← Book details Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 31

Sashe 14

Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun wawashe kyan na gado sun barshi da kad'an, Sai ya fito kuma bak'i. Amma daga baya da naga Mahaifin"su, Sai naga a she shi ya biyo sak"! Kamar ni Kenan.'Yan uwan mahaifiyata sun cemin Wai Mahaifina na biyo, Wai da na biyo mamata khadija, da Sai nafi haka kyau. Toni godiya na kewa mahaliccin halittar, domin nasan nafi wasu. Kuma babu mai dubana yace min mummuna. Ina nan a tsakiya. Idan ba'a yaba ba, to kuwa baza'a kushe ba.
Idan Mutum yana duban na k'asa da shi, to bazai yi butulci ba, domin Duniya kafi, a fika ne. Idan Mutum kullum na Sama dashi zai rink'a dubawa, to ba zai zama mai godiya da tawakkali ga ubangiji ba. Kuma ni ban yarda a Kwai mummuna ba. Sai mace taso zata zama mummuna, in dai tana la'akari da wasu da suka fita tana sarewa, tana k'ask'anta kan"ta, to baya zatayi tayi.idan mace ta yarda ita mai kyauce Itama, to kullum k'ara kyawun zatayi, domin zata kasance ne ko yaushe cikin yin a binda zai k'ara mata kyau.

Ra'ayin Sumayya ne.

Ni dai, tun da aka kawoni d'akina a ka watse, banyi tunanin komai ba Sai bacci. Kukan da na Sha, yasa b'arin kaina ya matsamin da ciwo, nasan babban maganin'sa irin na Kwan'ta nayi bacci. Sam banyi tunanin Wai na jira Ancle Fa'iz ba, ban sa rai da zan saka shi a idona ba.

Bani da bashin salla, har shafa'i da wuturi na sauke kayana. Tun da na Kwan'ta ban tashi farkawa ba, Sai uku da rabi na dare . Da Saura sallar a suba. Na jero addu'oi na fito rik'e da torch light mai haske, domin na kasa bacci kamar kullum. Fargaba da rashin sabo na sabuwar rayuwa. Kona koma bazan iya ba sosai saboda kar na makara a sallah. Na fito domin duba a gogon falo.Falon babu kowa wayam. Amma naga an rufe k'ofar falon da na sayo kad'an, an rufe sosai. Wannan shi ya bani tabbacin Ancle Fa'izu ya shigo, bayan nayi bacci.

Dab da sallar a suba na koma bacci na kamar mintina arba'in na farka, saboda ban saba bacci ba a lokacin. Falo na na fito, da nufin na je na d'auro alwala, domin anyi sallar a suba.

Sararo nayi, saboda ganin kuma Ancle Fa'iz kwance kan kujerata kamar mai bacci. Singlet ce a jikin'sa, ya rataye rigar Kayan' jikin hannun' kujerar. Na tabbatar bayan sallar a suba ya shigo, tun da d'azu k'arshen dare bangan shi ba, baya nan......😱
_______________________`_

Anyi mai wuyar, tun da
an shigo JIGON...... labari....Mu had'u a gaba Fan's😀.....

*🏤 NI DA GIDANA 🏤*

*_Littafi na daya_*

*NA*

*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

📱12
_______ Hannun'sa da yasa ya rufe fuskar'sa shi yasa na kasa tantance bacci yayi, ko idanun'sa biyu. Sai dai da nazo zan wuce na fita, Sai Jinayi yace "Ina zaki?" Idanun' nasa , dai a rufe yake da na juyo na kalleshi.
"Alwala zanje nayi" Nace.
Shiru yayi.

Bayan naje nayi alwala na dawo, na tarar kuma bayanan. Al'amarin' nasa Kam da d'aure kai.

Ya sake shigowa bayan gari, yayi haske sosai. Yana saye da rigar wandon shaddar da yasa d'azu, milk colour.
Dams Ina zaune a falin nayi zugum. Tunani kala kala sun lullub'eni.
Yace dani
"Ranki ya dad'e. Da ya shigo mukayi arba. Ban tab'a ganin'sa cikin nishad'i ba da walwala irin na ranar.
Nayi murmushi nace
"Ancle ai Sai ku wannan." Daga nan na rusuna na gaisheshi a ladabce.

