← Book details Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 31

Sashe 30

Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ancle Fa'iz Mik'ewa yayi ya dawo gabana ya zauna dab dani, jikinsa ma ya had'u da nawa. Ya yayemin mayafin da na rufe fuskata. Ya jawo hannayena duka ya matse cikin tattausan farin nasa hannun. Ya soma magana cikin wani irin tattausan lafazai, na lallashi. Nan naga Kawu Sulaiman Kawai ya
mik"e ya fice da sauri, saboda yaga a bin ya girmami ganin sa, bai kuma San Ina za'a tsaya ba.

*🏤 NI DA GIDANA 🏤*

*_Littafi na daya_*

*NA*

*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

📱24
________ Ancle Fa'iz ya soma da bani hak'uri ta hanyar kwantar da kai da murya da lallashi, tamkar shi yayi min k'azafin, Sannan ya d'ora da cewa "Sumayya duk a binda kike so zan yi miki shi, matuk'ar bai fi k'arfin yi na ba. Ni kuma alfarma d'aya nake nema a wurinki, shine ki koma d'akin ki a yau d'in nan. Komawarki yau, yana da matuk'ar muhimmanci, kuma komarki ita zata k'ara wanke ki daga zargi, kema ki samu sauk'in kuma damuwa, domin a Kwai wani a bu da ya biyo baya, bayan kin taho, Sai kin koma kuma zaki ji shi da kunnenk, na kuma tabbatar jin zai sa ki samu nutsuwa."

Furutan'sa sun d'an kwantar min da hankali kad'an duk da cikin damuwar nake sosai.

Nayi k'ok'arin k'wace hannaye na daga cikin nasa na kasa, domin k'ara matsesu yayi da ya fahimci nufina. Na dubeshi kad'an Wanda dama shi tun d'azun idanun nasa zube suke a kaina.

"Zaki koma d'in my Sumy?" Na girgiza kai.
"Ina jin nauyi Ancle. Ina jin nauyin idanun mutan gidan nan naku da suke yi min kallon mutuniyar banza. Bazan iya had'a idanu da su ba. Kai ma d"in kunyarka nake ji, kayi hak'uri Ancle Fa'iz ka barni. Na yafewa kowa ma, amma ka barni a nan please."

Ya girgiza kai da sauri.

"Bazan iya barinki ba Sumayya, Sai kin koma kin wanku a idanun kowa, nafa fad'a miki a Kwai a binda ya biyo baya, bayan kin taho, dole Sai kin koma zai yi amfani. Kuma Ki dai na jin kunyata ni. Kika kawo min k'ur'ani izifi sittin zan iya dafawa Wallahi, cewa baki aikata wannan laifi ba. To wai ma ta yaya hankali zai d'auki wannan? Idan mafad'in magana wawa ne, bai kamata majiyinta ya zama wawa ba. Ba yabon kai ba, ke da kike da kamata me za'kiyi da Khalifa? ni nafi can canta da kinemi buk'atar ki a wurina idan ma kina da buk'atar Kenan, amma ba wurin Khalifa ba. Tun da baki nema a wurina ba, to na tabbatar ba za ki nema ba a wurin Khalifa. Na auna d'abi'unki cikin ma'aunin sikeli na hankali, sun nauyayi nauyin aikata irin wannan aiki mummuna, Wallahi ba zaki aikata irin wannan b'arna ba, ba za ki tab'ayi ba, Sai dai idan ba kya cikin hayyacinkI. Ki yarda dani, ni tuni na yarda dake, duk da ba muyi jimawar da zan yi miki wannan yardar ba, amma ni Zuciyata ta tsimu da Samun a minci dake, zuciya ta ta nutsu dake. Kiyi min halacci my Sumy, kin yarda zaki koma?" Ya sake jefomin tambayar cikin k'ara shigar da fuskarsa dab da tawa kamar za'su had'e. Babu shiri na gyad'a kai nace "Na a mince." Saboda zan Sha kunya idan Kawu Sulaiman ya dawo ya same mu a haka, shi kuwa nasan ko a jikinsa.

