."
Cikin 'yar dariya Kawu na yace" Babu ji Yarima. ai bamu da fargaba, tun da muna da champion irin'ka."
"Kaji ka da wani zance. Ni kad'ai ne zanji da komai? Wato dani kuka dogara a nasarar Ku ko?to kuwa Wallahi zan kayar daku Ina sane."
"Tuba muke Yarima, mun tuba mun bika, ayi afuwa. Yarda Kawu Sulaiman ke kwantar da kai, shi kuma Fa'izu ya Sha mur serious babu kafar Zai sauko, Sai dariya taso ta subcemin na kanne. Yana nan dai bai canza ba. Nace a raina. Nan dai na bar'su ni na koma wurin Usman.
"Dan fodiyo, na jima ko? A yi hak'uri." Nace
Yace"Gimbiya ai bata laifi. Yaya kuka yi da Yaya Sulaiman don Allah. Ina cikin fargaba."
Nace"Karka damu, yace nan da Jibi idan yayi magana da kakanni na zai yi Maka magana.
Dad'i ya kasheshi a ranar, gani yake kamar yayi nasara. Ni kuwa tuni na fahimci Kawu na kamar bayason magana ta da Usman. Kai ban ma fahimci alk'iblar sa ba ma. Kamar bayason nayi aure a kusa ma, Sai nayi ilimi mai zurfi, amma fa zato nane. Koma hakan ne, nima burina ne dai. Amma Usman ne yake ban tausayi haka nan.
Da daddare an kawo wuta, na d'auko caza ta zan saka wayata a caji, inda Kawai Sai Ancle Fa'izu ya fad'omin a rai. Saboda shi ya had'omin da cazar, Sanda ya kawo min wayata da ya tsinta. gashi kuma a ranar yazo gidan namu.
Zuciyata keta haskomin duk wasu a bubuwa na Fa'izu da suka wanzu tsakanina da shi. Na rasa kuma dalilin da hakan ya zauna min kuma a rai. Murmushin da yayi min da muka had'a idanu, yak'i sharewa daga cikin k'wak'walwa ta, duk da na tabbatar babu Wata manufa a zuciyar'sa game da hakan.
Nayi kwance al'amarin farkon had'uwata da shi ya dawomin a hankali. Ga yarda a bin ya faru a tak'aice.
Gidan k'anwar kakata naje Wata asabar gidan Hajiya mariya, Wacce ita ta fara rainona bayan mutuwar mahaifiyata, kafin baba na ya rasu Shima. Bansan na yarda wayata bama, Sai da nazo gida, Ina kici kicin zaro canjin kud'ina zan yi aike, ga yaron aiken kuwa tsaye a gabana. To babu kud'I kuma babu wayar a babban zip d'in jakar, da bansan lokacin da suka zube bama. Dama jakar ta d'an farke Sai gani nayi ta yage ma sosai a she ban Sani ba. Nan nasan na rasa wayata a karo na biyu, domin ko Wata biyu batayi da saye ba da kawuna ya sayamun Sabuwa bayan an sace waccan. Kuma mai tsada ce a kan waccan. Damuwa ta tayi nisa, a raina a ranar, saboda kar Kawu Sulaiman yace Ina da sakaci da rashin kulawa a kan abinda yasa k'ud'i ya saimin. Waccan an sace, wannan kuma nayar? ai bazai ji mutuwar sarki a bakina ba kuma. Ba kina naja na tsuke. Amna fa kullum a farga ba nake, kar ya ne mini a waya ya fahimci komai. Kwanaki hud'u tsakani Sai ga Wata a miniyata mai suna Nuriyya.Muna hira nake fad'a mata b'atan wayata. Ta jajanta min. Nace"Bani a ron wayarki ma na kira layin, duk da ban saka rai bama. Duniyar yanzu ba gaskiya. Masu tsoron cin haram ko rik'e haram, sun yi K'aranci. Da kud'i a wayar taki?" Tace. "Kinfi kowa sanin wayata kullum cikin credit take, Bata zama fanko, saboda Ina da masu yi mata hidima." Na warce wayar Ina cewa.
"Allah ya shiryeki Nuriyya. Kullum baki da aiki Sai tatse samari, kuma ba'auran su zakiyi ba, Wallahi kiyi hattara.