Sashe 2
Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yabar a bin fad'a Kam da k'orafi. Saboda baki d'ayan makarantar, babu a jin da malamai ke tarairaya kuma a ke ji da su irin Mu. Bawai ga k'ok'ari ba, Sai dalilai biyu. ''ya'yan masu kud'i su suka cike fiye da rabin a jin. Sannan babu a jin da ya kai shi tsula tsula kuma kyawawan 'yan mata gagara gasa, daga kan farare zuwa bak'ake. Idan Mutum ya zagaye a jujuwan d'alibai ko'ina
Mutum Zai rantse tsince kyawawan 'yan mata a Kayi na makarantar a ka zube a a jin mu. Shi yasa yawancin malamai suna da wad'anda suke so cikin class d'in Mu. Shi yasa suyi ta tsiya ba'a yin komai na hukunci. Amma duk da haka a Kwai d'alibai tsirari a cikin a jin 'ya'yan talakawa, kuma wad'an da baza'a ce musu kyawawa ba, kuma baza'a kushe ba. Wato irin Mu, har dani.
Ni kad'aice ban tofa komai ba, a kan sabon teachear d'in namu. Wato Fa'izu Bukar. Takun'sa ni ya burgeni. Saboda ta hakan na tabbatar Zai yi maganin tsagerun d'alibai masu kuma nuna isar sunfi k'arfin komai. Kuma dole Zai kawo gyara da zakkarar da shagalallun d'alibai da dak'ik'ai. Saboda babu Wata alama ma da ya nuna na Wata yarinya ta isheshi kallo ballantana a ce ya k'yasa da har zata samu damar kawo masa lalata.
Fari ne sosai, da ganin Sama kasan cikin iyayen'sa a Kwai sirki.
Bayan farin fatar sa a goge take, irin gogewar da ba'a cika samu ba cikin Hausa Fulani. A gefunan fuskar sa a Kwai k'asumba da ta d'an feso, dake nunin yana da baiwarta askewa yake. Idanuwan'sa madaidaita ne, masu launin shud'i.idan haske yayi haske Kenan. Yana da dogon hanci sosai, da madaidaiciyar hab'a da k'asumbar sa ta zagayo ta kewaye ta, tayi masa wani irin kyau kuwa.
Babu a binda yafi komai yi masa kyau, irin turuwar girar sa bak'a da gashin kan'sa da suka d'ai sun isa bada shaidar irin jinsin da ya cakud'u da shi, ga Wanda yayi musu farin Sani. Wato (Shuwa). Madaidai cine a tsawo. Yana da diri irin Wanda mata suka fiso.mai cikar b'araza da gab'b'ai ,da fad'in k'irji. Bashi da rama Sam. Kuma bashi da k'iba sosai. Idanuwa bazasu tab'a k'osawa ba da kallon'sa, musamman mace. Kome take nema ga namiji, na dai surar kyau, to dole ta taka burki, idan tazo kan Fa'izu Bukar. Sai dai fa idan tana k'yamatar namiji Mara sakin fuska, mai jin kai da wulak'anci, tofa baza ta iya da shi ba Sai dai Hak'uri.
Cinnaka ba Sani babu sabo. Kirarin da naji d'alibai ke yi masa Kenan. Amma Sai da ya d'an jima a makarantar yaci sunan. Domin lokacin ne kowace d'aliba tasan wanene Fa'izu Bukar.
*🏤 NI DA GIDANA 🏤*
*_Littafi na daya_*
*NA*
*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
2
_________ A harkar jajircewa da karatu, da rashin sakin fuskar jawo wasa a karatu, sosai Fa'iz ya burgeni, saboda malamai da dama wasa suke shigarwa cikin karatun,su . Amma daga baya nima Sai na rink'a k'yamar wasu halayan Fa'iz Bukar. Bayan rashin sakin fuska kokad'an, a Kwai kuma iya cin zarafi ainun idan an b'ata masa. A Kwai shi kuma da d'agawa da jin kai, kamar d'an sarki.