Nayi k'ok'arin mik'ewa, Sai ya saki hannun nawa. Yin hakan Kenan, Sai ga Kawu Sulaiman ya shigo, Yariman nasa yace masa "Nayi nasara na jefa k'wallo a raga cikin sauk'i kuma Sulaiman"

Kawu Sulaiman yayi murmushi ya bashi amsa.

"Ai ba bak'on a bu bane hakan, tun da ka saba yin irin wannan nasara ko Yaushe Yarima"

Nasan dai da ni suke, suka malk'waya a bin da harkar boll.Duk da damuwar da nake ciki, Suka burgeni da naga sun yi wani irin tafawa da tafukan hannun, kamar musabaha, irin na a minan da suka yarda da junan su.

"Bari na Shiga mu gaisa da mutan gidan, Sai nazo Mu d'au hanya." Yariman ya fad'i a gaggauce.
Bayan mun Shiga mota
yace

"Ko za'ki jamu?"

Na girgiza kai nace "A'a"
Ya fuskanci Zuciyata babu dad'I, Sai yayi shiru Kawai yaja motar.

*********

Shiru muna tafiya kamar bebaye, har mun kusa isa gidan mun Sha kwanar Shiga layin gidan, Sai Kawai na samu kai na da ci gaba da kuka. Kuma kuka mai tab'a zuciya. Ba k'aramin kunyar Shiga gidan nake ba, ga bala'in tsoron Momi. Gani nake yi ma da na Shiga gidan tsawa zata dakamin tace na juya. idan nayi sa'a Kenan bata rufeni da duka ba, saboda bak'in Jinin da na k'ara a idanunta. Gani nayi Ancle ya tsaida mota a gefen titi, ya kashe injin motar, amma hannun sa yana kan sitiyari. Ran sa babu dad'i yace "Sumayya na fahimci zuciyarki tayi nisa bisa ga rashin son zama dani, saboda haka zan danne tawa zuciyar nayi miki yarda kike so, ba domin naso ba, Sai domin Sama miki da farin ciki da kwanciyar hankali. Nine silar komai, bazan so kuma na sake zama silar sake Shigarki k'uncin rayuwa ba a karo na biyu. A dane nake tunanin mu rabu, amma a yanzu wannan ya kau. zan yi juriya ga yarda kike so,saboda farin cikin ki nawa ne Sumayya.

Yanzu zan juya na mai dake gidanku, ni na rink'a zuwa Ina dubaki, har lokacin da zaki samu nutsuwar zama dani, ko kuma Sanda na hattama gini na"

Tausayin'sa naji ya kamani kuma, da wata irin sabuwar soyayyarsa. Domin kuwa an zo gab'ar da Ancle ya saryar da nasa farin cikin domin inganta nawa. Duk mintina son Ancle Fa'iz ji na keyi yana k'aruwa a Zuciyata, ballantana a ce na kalleshi. Ko a mafarki ban yi zaton zan iya auren Miji na kerewa sa'a irin Ancle Fa'iz ba ballantana na samu kulawar sa. To ni wacece da zan yi ta wahalsheshi, bayan yana da Wacce ta damfarani da k'asa ta take in dai wurin cikar halitta ne, da jan hankalin namiji a ko Ina.

Kija zaren ki a sannu, karfa ya tsinke. Zuciya tace ta bani shawarar.
Bansan Sanda nace

"Ancle mu tafi, na hak'ura zan je."

Bai tada motar ba yace"In dai da gaske, kin a minta dani, kuma kina son zama dani, to karki k'ara yin kuka Sumayya'"

Na sunkuyar da kai nace

"To, na daina"

Ba zata naji Ancle yace

"Sumayya bansan San da k'aunarki ta shigeni ba, kuma ban tabbatar da hakan ba, Sai bayan da kika gudu gida ban Sani ba. Kawai Sai naji gidan yayi min kuma zafi, naji kad'aici da ban tab'ajin sa ba. Na kuma rasa sukuni da kwanciyar hankalI sosai.