Ya d'an nade rigar'sa ya zauna a kujerar dake gefen tawa, ya juyo yana kallona yace.
"Sumayya ake kika kika can,can'ta da a baki kambun sarauta guda. Irin wannan harkar Hutu haka? Tun jiya kika yi kwanciyarki da wuri, har na shigo baki Sani ba. Da a suba ma na shigo na k'wank'wasa jikin gadon'ki domin kiyi sallah, bakisan a nayi ba. Ni kuwa Ina na samu wannan hutun jin dad'in?

"Kai d'in dai kai ka dace da rik'e kambun sarauta Ancle. Ko a sunan da a ke kiranka da shi, an an yarda anbi. Yarima fa kake.!
Murmushi yayi, da ya k'ara masa wani sihirtaccen kyau, ya Saki Zancen, domin yaga nayi baki, har na fishi hujja.

"Kije Ku gaisa da Momi, domin muna gaisawa take Tambayata ke, Wai Yaya kika kwana, nace k'alau, Amma Kije taga zahir dai."
Naji sanyin dad'I da momin'sa ta soma damuwa da al'amarina. Nace"Yanzu Dama nake tunanin naje na gaishesu, ita da Abba, to ban Sani bane, ko sun tashi daga bacci, ko basu tashi ba."
Yace
"Ai mu nan gidan, in Dai muka tashi da a suba mukayi salla, to Bama komawa bacci. Idan ma a Kwai mai komawa baccin, to nine, kuma ba kullum ba nima, Sai San'da bani da uzurori da yawa. Amma Kije Ku gaisa da momin, shi Abba ya fita yau da wuri, Amma an jima Zai dawo.

Na dubeshi, cikin rausaya idanu.
"Ancle, Muje Kayi min jagora, kaji?"

Yace cikin bud'e min idanuwa
"Kina da larurar makan'ta?
Nace"Ko d'aya.

"Then, why kike so na jagoranceki?"

"Kunyar Momi, nake ji Allah."
Ya gyad'a kai "Kina da aiki a gaban'ki Yarinya. Amma fa bazamu jera ba Gaskiya, Sai dai ki bari nayi gaba, ki biyoni a baya."
Duk da bansan k'asadin'sa ba game da haka ba na hak'ura da hakan, saboda tuni na soma fahimtar'sa, Ancle Fa'iz, mutum ne shi da bashi karb'ar uzurin magiya ko roko, shi yasa ma ban soma ba.
Sai da na bada sa'oi tukun na bi bayan'sa

A harabar tsakar gida na had'u da Muhibbat Tana Shara, muka gaisa, amma dai banga sakin fuska sosai a wurinta ba.
Ita kuwa Khairat, Tana kichean Tana had'in Karin kumallo, domin k'amshin soye soyen'ta ma ya kauraye gidan.
Da yake, Ina d'an hangen'ta, duk da Bata hangoni ba, na k"arasa bakin k'ofar kichean d'in muka gaisa, nayi mata sannu da aiki cike da fara'a saboda naga fuska a wurinta. Da fara'a sosai ta amsa tace. "Yauwa Anti."
Yarinyar tashi d'Aya ta shigemin zuciya. Da alamu zatafi Muhibbat kyakykyawar Mu'Amala. Idan kuwa haka ne, Sai nace ta gama tako sa'a a matsayunta na 'ya mace. Domin kuwa ba k'aramar kyakykyawa bace Khairat. Kyau da hali, kuwa ai sai mai sa'a kan sa'a, d'ai d'ai Ku ke had'a duka.
A zaune dirshan na samu Ancle Fa'iz a falon Momi, kuma a gaban momi, yana shan tea. Duk da jin shigowa ta, bai cira kai ya dubeni ba, face momin da ta zubamin idanu, Tana k'aremin kallo a hankali. Ban kuma yi Mamaki ba, saboda jiya da a ka kawoni wurinta da daddare fusKata a lullub'e take har muka baro wurinta. Yanzu ne Kenan zata k"aremin kallo sosai.

