Sashe 24
Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Matar Yaya, wallahI ki k'ara rik'e mijinki da kyau, domin Kusan kullum Sai Salima ta yiwa Momi waya. Rannan hands free Momi ta manta tasa, naji Salima tana yiwa Momi magiya kamar zata yi kuka, Wai tana bala'in Son Yayan Mu, shi yasa baza ta iya zama da kishiya ba, Wai Momi ta taimaka mata. Saboda Salimar ta cewa Yaya, ya sakeki tun da saboda ya sameta ya aureki, kuma tun da Momin ta ta sauko ma tace ko yaushe yazo a yi aure. Amma Sai Yaya yace mata babu ruwanta da zancen auren sa dake, tayi gefe da shi. Kawai tasa himma a kan tsara musu Zaman farin ciki da Soyayyar da za'su shimfid'a, kafin isowar auren. Ita burin Salima fa Kawai Yaya ya sakeki kafin auren ta da shi. Shi kuma yak'i bata amsar yiyuwar hakan. Momi Hak'uri ta bata dai, tace tabar komai a hannun'ta zatasan yarda za'ta b'ullowa komai, saboda yanzu binsa take a sannu, saboda har yau bai gama hucewa ba, da a binda maman'ta tayi masa. Kuma Khairat ta ce min, taji Momi tana fad'awa Ancle Fa'iz Wai ya d'auki matakin plannig, wato tsarin iyali a auren ku, saboda batason ya haihu da ke kafin zuwan Salima. In so samu ne ma ya sallameki yanzu, tun da kwalliya ta biya kud'in sabulu. Amma Sai cewa Momi yayi. Momi nasan a binda nake yi nima name ya kamata nayi a lokacin kuma da ya dace, kusamin ido. Momi bataja musu da shi ba, duk da bata fahimce shi sosai ba. Haka za'lika nima ban fahimta ba. Amma fatana kar burin su ya cika a kanki Anti Sumayya. Wallahi ni nafisonki da Anti Salima."
Wani irin k'aunar Khairat ya k'ara mamayeni. Rungumeta Kawai nayi, nace "Khairat Ina k'aunarki, fiye da kowa a gidan nan. Allah ya ganar da su gaskiya, su san ni ba a bokiyar hamayya bace, face masoyiya ga Ancle, mai son sa da son ci gaban'sa, da su baki d'aya. Ta kuwa ce "Amin.
Murmushi nayi, da a ke gudun, na samu ciki na haihu da Ancle, to duk Ina tunanin su ya tafi? Ko jituwar da suka ga munayi da shi a tsukun, suna zaton komai yana tafiya na aure tsakanina da shi? Da sun San komai nasan Momi bazata yi a sarar yawun bakin'ta ba.
Tun da Khairat ta fad'amin maganganun nan, suke tayi min yawo a rai. Tabbas k'Wace goriba hannun kuturu bazai yi wuya ba. Za'su iya iya rabani da Ancle Fa'iz nan da nan, tun da ko tubalin ginin dasa sabo da k'auna da shak'uwar da nake fad'i tashin yi kullum, bai yi nisa ba, ballantana yayi k'warin da Sai anyi gwagwagwa da shi, kafin a rushe. Shi yasa Wata zuciyar ke min shelar cewa, Kawai na shafawa kaina lafiya da Ancle, na saddak'ar, nasa rai da isowar cikar wa'adin auren mu, na rungumi k'addarar shiryawa Zaman zawarci, da tunkarar sabon wani auren da bazan tab'a so ba, Sai dai nayi a larura.
Saboda manyan matsaloli ne masu wuyar warwaruwa ke ta tunkaro ni cikin aurena da Fa'iz. Ko ga na Momi Kawai ya isa na sare. Saboda naga k'iyayyar mai zafi ce, tunda har ba'ason had'a jini dani. Lallai Khairat, tana k'aunata sosai, tun da ta iya fad'amin sirrin mahaifiyarta.
