Sashe 25
Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ban yarda ke mutuniyar banza bace,mai kuma mummunan hali. Banyarda ba Wallahi, duk da kinyi ik'irari da bakinki. Duk in da kika je kika b'ata kanki, zanje k'Arya kike. Zan baki Kariya sosai, na kuma wankeki, nace Sumayya yarinyace me ladabi, mai kirki, mai Hak'Uri, mai addini, tayi zarra wurin Yakanah da kamun kai."Furutan sa sun zo min a ba zata. Ban tab'a sanin shi d'in ya tsaya nazarin sanin halayena ba, har ya karance su tsab, a tsawon Watanni Kusan biyar da auren Mu. Jikina yayi sanyi, kuma yayi laushi lub'us. Har lokacin hannun sa yana rik'e da hab'ata fuskata na fuskantar tasa yace.
"Bansan me ya hargitsaki ba, ya kuma tunzuraki, har kike k'agar halayyar banza kike danganta su, da kanki. Me zai sa kiyi haka. Haba my Sumy."
Baki d'Aya lakar jikina ta mace. Sunan da ya k'irk'iran min lokaci d'Aya, yayi matuk'ar karb'uwar jin dad'in sa da tasiri a Zuciyata, wurin hab'aka k'aunar Ancle a zuciya ta, da da nake k'OK'arin ya kicewa da k'arfi, saboda wuya, da fitintinu.
Cikin sauk'I Ancle Fa'iz yajanyo ra'ayina na fad'a masa a binda ya faru, Amma banda na can baya. Ko sunan Momi ban kamaba,domin matsayinta gareshi, bazan iya cewa tayi min wani a bu ba.
Fushi sosai na Gani kan fuskarsa, yace"Banyi Mamaki ba, Muhibbat zata ya fiye da haka. Dadai Khairat CE, shine zanyi ko kwanto, domin shigen halayyarku d'aya.
Muhibbat kowa Hak'Uri yake da ita a gidan nan Sumayya. Ko iyayen Mu, ni nake yi musu maganinta idan ta buwayesu, domin ni kad'ai take shakka. Nasan kuma ba iya a binda ta tab'a yi Miki Kenan ba, kin b'oye wasu. Kiyi Hak'Uri domin, ni. Ki jure domin ni.ki kau da kai domin ni.Nasan kina Sona, domin a binda kike min, Wallahi soyayyace Kawai zata yi jagoranci ga haka.Don Allah komai ya wuce, kinji Sumy?
Bansan Sanda murmushi ya sub'uce kan leb'ena ba.
"Wallahi komai ya wuce. Kuma zan k'ara d'amarar juriyar a binda sake biyo baya, my Ancle. Naji dad'I daka fahimceni, batare da tallafina ba.
Da sauri yace
"Yauwa my daughter. Bazance da Momi ko Muhibbat komai ba, domin cewa za'ayi Nabi bayanki. Sai kiga rigingimu sun kuma b'allewa. A Kwai wasu a bubuwa da nasani da kike zaton ni d'in bansa ni ba. Har jarrabaki nayi a wani a bu, Amma Sai da kika lashe jarrabawata. Nayi Miki jinjina Gaskiya."
Ya k'arashe cikin wani tattausan murmushi, ya Mik'e a hankali, jikin sa Sam babu kuzari ya Fice.
To ni d'in ma ya burgeni ainun, na yarda ya janyo hankalina, yasa nayi sanyi na hak'ure komai, sa'I d'aya. Ban tab'a zaton Yana da taushi da sanyi na d'abiar iya tarairayar mace ba cikin salo na sace zuciya. Ni Kam ai Sai na k'ara matowa a Soyayyar Ancle Fa'iz.
