Sashe 5
Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni d'in marainiyace ta gaskiyar, tun da ban bud'i idanu da iyaye na ba duk sun rasu Ina yarinya sosai. Bayan nan kuma nazo na rasa kakata Hajara ita ma data rungumi maraicina da kyau, take nunamin k'auna muraran. Sai da ta shekara da rasuwa jakana yayi aure, kuma Saboda ni. Saboda babu yarda za'ayi ya zauna dani babu mace.
Naga mutuwa a rayuwa ta Kam. Amma Sai a tara masu iyaye Sama da d'ari ba'a samu mai Samun kulawa da tattalin k'auna iri na ba. Dangin mahaifiyata Khadija suna son mamana sosai, shi yasa bayan rasuwarta Soyayyar ta dawo kaina. Haka ma kawuna Sulaiman Soyayyar dake tsakanin sa da yayarsa mamana da bata da bazata fad'uba, kaina ya tattarota bayan rasuwarta. Su biyu ne tal wurin iyayen su, kuma a Kwai k'auna da fahimta mai zurfi tsakanin su. Wannan dalili yasa Kawu yake mugun Sona da tausayina. Motsi kad'an Yana bibiyar me nake ciki. Kome ya samu ni Zai kawowa. Tun da ya gama digree babu aiki ya Shiga buge bugen aikin Samun k'ud'i na k'arfi, daga wannan zuwa wannan, duk saboda ni. Ma'abocin son K'wallon k'afa ne sosai. Suna da Club babba ma na matasa irin sa. Suna buga mach kurfa kurfa na state state bayan na garin su idan an gayyace su. Yama fi Samun kud'i tanan babu laifi. Amma lokacin daya ke bawa boll dabam, lokacin buge bugen sana'oin sa ma na kafi zuru da bam. Yayi rini, yayi Aikin gini, yayi aikin electric, har aikin fenti ya iya, idan an kirashi zai b'adda bami yasa Kayan aikin yaje yayi ya karb'i kud'in'sa. Mai k'wazon neman na kaine Kawu Sulaiman,bashi da girman kai Sam. Kuma duk sana'ar da yaji ana Samun kud'i zai koya, ba tare da raina taba. Shi yasa baya rabo da'yan kud'ad'e. Bamu da shi, sai na rufin a siri saboda kakana ma a zaune yake ba kullum yake fita ba, da harkar Sai da turare ta karye masa. Da kanti ne da shi guda na saida turarurruka, yanayin rayuwa komai yaja baya. Kawu sulaiman ne ke k'ok'arin a bubuwa da yawa. kuma rayuwar mu babu fallasa, komai a Siri a rufe ruf.'Yan Kayan k'walam na motsa baki ma Kawu na kan sayo lokaci lokaci. Ban rasa kuma 'yan Kayan ado irin na 'yammata ba, Kawu sulaiman yana fito dani kunya, ko ban furta ba Zai sayo dai dai ikon sa. Ya kuma ban k'ud'i ko zan buk'aci wani a bu. Ya wanke min duk wani hawayen maraici, saboda ubana talaka ne sosai, bai barmin komai na gado bama. Ko gidan da suke zaune da mahaifiyata ma na hayane, kuma biya masa ake yi. Tun mahaifiyata tana raye Kawu na yake nunamin Wata irin kulawa da soyayya, da Ina yarinya naji daga kakata, bawai Sai data rasu ba. Domin da ta rasun ninkawa kuma yayi.Ya kusa zautuwa ma da mamana ta rasu saboda kusancin sa da ita da k'auna. Kakana ma da matar sa kulawa da k'auna suna bani iyayin'su, saboda maraici hawan hawa da na samu kaina a ciki.