********
Na tari, ruwa a fanfo, zan Shiga band'aki nayi wanka. Muhibbat ta taho da sauri da nufin angijeni tayi saurin shigewa saboda neman fitina, bayan ta baro wani band'akin a bayanta. Batasan a yarda nake ji da tsiya ba, kowa ya tunkaroni a lokacin karawa za' muyi. Shi yasa banyi jinkirin angijeta ba,iya k'arfina, Sai gata a k'asa wanwar
Ta kuwa Mik'e da masifa za'ta soma aunamin zagi, yarda ta saba. Nace cikin d'aga murya
"Ahir!, yarinya. Karki d'auki kawaicina a matsayin gazawa. Kuma karki d'auki Hak'uri na a matsayin tsoro. Idan har ke kin cika d'iya ta halas, to ki kai ga jikina, domin fad'a na baki na matsorata ne."
Sautin murya ta da yayi Sama, a she Momi taji yo, Sai ta fito, haka Khairat, suka zubo Mana idanu daga saman bene.
Muhibbat tayi min wani matsiyacin kallo tace
"Samun wuri, Wai d'an wake a hotel. Ke bora, kuma 'Yar tsaron k'ofa, har kina da bakin magana? har da fiffik'a?
To ba za ta kaimu da nisa ba, zakisan matsayin ki idan kin manta. Bari Yaya ya dawo."
Dama nasan a binda ake nema Kenan a keta jangwalata,na d'aga hak'ark'ari ace ga a binda nayi. Basu San yanzu na k'una bana tsoron k'auri. Ta kwab'e ba damuwa ta bace.
Nace
"Abanza Wai talaka ya girmi sarki. Me Yayan Zai iya yimin? Iya Kaci yace ya sakeni, shine k'ololuwar hukuncin da zai yi. Ko zai datse fitar Numfashina? Ko kuwa zan daku ne? Iko guda ne, ya sakeni, kuma na shirya, tun da ba'autan maza bane. Kuma gari da yawa, maye ai bazai ci kan'sa ba. Idan kin isa tsagera kizo kuma ki shafeni, idan ba'a kwashi k'asusuwanki ba."
Furutaina sun tunzura Momi, saboda gabanta nake tijarar, kuma tasan na ganta. Kuma tasan idan 'yarta tayi sake muka dambata, Sai na lallasata sosai, saboda na fita siffar k'arfi ma a ido. Ita 'yar kyalan kyalan take. Bata da cikowar komai a jiki na cikar surar mace. Kyan iya fuska yake, Sai farar fatar abin alfahari, irin na 'yan uwanta, idan aka cire Khalifa.
Momi tace "Karki kulata Muhibbat. Ai Kare baya yi Maka haushi ka rama, Sai Ku zama d'aya. Ko a usuli da nasaba kun bambamta, ba kya daka ta tata ba. Kinsan kuma harbi ga d'an kunama gado ne."
Na d'aga kai na kalli Momi a zuciye, na kau da kai, Kenan ta ramawa 'yar ta. Darajar haihuwa taci, da tazarar shekarun da ta bani, gashi na samu tarbiyyar girmama manya, da ta gane ita ma shayi ruwa ne. Domin sun kaini k'urewar bango.
"Momi, ni Mamaki take bani fa! Wai 'yar jiran k'ofa jeda a bin cewa. A cewar Muhibbat.
Na Doka mata kallon k'ask'anci.
"A littafin maganganun dake bakina, shafin farko ma ban bud'e ba. Zan kuma karance Miki shi, in dai kika ci gaba da ja dani. Matsoraciyar Kawai, Wacce a fad'an baki tafi kauri." Ina kai nan, Sai muka had'a idanu da Khairat. Murmushi tayi, dake nunin taji dad'in 'yancina da na karb'a.Dole idan ba'a kiyaye ni ba, za'a sassauta kuwa.
Nan na wuce band'aki na bar Momi da Muhibbat suna ta yada maganganu. Na fahimci na had'a musu zafi, bayan mamakin da na basu. Basu tab'a zaton zan iya haka ba.
A na Kiran sallar Isha'I na jiyo sallamar Ancle Fa'iz ya shigo. Nasan Kiran'sa a Kayi a waya, domin baya dawowa dai dai wannan lokaci.
Nan ma saman Momi ya wuce kai tsaye.