*🏤 NI DA GIDANA 🏤*
*_Littafi na daya_*
*NA*
*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
📱20
_______ Faruwar rikicin nan, da aka so Ancle ya d'au mummunan hukunci a kaina, kamar k'ara ingiza alak'ata da Ancle Fa'iz tayi da k'arin shak'uwa. A binci tuni Ancle ya maido cin,sa falona. Ko Momi tayi masa girki, Sai ya d'auko ya shigo wurina. Dama ga nawa da ya zame masa k'ara'i, Sai yaci ko bayawa. Yanzu kuma yakan d'an yaba, sab'anin da da Sai ya kushe, ko yace na kuskure wani a bu, ko kuma yayi shiru bazai yaba ba, ko da yayi dad'in. To yanzu, nima na k'ara zage damtse ne sosai wurin kyautata girkin da jikina da kud'ina. Na sayi littattafai na koyon girki da Shiga group group kuma na internet na koyon girki, har da na practical. Duk domin na k'wato 'yancina a matsiyina na matar Fa'iz ya damu da girkina, ya rink'aci fiye da na kowa.
Jiddin tare muke cin a binci da Ancle Fa'iz. Hira ma ya rage yawan yimin k'orafi, ko nuna damuwa irin da yace na dameshi. Amma dai duk da haka bai fiyason hira ba, Sai Sama Sama. Ana jimawa sosai kafin ayi hira da shi mai tsayi. Sannan zafin zuciyar'sa yana nan daram, Sai dai idan ba'a b'ata masa ba. Shi yasa nasan irin takun Zaman da nake da shi.
Momi da Khalifa da Muhibbat ganin mun sake d'inkewa da Ancle fiye da da, ai Sai a ka sake yiyowa kaina da fitintinu iri iri, amma ba'a takani kamar da. Musamman Muhibbat da take zuwa gabana ta d'uramin ta maguzawa (zagi). Yanzu Sai baya baya, idan zata yi min tsiwa, saboda na nuna mata nima A' ce , tsab zan casa ta idan ta Shiga hannu na. Wannan yasa a Kayi musaya, Khalifa ya karb'i ragamar, domin yasan bazan iya da shi ba. Sai yafi uzzuramin a tsukun. Zagi ta uwa ta uba. Lub! nayi , duk da nasan iya zagi zata tsaya, bai isa yace zai kai hannu jikina ba. Na mai da shi, tamkar Kare mai haushi, da Sai an kula zai samu tasiri. Saboda darajar Kawai Ancle da yace na jure domin shi."
Cikin hutu muke a tsukin. Saboda haka, Ina zaune na rasa a binyi, ga babu wuta, babu a bokin hira, na fito tsakar gida fitina ta afku. Na rabka ta gumi. Ancle Fa'iz ya shigo da sauri, ya tsaya kaina yace.
"Sumayya zo Muje kiga motar da na Saya a k'ofar gida, Sati shida Kenan da na bada cigiyar a samomin irinta, Sai yanzu a kayi katarin samota."
Cike da farin ciki nayi a zamar Mik'ewa."Wow! Ina murna my Ancle. Muje na ganta. Nasa mayafi nabi bayan Ancle Fa'iz. Motar Kam tayi kyau sosai. Pomatic, sunan ta, kuma Automatic ce. Dark green. zata dace da mai ita Kam.
"Gobe tun da babu makaranta, Sai Muje na d'anaki Mu zaga gari ko?"
Cike da zumud'i na gyad'a kai. "Sosai ma, a she nice farkon d'ani "
Washe gari kuwa, a gaban Momi da Muhibbat muka Fice ni da Ancle. Mugun kallo Momi ta jefa min da nayi mata sallamar zamu fita da Ancle. Bata tsinka ba kuma. Amma nasan Ancle ya fad'a mata komai.
Tafiya muke cikin 'yar kyakykyawar motar zuciyoyin Mu duka cike da nishad'i. Hatta Ancle na ganshi cikin walwala sosai, duk da ba Wata hira muke sosai ba, Sai Jifa Jifa, Sai Jan motar da yake, sannu sannu, ya Saki slow music na R. Kelly, cikin wak'ar sa ta I blieve I can fly. I blieve I can touch the sky. Ancle yayi 'yar dariyar nan tasa ta burgewa da Sai tayi hali za'aga yayi.
