← Book details Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 31

Sashe 8

Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sam banji dad'in hukuncin da Kawu ya zartar ba, don dai yafi gaban nayi jayayya da shine, matsayin sa ya wuci nan nesa. Amma na k'alubalanci tunanin'sa. Usman da Alhaji Rabi'u duk babu na yadawa wurin yabo. Sun Sha d'awainiya dani da Zaman jirana na shekaru, amma tashi d'aya a koresu? da wani ido zan kallesu? Wani zargi zasu yi min? ta Ina zan maida irin'su? Wani lokaci kuma zan d'auka Zaman jiran Wanda Zai dace dani a d'abiance, bayan shi hali ba'a goshi yake ba da za'a gani a tabbatar. Abin a lullub'e yake. Addu'a ce Kawai na tabbatar idan anayi zata lalubo Wanda ya dace dani, amma ba hasashe, ko zato ba.

Na Shiga damuwa har wayewar gari, amma ban bari kawu ya fahimta ba, saboda ina jin nauyi da kunyar yasan hakan. Domin bani da kamar sa a Duniya. Bana iya had'a kaunar'sa da ta kowa. Abinda yayi min a rayuwa, cikin family d'ina kaf babu Wanda yayi min rabi rabin'sa. Ya cancanta da nayi masa biyayya a komai da bai wuce k'a'ida ba, wato haramun. Da wannan dalili nayi ta jinyar damuwar Zuciyata a b'oye Ina had'awa da addu'a har komai ya sassauta a raina. Ban sake fita zance wurin Usman ko Alhaji Rabi'u ba. Sun dai daina zuwa, bayan d'ayansu kowan ne da yazo sau d'aya Kawuna Sulaiman yaje ya gana dashi. Bansan yaya suka k'arke ba. Ni dai nasan, duk Sanda tsautsayi ya had'oni da su a hanya, zan sha kunya, kamar na nutse. Bana fatan zuwan wannan rana ni Sumayya.

*🏤 NI DA GIDANA 🏤*

*_Littafi na daya_*

*NA*

*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

📱7
_______ Bayan watanni har biyar da korar Usman da Alhaji Rabi'u, hak'urina ya soma gazawa saboda Wata uku da suka wuce a ka soma gwab'amin da Zancen aure. Wai naki aure, duk sa'oina suna d'aki da yara d'aya ko biyu . Wai na fake da karatu. Wani lokacin kan Kawu na a ke jefa k'orafin, Wai shi ya huremin kunne na tsiri karatu domin kar nayi aure nayi nisa da shi. Saboda kowa ya lura da irin k'aunar da yake nunamin. Kuma a binda ya jawo matsalar, duk cikin dangin iyayena na kusa babu mai karatun jami'a mace. Kakana ma Sai da ya gwab'amin magana cikin hirar wasa yace, Wai na kusayin kwantai, saboda na tsaya ruwan ido da buri. Kakata Hajiya Mariya ita kullum naje k'orafin Kenan na aure. Itama kan Kawu Sulaiman ta d'ora laifin. Wani lokacin Hajiya Mariya fushi take yi sosai har takance. "To ya jik'aki ya shanye mana, tun da bayason kiyi aure. Na kan sake kunnata nace" Tsohuwar nan kin fiye rigima. Kinci zamani irin naki, ki barmu muma muci irin namu Mana, kai fa ya waye yanzu, karatu a ke fara zurfafawa kafin aure. To nan fa Sai ta balbaleni da fad'a har korata ma take yi tace kar na k'ara zuwa mata gida.

Amma Sai na koma. Baza'a rabu ba Sai mun kuma yin fad'an. Sai dai idan bata matsamin da zancen aure ba. To ban san me zasu ce ba ko zasu yi kuma, idan suka San ya kori masu zuwa neman aure na. Duk da hukuncin nasa Sam bai min dad'i ba nima, bazan iya suka ko tona komai na Kawu na ba da za'aga bak'insa ba. Ina tsananin k'aunar sa, bazan iya b'ata masa ba Ina sane.

Maganganun sun dameni lokacin da Usman ya aikomin da wasik'a a ciki yace wai naci a manar sa Ina sane, nasan wani za'a bani amma nayi masa alk'awarin aure. Ban ko bashi amsa ba na rabu da shi, saboda nasan kome zan fad'a masa bazai yarda ba. Alhaji Rabi'u kuwa, ban sake jin d'uriyar'sa ba shi.

Rannan Ina zaune a tsakar gida, Baba Talatu ta tafi unguwa. Ranar bani da karatu, a hutu muke. Komai ni nake yi dama in dai Ina gida, kuma ni nake sa kaina, bawai Baba Talatu ke cewa nayi ba. In dai ta ita ne wanke wanke Kawai zanyi da sharar tsakar gida. Na gama komai, Ina zaune, Kawu Sulaiman ya shigo, ya sameni zaune nayi shiru .

Ya jawo kujerar k'arfe da Baban'sa yake zama, ya zauna s gabana d'an daura dani.