Na kan had'u da shi a harabar makaran'ta, nayi niyyar gaishe shi, ko nuna sanayya, amma Sai ya wani d'auke kai ya kuma tsare gida. Wato kar ma na samu kafa. Jinkai dai wurin fa'iz ya shaddade. Ko mace wata dama idan tasan ta isa a komai, takan yi, amma shi namiji ai ya hak'ure. Wannan dalilai yasa naja baya. Idan na ganshi a gabas, to Sai nayi yamma ni.
Washe gari, period d'in sa tana Shiga, Sai gashi ya shigo. Ya ninka jiya a kyau Kam. Kayan da yasa, bayan haska shi da suka k'ara, sun yi masa kyau sosai. Ba kuma wasu Kaya bane na musamman. Kayan sanyi ne. Rigar sanyi ce mai duhu ruwan k'asa mai kwala, Sai wani gida gida a gaban rigar mai launin fari fari. Jin's d'in wandon daya sa, Shima ruwan k'asa ne, amma mai haske. Sai safar hannu, ruwan k'asa, safar k'afa ma haka. Komai dai to mach. Duk dai sanadin sanyin da a ke yi, yayi wannan shigar. Sanyin ranar yafi na kullum ma. Kayan da yasa jiya ma sun yi masa kyau, Amma na yau Kam ba'a magana. Ko daya ke, dole Kaya suyiwa Fa'izu kyau, ko wani iri. Amma fa ba kowa ne zai yarda ba, Sai Wanda ya ganshi.
Ya tsaya gaban a ji, ya dafa tebur d'in teacher, ya kallon d'alibai d'ai d'ai cikin jin kai da isa.
"Ina a ka kwana game da topic d'in da na karantar jiya, Kowacce ta fahimta?" Shiru babu Wacce tayi magana.
"Wata ta tashi tayi min bayani ko in brief."
Nan ma shiru.
"Any Quetion?" Nan ma babu Wacce ta d'aga hannu.
Ya gyad'a kai
"Cab'? Lallai yau jiki zai yi tsami. Kuna nufin wahalar banza nayi Kenan?"
Ga rashin sanin Fa'iz, yawanci an gane aikin sa. Kawai shiryawa a Kayi a nuna masa bai isa ba. Saboda yaci mutuncin d'alibai shalelen makaranta daga zuwa. Kuma ya nuna musu iyakar'su. Kuma intisar da ita ce zak'ak'uwa wa ta ma rasa kunya, ita ta tsara a nuna masa mun gagara, sunan da malam Abba ya Sama na. Ni dama bana cikin had'in kan. Shiru nayi naga na samu 'Yar uwa, Mu zama Mu biyu. ganin zai yi zaniya, nayi saurin d'aga hannu.
Daya ganni ya fara da yi min kallon kufula.
"Da kema kin iya kika saje da su? duk zan iya daku don k'aniyar'ku. Naku wasa ne Wallahi."
Da sauri na soma yi masa bayani cikin turanci, saboda banason a binda zai tab'a min lafiyar jiki. Ina tsoron duka sosai, tun ina k'arama.
Tambayoyi ya Shiga jeromin da turanci, uwa da 'ya'ya har da jikoki, duk domin na gaza amsa d'aya nima na fad'a tarkon'sa. Haka na fassara shi. Allah ya taimakeni na bashi amsa,saboda duk cikin class d'in babu Sama dani a kaifin basira, da haddace a bu. Ni nake d'aukar lambar farko duk jarrabawa ma.k'oK'arina ya haskakani, har na samu muk'ami.
Yace cikin watsomin kallon raini.
