← Book details Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 31

Sashe 23

Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Duk wani laifi idan a kayi a gidan, Momi ni take cewa. Babban a bin takaici har Sata a ka kallafamin. A zatona babu wani abu da ake sacewa, domin a d'oramin laifin Sata, Sai Momi yau tace an sace mata a bu kaza, gobe ma haka, kuma tace nice ware, nice lallai zan d'auka, domin cikin 'ya'yan ta babu b'arawo. Momi ta kirani cikin 'ya,'yan ta, ban da Ancle, taci min mutunci a matsayin ni b'arauniya nayi mata Sata. Khalifa ma da Muhibbat su zageni son ran'su. Khairat ce Kawai bata tofawa, Zanga ta b'ata rai sosai. Na lura bayan kirkinta, hak'uri ne da ita ainun.

Muhibbat ta matsamin lamba sosai a tsukin. Idan nayi wanki, nayi shanya ta zubar a k'as. Da yake Ina wanke ma na Ancle marasa nauyi, amma bata zubar da na yayan'ta. Kunji son zuciya. Ni ke sharar gidan, amma randa Muhibbat ta so tsiya, Sai ta fizge tsintsiyar daga hannu na, ta share ko'Ina. Sharar idan ta kwashe Sai ta watso falona. Na rink'a dauriya, Sabida Kawai bana so K'orafi ya fara b'ulla daga bakina wurin Ancle ko wani nawa. Sannan Zuciyata tayi nisa a son Ancle Fa'iz, banason a binda Zai haifar da sa'in sa tsakanina da kowa nasa . Zaman aure na mutu ka raba na k'uduri yi da shi, iya yina.

Komai nawa na Kayan kichean, ni da Muhibbat muke amfana, musamman idan tayi bak'in k'awayen'ta, komai na kichean d'ina za'tayi facaka da shi. Filet filet da kofuna na k'arau ta yi amfani da su, ta zubemin a waje babu wankewa, ta kuma fasa na fasawa da gayya, duk dai Sai an cuzgunamin nayi magana, an zagi ubana. To, ni kuma Sai nayi lub, kamar banji ciwo ba. Kayan kichean d'ina duk ta farfashe k'arau d'in, ban dai tanka ba, na k'yale. Sun Sani a kwana sosai Muhibbat da Khalifa. Wulak'anci salo salo, zagi da Habaici. Hannune Kawai basa sawa su dakeni. Sau d'aya nayi wa muhibbat magana da ta fasamun fulas d'in shayi, da shi kad'ai ya ragemin, ta kuma kwashemin drink's na Friedge da nake tanada saboda Ancle.da tayi bak'i.

A binda ya fito daga bakin'ta shine.

"Ai naga, ba' daga gidan uba, akazo da drink's ba, yayan mu ya Saya, aikin banza shishshigi babu kwarjini"
Raina ya sosu, tamkar na fallamata mari, amma na daure zuciya.

Tabbas yayanta na sayo komai, amma Wanda duk ta kwashe ni na Saya. Kawu Sulaiman yana aiko min da kud'i a kai a kai, kuma yawanci, wurin yiwa Yayan su d'awainiyar sa kai na, ke tafiya. Sauk'inta bana yini a gidan,saboda makaranta, ba domin haka ba, a bin yawa zai min, Wai shege da hauka.

Ranar a sabar bani da lacture, banje school ba. A Kayi dace nayi bak'i kuma.'yan uwan ummata da suke uba d'aya, baba Maryam, da baba hasana. Tare na had'a Mana a binci mukaci, Sai yaran su, dana ware musu a faranti guda.

Fa'iz ne ya shigo da a zahar da ba sabon'sa ba. Ina hangen sa ta taga, saman Momi ya haye rik'e da poly bag k'arama, irin ta take a way.

Muna hira da bak'ina ya shigo falon da sallama, baisan da bak'in ba, Sai da ya shigo. Bayan sun gaisa, na gabatar masa da su, Sai yace nazo Yana son ganina dama tsintsiya ce a hannuna, zan share a bincin da yaran suka watsar, sai baba Maryam tace naje Kiran mijina ta share. Nabi bayan Ancle

Yana tsaye a d'akin nasa ya rungume hannu a k'irji, ya jingina da bango, kamar wani a bu yana damunsa na fuskanta.
Nace "Ancle yau ka dawo da wuri Amma "

Fuskar'sa babu walwala yace "Eh!" Yayi shiru. Sai daga baya Yaci gaba.

"Momi ta dawo dani,saboda waya tayi min Wai na taho da mata da take a way yunwa take ji. Nace mata yanzu Momi a binci Sai ya gagareki a gidan bayan da a Kwai komai? Saboda bana son dawowa, Ina kan wani a bu mai muhimmanci, amma Sai da na barshi, saboda tace min su Khairat dama ke dafa binci su bata, kuma duk sun tafi unguwa tun safe . Kuma gashi likita yace lallai Sai taci a binci sosai kafin tasha magungunan ta, na larurar rashin lafiyar da take ciki."
Nan na dubeshi nace, Dama Momi bata da lafiya?"