Yace"Sumayya kinji wani Mak'aryacin mawak'i a binda yake cewa kuwa?" Na saurara, naji nace "Ai da kansa yake Ancle. Tunda cewa yayi ya yarda zai iya tashi sama, kuma ya yarda zai iya tab'o saman gajimare, kaga mu 'yan jini da kunne, ba yarda muka yi ba."
Ancle ya gyad'a kai.
"That is true." Yace a Tak'aice.
Na maida kaina wurin taga ina ta faman kallace kallace ta tagar mota, har na k'yallaro Wata mata tana tuk'a mota, gwanin Sha'awa.
Na waiwayo gefena nace wa Ancle Fa'iz. "Ancle Wai kuwa tuk'in mota da wuya?"
Yace "Babu wani wuya, nima nan da nan na koya. Kinga wannan Automatic tafi sauk'i sosai fiye da manual, domin Kinga Auto, ita take caccanza giya da kanta, kuma totur Kawai zaki taka, ki tafi, babu ruwanki da taka kuloci da caccanza giya."
Nace"To ai ni bazan fahimta ba Ancle Fa'iz tun da ba koyon nayi ba"
"Kina Sha'awar koyon tuk'in mota?" Yace bayan ya rage sautin music d'in da yake tashi da hannu guda, guda kuma yana kan sitiyari yana d'an jujjuyashi.
Nace "Wallahi Ina Sha'awar driving."
Yace "To kuwa kin samu. Bari Muje filin koyon tuk'i na soma nunamiki daga yau." Ya juya kan mota, ya canza hanya Sannan ya k'ara speed, Sai gamu a babban wani fili babba, har da Wata mata ma da mijinta, Itama tana koyo.
Ancle ya nunamin komai a hankali, da yarda zan yi komai. Kamar wasa ya bani kan motar, ko tsoro bai jiba, yace na jarraba, amma yana kusa dani a gefena. Kafin na soma yace" Sai kin sa nutsuwa sosai fa, kuma ki cire tsoro, idan ba haka ba, zaki jima baki iya ba."
Tiryan Tiryan da na bi shawarar Ancle na kuma bi yarda ya nunamin komai, Sai gashi Ina tuk'in motar sannu a hankali. Sai da ya sani nayi round biyar na tafkeken filin wurin.
K'arshe yace " Sumayya, Stop the car."
Da na tsaya cak, yace.
"Kin burgeni gaskiya. Nasan duk in da muka sake yin fita uku ko biyar zaki iya mota. Abinda ya rage Kawai zai rage miki, hawa titi da lunguna, kinsan Shima training d'insa, dabam yake da na filin wuri irin wannan. Yanzu ki mai damu gida."
Na zaro idanu "Daga koyon farko? baka tsoron na tintsirar da kai a hanya, ko na yasheka a wani sak'on?" d'an Murmushi Kawai yayi, bai tanka ba, ya karb'i kan motar.
*******
Tun daga ranar kullum Sai mun fita a mota nida Ancle Fa'iz saboda koyamin mota. Mu kanyi yawace yawace kuma sosai a mota, bayan mun gama da komai. Bantab'a Samun farin ciki ba, zuciya ta ta rink'a haske tun da na auri Ancle, ba kamar na lokacin. Domin mun sake da juna da hira da annashuwa fiye da ko Yaushe. Amma dai har lokacin bansan matsayi na ba wurin Ancle Fa'iz. Ko da wasa banga alamun Wai Sona a tare da shi ba, duk da kulawar da yake bani fiye da baya, da kuma hira ta nishad'in da Mukan yi.
A k'arshe dai nike Jan mota na fita damu na dawo da Mu. Har takai ma yakan bani mukullin motar na fita, ni kad'ai a cewar sa, da haka zan k'warance. K'iyayya sosai kuma mai zafi, na ganta a wannan k'arni, tasu Momi da 'ya'yanta, amma nayi biris.