Lokaci guda zuciya ta ta Shiga sark'ak'iya na na k'yaleki ko nabi bayanki. Wacce tafi a zalzalata ita ce na nabi bayanki. Domin har gargad'I na ma tayi, tace kai wani irin Mara wayone kake neman jazawa kan ka a sarar macen k'warai mai kyawun d'abi'u irin wannan?.
Tabbas Sumayya kin can can ci SO! a wurin namijin da yasan ciwon kan sa, kuma yasan me yake yi."

Wad'an nan zak'ak'an kalamai da na jima Ina sauraron jin su daga bakin Ancle ban so suka zo min lokacin da nake cikin zullumi da fargaba da rashin nutsuwa ba.

Nasan komai zan iyayi na farin ciki da bai kaucewa k'a'ida ba, a kan wannan abu mai kama da babban albishir, da bansan dame zan misaltaba. Baki d'aya ma Sai naji fargabar zuwa gidan su Ancle ta sulale tayi nata wuri. Wani k'warin gwiwa ma naji da k'arfin zuci, saboda Samun Soyayyar Ancle da na sare na cire tsammani. Shiru da nayi saboda farin cikin da ya ratsani, yasa Ancle ya kaimin dunguri da key d'in mota.

"Kin yi wani silent, ko kina doubting ne ?"

Murmushi ya sub'uce min "Wallahi A'a bana ko kwanto, domin na yarda da kai"

Murmushi yayi, yace kuma "Kinyi zaton hakan zai faru?"

Na kasa bashi amsa a nan" Ya gaji yace.

"Kika yi min shiru? za kiyi bayanin komai a gaba, kuma da bakinki."

Bansan me yake nufi da hakan ba, shi yasa naci gaba da tsuke baki.

Yayi wa mota sabon key muka ci gaba da tafiya.
Tare muka Shiga gidan kuma a jere da juna, ni dai kamar a ce kyat na runtuma. Sai Mik'a wuya nake saman Momi Ina waige. Muhibbat ce ta fito daga d'akin ta tana waya har da dariya. Tana tozali damu, Sai ta runtuma a guje d'aki har da b'amewa daga cikiU

Ancle Fa'iz da ya bita da kallon harara naji yace "Sha Sha Sha ,kyayi ki gama, zamu gauraya a gaba ne. Nan nasan shi take gujewa Kenan.

Muna Shiga Falona ko zama bai yi ba yace
"Sumayya bari naje wurin Momi na dawo." Ya share fiye da awa guda, kafin ya dawo.

Da ya dawo fuskarsa dai babu walwala sosai, yace min."Sumayya kiyi hak'uri a kan komai za'ki gani, komai zai koma dai dai sannu a hankali, da yardar Allah. Na kuma d'auki wasu matakai ma na gyara, a yanzu da kuma nan gaba. Yanzu kuma idan munje wurin Momi dake, ki bata hak'uri sosai, ki nuna ke mai laifice a gareta, ki nemi gafarar ta."

Nayi murmushi "Momi nace fa Ancle, ba Sai ka tunasar da ni ba. Wallahi Ina da niyyar hakan dama"

Yaji dad'in lafazai na, yace
"To Muje"
Ni na shige gaba, ya biyo ni a baya. A fargaba nake, dakiya na aro Kawai. Momi tana tare da Khairat da muka Shiga. Ina Shiga na zube rigis kamar a fada, na kai gaisuwa ga Momi, cikin ladabi tsura. Ta amsa kadaran kadahan. Fuskar dai babu fara'a
Khairat kuwa naga murna sosai da farin ciki sosai da zuwana. Ta gaisheni cike da walwala.

Ancle Fa'iz yace"Khairat ki rawo Muhibbat, tun da Khalifa baya nan, Sai ta wakilceshi, kuma tun da bakin su ma d'aya wurin iya shege, nasan zata labarta masa."
Chapter 30 · 0% Book details