Bayan na zube na gaisheta tace "Sumayya, yau kin wayi gari, a sabon wuri, Yaya a kaji da kewa?"
Kaina sunkuye cikin ladab nace "Momi AI bani jin sauyin komai, tunda Ina tare daku, kamar Ina gida ne.Ku iyayena ne, su khairat kuma 'yan uwa nane.

Na lura furucina ya faranta mata, a fuskarta na Karan'ta. Momi da Ancle Fa'iz suna kama sosai, har kalar fatar fara tas, mai sofanen jajaja, da kuma k'wayar idanun mai haske da yawa, da har yake bada launin shud'I shud'I. Duk da shekaru, sun d'an hauta kasan ta zuba kyau na lokacin k'uruciya, domin kuwa har yanzun Yana nan, sauyin kad'an ne, na turawar shekaru. Tabbas barewa bazata tab'ayin gudu ba, d'anta yayi rarrafe. Momi ta kalli Ancle Fa'iz da yake karyawa a nutse, tace

"Sumayya ga karin kumallonku can Khairat zata kai muku, kuma ga mijinki yazo ya dirarwa nawa, ai Sai ki matso Ku cinye Kawai tare, Khairat ta k'aro muku"
Kunya naji ta kamani, domin bazan iya wannan aiki ba gaban Momi. gashi kuma bazan iya bijirewa umarnin'ta ba.
Ancle Fa'izu kub'utar dani yayi da yace.

"A'a Momi, wannan ai yama k'are, ko bai k'are ba, gwara a kawo mata nata. Ni yau girkin ma na khairat, maleji nake yi da shi, duk ta cika magi. Can Yana cikin ci yayi saurun furzar da wainar k'wai.
"Magi, na tauna Momi, me ya samu Khairat haka?".
Momi ta dubeni tayi 'yar dariya.
"Sai kinyi kamar kina yi Sumayya, domin kin had'u da Miji mai tsirfa da k'orafi, ko Yaya aka kuskure. Ni na faraci kafin shi aMMA banji wani magi ba. Gishiri ne ya fito d'an kad'an. Kuma baiyi yawan da za'a yi k'orafi ba ko kad'an."

Nan ne naga ya d'aga idanu ya dubeni da sababben kallonsa Mara manufar komai yace
"Sumayya, karfa Zancen Momi yafa kid'imaki, duk da Gaskiya ta fad'I, Amma nasan baza'ki iya dani ba kema. Shi yasa girki iya cikinki za'ki rink'ayi idan kin soma girki.
Ya dubi Momi kuma
"Momi, kwanon a bincina fa Yana nan a wurinki kamar da, saboda Kinfi kowa sanin yarda nakeson d'and'anon a binci ko Yaushe.Khairat ke kamanta irin girkinki, to naga Itama ta soma shiriricewar yin girki irin na Muhibbat, yau a bu yayi kad"an gobe yayi yawa, to Itama na yafe ta, randa duk ba kya gida baki samu damar yimin girki ba Momi, waje zanje na samu Wanda yayi min na saya wallahi."
Banga wani sauyi ba Sam, a fuskar Momi, game da furucin d'anta, duk da tace
"Kadai biyo hanyar da bazata b'illemaka ba Fa'iz. Kayi aure, Amma aka da kwanon a binci? Kana dai da aiki a gabanka"

Ko kunya yace"Ja ma kuwa Momi, Amma nasan zan iya ne."
Ire iren wannan baisoma damuna ba, saboda nasan manufar auren da mukayi shi a zuciyarsa . Amma ni a Zuciyata, aure ne nake ji munyi mai manufa kyakykyawa, irin Wanda a keso. Shi yasa ni a binda zan maida hankali a kai, shine na Yaya zan janyo ra'ayin'sa gareni na canza masa alk'iblar da yake fuskanta.
Chapter 14 · 0% Book details