Ina da ra'ayin son ci gaba da karatu, shi yasa ma aure baya gabana, ko kula da Sha'anin samari, tun kafin na kammala secondry. Duk da haka dai Ina da samari biyu da nake sauraren su Sama Sama. A Kwai Alhaji Rabi'u magidanci mai mata da yara. Yana da sukunin sa kuma yanayi min 'yan hidindimu. Yana da mota da yake zuwa wurina ma. Sai usman shi kuma saurayi ne, tela ne na aikin surfani. Hankalina ya d'an fi kwanciya da Usman saboda shi saurayi ne dai dai dani. Ina tsoron fad'awa tsakiyar ma'aurata. A nawa ra'ayin gwara tazo ta sameni. Amma shi Alhaji Rabi'u kullum Zancen'sa na bashi dama ya fito, amma bana bashi had'in kai. Shima Usman ya damu da azo a yi wani a bu, Shima d'in ni nake bashi matsala. Ina son na samu ilimi sosai nayi aiki na rink'a tallafawa Kawu da kakannina.Wannan shine burin sumayya a b'oye.
Kwanci tashi jarrabawar Mu ta fito na samu sakamako mai kyau k'warai. Shi yasa direct jami'a,suka amsheni.
Kawu yayi ta samin albarka. Sosai yayi farin ciki, har kyauta yace Zai min. K'awaye nama duk sunci da kan mu yake a had'e. Saboda halayyar Mu guda ce ta son karatu. Amma nafi su Maki dai.
Kawu sulaiman yayi min nasiha sosai da shawarwari, wurin tafiyar da rayuwata ta jami'a. Yaja kunne na sosai a kan kar nayi Mu' a mala da k'awayen banza da samari. K'arshe yace.
"Na baki dama, don Allah kar ki bani kunya Sumayya, kija mutuncin ki, kiyi a binda ya kai ki Kawai, wato karatu."
Nace" Kar kaji komai, Ancle, zan kiyaye, ka ta yani da addu'a."
To ban bashi kunyar ba kuwa. A shekarata ta biyu a jami'a ya dad'a sakin ransa sosai saboda yarda yaga komai nawa yana tafiya dai dai, Sai ma k'arin ci gaba. Na k'ara nutsuwa wurin kula da tattalin kaina. Na k'ara sanin darajar kaina sanadin k'yamatar wasu a bubuwa da nake gani. Na k'ara kyau na gogewa da Wayewa kuma. Ba fara bace ni, Amma za'a iya Sani a layin farare idan sunyi k'aranci. Saboda kulawa da kaina da nake sosai, fatata Sai ta k'ara gogewa ta haskaka sanadin gyara. Kawu lokacin Samun'sa ya k'aru, ya kuma Saki Samun'sa sosai a kaina ma a lokacin. Burin sa Kawai Sumayya ta zama a bar kwatance da alfahari. A tsukin kuma Usman da nake cewa Dan fodiyo, ya matsa lamba Sai na barshi ya turo manyan'sa. Ga a binda yace da nak'i yarda.
"Sumayya, don Allah ki rufamin a Siri nasan Matsayina. A farga ba nake tsindim na zaki iya kub'cemin. A komai kin canza kin samu haskakar da za'a k'yalla idanu a kan'ki a kawo miki hari. Babban a binda nafi kwad'ayi a kan'ki shine kamun kan'ki da nutsuwa da tarbiyya. A Ina kike tunanin zan lalubo irin'ki idan na rasa ki.? Tabbas zan Shiga tasku idan na rasa ki. Ina sonki Sumayya fiye da tunaninki, don Allah kar kiyi min wasa da hankali. Ni dai na fito a San dani nasa rai ma. Aure zan jiraki zuwa lokacin da kika shirya."
Sam aure baya raina a lokacin, ko fidda ma gwani. Tausayin Usman shi yayi rinjaye a raina, bawai son'sa ko son auren'sa. Na a mince amma ya bani kwana biyu nayi magana da Kawu na. Yayi ta murna kuwa.
Ranar da mukayi zan fad'awa Kawu Sulaiman, Usman zai zo yaji inda a ka kwana, ranar Kawu na ya tashi da gyare gyaren d'akin'sa, saboda ranar lahadice baya fita Sai yamma, ni kuma bani da lacture.