"Kinyi sa'a kin haye, kin tsallake hukunci na. Da kin gaza amsa tambaya d'aya da bazaki tsallake hukunci irin nasu ba. Amma zaki fad'o tarko na wataran, domin ban huce da ke ba.Saboda na kula Ku duka taron tsintsiya ne babu Shara,ba kusan ma me yakawo Ku makaranta ba. Shashashan Kawai, dak'ik'ai." Yau mun gamu da gamon'Mu. Haka na rink'a fad'i a zuci Kowa ya k'ara fusata da raina kan'sa fa ga wannan tahaliki. Bai d'auke Mu ma a bakin komai ba, face Shara, tun da aibata mun ma da yake shaida ne.
"Je ki kisamomin bulala babba a staff room, kuma ban yarda da babu ba." Yace dani. Na tashi zan fita Wata ta d'aga hannu Wai zata yi bayani. Yasakar mata kallon banza, Sannan yace
"Is too late"
Ta koma ta zauna ragwaf
Nayi sa'ar samo k'atuwar bulalar malam tukur. Nasan da ban samo ba, nima tawa ta sameni.
"Ten, Ten, lashes ta tabbata ga kowace yarinya. Ku fito one by one Kowacce ta k'arb'i tata. Na baKu damar da zan baku kun wofuntar, saboda baku da kirki, ban San me kuka d'auki kan, Ku ba. Ni kuma nasan kaina da darajar lokaci. Bazai yiyu na rink'a zuwa Ina aikin banza ba. Kullum Sai kun daku Wallahi, in dai baku canza ba. Zanga da bam bamci Ku da jaki ko babu. Tun da shine kullum cikin duka, amma baya canzawa.
Wata matsoraciyar duka irina farida ta soma bashi hak'uri tana hawaye.
Ai kuwa da sauri ya d'aga mata hannu.
"Yi min shiru ko bulalarki ta k'aru. Banace muku ni bansan kalmar hak'uri ba?"
Wai yau 'yan class d'in Mu za'a daka.? Ko tsawa bamu Sani ba. Kuma Wai bulala goma goma. Na tabbata yarda a jin ke cike da 'ya'yan gata'ya'yan so, wasu ko yatsa ba a'tab'a sa musu ba da sunan hukunci.
Intisar Ina kallon'ta taunar cingam take ma a binta, tana tab'e baki, Tana kallon fa'izu k'asa k'asa, saboda gani take tafi k'arfin nan. Duk cikin a jin babu kamarta a kyau, kuma babu Wanda ya kai Uban'ta kud'I. Malaman dake son'ta da yawa, shi yasa take tsula tsiyarta. Bata da kok'ari ko kusa, Amma Sai muga taci jarrabawa. Bata kallon kowa da gashi. Ta gasawa malami bak'ar magana kuma ta kwana lafiya.
Ita ta fara fitowa, kamar zuwa tayi a fara dukan takanta, Amma Sai ta tsaya daga d'an nesa ta dubi Malam Fa'iz tace.
"Sir, gaskiya bamu can can ci duka ba. K'aidar koyarwa, duka shine mataki na k'arshe. Kamata yayi Kayi ta mai mai ta Mana karatun, ko na Sati guda ne, har Mu fahimta. Kuma fa mu senior ne kar ka Manta. Duka ai Sai jenior."
Ina lura da kallon mamakin da yayi mata, tare da jin jina k'arfin zuciyar'ta da ta iya fad'a masa hakan. Rashin sanin intisar yasa yake mamakin. Bata da shayi, ga isa da alfaharin dukiyar uba da kanta. Shi yasa take ganin babu namijin da bazata taka ba, ta Sha ko da yake naga ta sassauta ma rashin kunyar tata a kan'sa ga yarda takewa malamai.
Yace da ita.
"Come here ". Ta isa gareshi yarda ya umarceta. Yace"Me kika ce?" Ta sake mai maita masa kuwa, har ma da 'yar dariya.
Ya fusata yace "Why are you laughing.?"
Mai makon ta bashi amsar dalilin dariyar, Sai ta sake yi ma. Wani irin mari ya kai mata, ba domin tayi saurin kaucewa ba, ranar da taga taurari.
Cikin harzuk'a yace.