Ya dubeni galala. "Wace irin tambaya kike min? Waye baisan MomI bata da lafiya ba, kwana biyu? Duk da tace kikan jima bakije kin gaisheta bama, amma ai za'kiga ta fad'a kwana biyu.

Wannan abu ya Sosa min rai, shi yasa kika ga na kasa juriyar a jiyewa zuwa wani lokaci. Domin da nace Momi tayi Miki magana ki bata a binci, tun da kina gida, Sai tace bata buk'atar a bincin ki, tun da baki damu da ita ba. Tunda ta kwanta jiyya baki tab'a yi mata sannu da jiki ba, ba kya gaishe ta ma. Kuma da kina bata a binci, kika daina, Sai dai kiba almajiri. A binda ciwo a ce Momina ta rasa a binci a gidan nan Sai da na dawo, smma ga bak'inan su sunci, har sun zubar"

Tun da nazo gidan raina baitab'a b'aci ba irin ranar. Duk a binda suke min, ni banyi k'orafi ba Sai Sai su? Kuma gashi ya Shiga cikin su, ya yarda tun da yake tuhumata.

Na had'iyi yawu da k'yar
"Nifa ban fahimci zargin nan da ake so a lik'amin ba. Sam ni bansan Momi bata da lafiya ba. Waya fad'amin? Kuma Ina gaisheta, ni banga alamun wani rashin lafiya ba. A binci Ina bata ta dainaci tace bataso, to Yaya zan yi. Kuma a binci ma ai cewa a kayi nayi iya cikina, nifa a ka ware. Kuma ai ba'a bani umarnin ma bawa Momi a binci ba, ni nasa kaina nake bayarwar.

Take naga ya fusata ga rashin zato na.

"Har wani alfahari kike na Wai ke kika sa kanki kika ga damar bawa Momi a binci? Sai da kika ga Dama? to kiga kuma hagu. Kar ki sake bawa Momina a binci, umarni na baki Shima. Ki dafa iya cikin ki na sake fad'a. Ki Sani, ko zan iya hak'uri a kan wani a bu, banda a tab'amin uwa. Ko wanene bai isa ba wallahi."

Take zuciya tazo min iya wuya. A fusace nace

"Girkin ma ai ba dole bane. Domin iya cikina zan wahala? Nama daina dafa komai, kome na samu ya fad'o bakina ya wadatar. Kuma Allah shine Sha'hidi a kan kome nene Gaskiya. K'Arya ta shekara k'Arya. Gaskiya na makwafinta.
Ina fad'in haka na Mik'e nayi ficewata. Na fusatashi sosai na gani kan fuskar sa, amma Sai naga ya gaza cemin komai, face bina da kallon Mamaki, har na Fice.Tun daga ranar na rufe kichean ruf, ko ruwan tea Bana dafawa. Sam Bana karyawa da safe, ko Ina gida. Abinci Sai a bu mai ruwa ruwa,Sai ciye ciye Sama Sama. Amma banacin Gaskiya a bincin kirki a cikina. Ga damuwa da na d'orawa Zuciyata. Kuma na d'au fushi da Ancle Fa'iz ko falonsa bana zuwa. Da safe Yana shigowa wurina Bayan sallar a suba. Bayan na gaisheshi, bana sake ko kallon sa ballantana na tsinka masa. Shima ganin babu fuska, Sai ya ajiyemin kud'in da yake bani, batare da sake kulani ba. To dai banga ya d'au fushi kamar ni ba, yarda na fuskanta. Komai ya sayo Zai kawomin nawa d'aki ya a jiye. baya cewa komai, Sai ya fita. Ni kaina banyi zaton Ina da zuciya ba, Sai da aka kaini bango. Dama wasu sunce, mai hak'uri bai iya fushi ba

*🏤 NI DA GIDANA 🏤*

*_Littafi na daya_*

*NA*

*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

📱19
_______ Ba iya Ancle Fa'iz na d'au fushi da shi ba, duk gidan ne. Ji nayi an kai ni gargarar da bazan kuma d'aukar raini da wulak'anci ba. Momi Kawai zan iya d'agawa k'afa, albarkacin Ancle Fa'iz da kuma darajar haihuwa, tun da ta haifeni. Amma ita kan'ta Momi taga canji a wurina. Kullum zan je na gaisheta, Amma fuskata babu walwala, da rawar jiki na biyayya da nake yi mata. Domin da kullum naje gaishe ta, Sai na tambayi ko da wani aiki da zan yi mata. Bayan fa Kusan aikin gidan gaba d'aya da na kallafawa kaina, kamar mai aikatau.

Momi ta ban Mamaki da tace Wai bana zuwa gaishe ta, da bata a binci, da dubiyar rashin lafiyar da ban San da ita ba. Gaba d'aya zuciya ta ta karkata wurin yarda da cewa Momi Yak'i takewa Salima bayan idonta.

Domin Khairat ce ta sameni rannan da babu kowa a gidan bayan sallar magariba, tazo d'akina tace min.
Chapter 23 · 0% Book details