Na Shiga taya shi, saboda gyaran da yawa. Kusan yayi d'ai d'ai da komai na cikin d'akin. gyare gyare da goge gogen da yawa. Na kafe Sai ya barmin nayi ni kad'ai. Ya saduda ya tafi ya barmin.
Da yake Ina da saurin aiki, Sai gashi na gama. Ina mai da komai muhallin'sa naci karo da Wata farar ambulan 'yar babba. Ko Ancle Sulaiman ya sanni da lafiyar bincIke.kamar nawa na Shiga k'ok'arin bud'ewa, domin naga menene a ciki. Amma a tsorace nake kar ya shigo ya ganni, yace mai hali kin soma ko? Domin na saba da wannan kalma tun Ina yarinya.
Tuni na fahimci hotuna ne, da sauri na shiga zaro su, duk zatona hotunan budurwar sace da ban tab'aji da gani ba.
A bin takaici a gareni, hotunan maza na gani, saye da Kayan 'yan boll har dashi. Wani Mutum uku wani Mutum biyu wani shida. A Kwai kuma Wanda suka had'u su duka suka sa boll d'in a tsakiya shida 'yan club d'in nasu. Amma menene yaja hankalina na kasa a jiye hotunan kamar yarda naso da fari, da naga ba hoton mace bane?
Mutumin da na yanke zaton zan sake gani a rayuwata, Mutumin da nasan babu wani dalili na sake had'uwata da shi, shine a cikin hotunan 'Yan club d'in su Kawu Sulaiman. FA'IZ BUKAR.
Na sake kai ganina ga hoton, amma bisa ga Wanda ya d'au hankalina da ganin'sa wato Fa'iz. Gaba d'aya ya haske hotunan. Kowanne da ka kalla, shi zai fara janye kallonka. Muryar Kawu Sulaiman naji a tsakar kaina.
"Me hali baya fasa hali dai. Bincike kike min ko gyara sumayya?" Nace. Yi hak'uri my Ancle. Wani malamin Mu na secondry na gani shi yasa na tsaya dubawa ma, dama kasanshi?" Na nuna masa shi. Ya duba yace. "Au, Yarima kike nufi?"
Na sake nuna masa shi, ga zatona bai kulaba.
"Ka ganshi fa, wannan farin na cikin Ku, malam Fa'izu fa."
Yace"shi d'in nima nake nufi ai , sunan'sa Fa'izu, amma Mu a bokan'sa Yarima muke ce masa. Mu kance masa kuma Gimba, wato d'an sarki, a hausance Kenan. Amma mun fi Kiran'sa da Yarima, Shima d'an sarki Kenan, Amma a yaren barbarci ne, saboda usulin Mahaifin'sa babarbare ne, mahaifiyarsa kuma k'abilar shuwa a rab ce.
Na dubi Kawu saroro. "Me yasa kuke ce masa Yarima Ancle.?"
Murmushi yayi ya karb'i hoton."Abokai suka sa masa kuma ya bishi. Baki ga takunsa yayi kama da na masu wannan sunan ba kema?"
Nayi gajeriyar dariya.
"Tabbas na harbo jirgin Kam, sunan ya dace da shi sosai, kun iya sa sunan a muhallin'sa. Ai yayi dealing sosai a school d'in Mu. Bana zaton a Kwai d'alibar da zata mance dashi. Sunayen ma da za'a kirashi da shi suna da yawa. Dama d'an club d'inku ne Ancle?"
"Sosai, a harkar boll kuma muka had'u muka saba. Shekara shida Kenan da ya shigo club d'in Mu na Kaduna united. Ya iya boll fiye da zaton mai zato, da shi muke ji a club. Ko jiya na had"u da shi da yamma a club, mun Sha hira a kan gasar Wata boll da muka je. A Kwai mutunci tsakani na dashi, duk da babu Wata a bota dai sosai tsakanin Mu, Sai mutunci sanadin club tare da buga k'wallo. hirar ta datse ne saboda baba Talatu da take kirana. A ranar dai da Usman Dan fodiyo yazo hak'uri na bashi, nace ya k'ara min kwana biyu dai. Mantawa nayi ban yi Maganar da kawuna bama.