Ina zaune rik'e da kofin flastic, Ina shan corn flake's, domin shine ire iren kalar a bincin da na komawa, mai ruwa ruwa. Sati biyu Kenan da k'untatawa kai na da nayi na k'in yin girki. Saboda b'acin ran da nake ciki, Bayan rashin a bincin kirki, duk na soma rama, k'asusuwa na kwarin wuya son soma yi min mirjani. Ga bak'i da na soma yi.
Ancle ya shigo da sallama, saye yaje da rigar kakin jin's riga mai gajeran hannu da wandonta na jin's. Gaban rigar manyan mab'allaye ne, ya b'alle biyu na saman a na hango k'irjin sa kad'an.Kayan jajaye ne masu duhu, shi yasa sun k'ara haskaka kyawunsa da hasken fatarsa. Kyawun da suka yi masa bazai misaltuba. Tamkar d'an bak'on balarabe a k'asar Hausa. Bantab'a ganin yasa Kayan ba. Ta yiyu, sababbine ko a jiyayyu.
Ranar ko sannu da zuwa na kasa yi masa,saboda nauyin damuwa da ya rik'emin Mak'oshi. Tun da muka samu Sab'ani da shi, dama gaisuwa Kawai ke had'ani da shi, ko sannu da zuwa, idan ya dawo ya shigo a jiyemin nawa a binda ya sayo na Mak'ulashe. Ancle Mutum ne mai sakin hannu sosai na sayo wannan sayo wancan na wasa baki, in dai yana da shi. In yayi kud'i za'aci dad'i Kam ba kad'an ba.
Ya zauna kusa dani kan kujera. Na basar na ci gaba da shan corn flakes d'ina kamar ban San da tsirar sa ba. K'iris Kawai nake jira, a yi b'atacciya.
Yace "Sumayya!. Na amsa da k'yar.
"Wai maye yake damunki ne? gaba d'a ya kin canza, kan d'an a binda bai kai ya kawo ba. Ban San ki Sam da halayyar fishi ba, ko rigima, ballantana fad'a. Ina kika a ro wad'an nan d'abi'u?
Na fusata nace.
" Ba'arowa nayi ba ma, Karb'owa nayi kyauta, domin na ceci kaina Ancle."
Yayi d'an jinkirin magaba, domin jinjina furutaina.
"O k, naji. Yanzu fad'amin a binda ya faru a yau. "
"Au, ba'a fad'a Maka ba?"
Yace"Ko an fad'amin a dalcine naji kuma daga b'angarenki ko?"
Nayi yak'e na takaici.
"Duk a binda akace Maka nayi gaskiya ne Ancle. Bani da kirki. Duk d'abiar da kasani ta banza, toni gwanace. Matsalolin duk da suke faruwa a gidan nan, nice sila, tuntuni fad'a Maka ne ba'ayi. Saboda haka babu wani bincike da zaka kumayi. Kazartar min da hukunci Kawai, shine magana.
Kuka ne ya nunamin fin k'arfi, na aibata kaina da nayi, domin na yarda k'wallon mangwaro na huta da k'uda.
Nayi k'ok'arin Mik'ewa na shige d'aki, Sai Ancle ya rik'e hannu na, domin dakatar dani. Iya k'arfina nasa kuwa na fizge, saboda a tunzure nake sosai nace "Ni ka rabu dani. Ka zartar min Kawai da hukunci. Na fad'a d'akin ina sheshshekar kuka. Baki bud'e na bar Ancle Fa'iz, domin furutaina sun girgiza shi ainun.
Ina Shiga d'aki Sai gashi ya biyo ni. Na hau kan gado, Shima ya hawo. Ina ja da baya, Yana biyoni.
"Wai ka rabu da ni Mana. Bana fad'a Maka gaskiya ba? Ka k'yale ni Ancle.
Nama rasa a binda ya hanashi yin zuciya a lokacin ya rabu dani, domin mai zuciyar ne.
Sai da na kai k'arshen gado, na Hak'ure. Ga Mamaki na, ya d'ago fuskata, da hannayen'sa ya Shiga sharemin hawayen fuskata.