"Sumayya a Kwai wani a bu da zakiyi yanzu?"

Nace"Babu Ancle. Sai girkin dare, kuma Sai yamma sosai zan d'ora,tun da mai sauk'ine."

Yace"Wannan damar nake jira da baki komai, kuma babu kowa Mu tattauna Wata magana dake. Kisa Nutsuwar nan taki da nasan ki da ita ki saurareni, ki kuma fahimceni 'yata".

Kafin nan zan baki wani d'an labari da Zai zama shine sharar fage,na a binda zamu tattauna."

"Kinsan ai Yarima ko? . Na dubeshi da hanzari, Sai ya zarce da cewa. Ko daya ke, Kinfi ganeshi da Fa'izu. Zan baki labarin'sa a tak'aice, bazan b'oye Miki komai ba, saboda Gaskiya da Gaskiya ce za'suyi aiki.

Yarima haifaffen garin nan ne, amma a salin'su 'yan maiduguri ne.
Mahaifiyar'ta sunan'ta Suwaida. Kuma k'abilar shuwa Arab ce . Baban'sa kuma babarbare ne, sunan'sa Alhaji Bukar, amma asalin'sa bafulatani ne na sokoto.
K'annen Fa'izu uku, biyu mata Sai namiji dake bi masa Khalifa. Tsiran'sa da Khalifa,shekaru uku yace min. Bad'an masu kud'i bane Yarima, ba kuma talakawa bane can. Sai sa Sai sa. Amma dai yawancin d'awainiyar gidan Yarima keyi, musamman na k'annen'sa mata. Muhibbat da khairat."

Yarima d'an boll ne sosai, domin kuwa makarantar school a cadamic yayi dake cikin k'asar Ghana kuma cikin birnin Ghana ACCRA. Suna koyar da boll ne da karatu. Tun tashin Fa'izu da son buga k'wallo ya taso, tun Yana k'arami, har girman'sa. Ya kuma samu sa'a a cikin harkar, ko nace yana kan samu. Iya boll d'insa yasa wani a gent dake hayowa 'Yan club club a turai k'wararrun 'yan boll, yace Zai kai shi spen wurin 'Yan club d'in bacelona, ko real Madrid dake k'asar turan ta spen su sayeshi. Saboda ya iya boll sosai Sumayya. Duk fita Sai yaci mana cup. Lamba Sha d'aya yake bugawa, Kinsan sune 'yan gaba, amfi ji dasu. Da yawa ma club Sukan gayyaceshi ya buga musu boll idan za'su gasa. To Sai yasa kan'sa dai yake zuwa, Kinsan halin Mutumin.

Yayi harkar Teaching na wani lokaci da yasa kan'sa. Amma fa ya watsar yanzu, saboda harkar boll tasha masa kai, kullum Samun ci gaba yake a cikin'ta.

Burin Fa'izu tafiya spen kawaI. Amma hanzu egent d'in dai bai nemeshi ba." Ni kuwa na kada baki nace.

"Ancle, mai yasa Sai yaje Wata k'asa? Yayi a garin'su Mana."

Yayi 'Yar dariya.

"Sumayya ai fitar sa k'asar turai shine ribar wahalar buga boll d'insa. Domin kuwa can ne ake Samun kud'i na fitar hankali. Kinsan idan ya taki wannan sa'a ya tsallake tudun mun tsira kuwa? Ko Kinsan a Kwai d'an boll d'in da yake d'aukar miliyan talatin duk Sati a k'asar turai?"
Nace cikin rik'e baki a rud'e.

"Duk Sati Ancle?".
"Sosai kuwa. A Kwai mai d'aukar Sama da haka Sumayya. Nan ma a na Samun k'ud'in musamman idan club ya shahara, amma ko kusa baza'a had'a shi da k'asar turai ba Kinsan yawancin kud'in ma daga wurin 'yan kallo a ke Samun yawan kud'in, to can turai, Mutum d'aya kika ji kud'in da zai biya ya Shiga kallon gasar k'wallo Sai ki rik'e baki. To Mutum miliyan nawa, ko Mutum d'ari nawa zasu Shiga kallon gasar boll na Wata Wata na k'ASA k'ASA, na cub club ke karawa da juna. Bari dai mubar Maganar boll, Mu tafi kan wacce a kanta za muyi magana.

Yarima yana da Wata budurwa da suke matuk'ar son juna mai suna Salima. Tana da kyau Wai ainun, a fad'in a bokin Yarima na hannun dama mai suna Hashim. Ni dai ban tab"a ganin'ta ba, Sai jin labari. Mak'otan Mune, suna zaune a Kaduna, cikin unguwar sarki.
Mahaifiyar Salima attajira ce, domin business take na saro furnitures daga k'asashen waje. Sun rabu da Mahaifin Salima, ta sake wani auren wani attajiri a unguwar malali. Amma Salima tana gaban'ta. Ita kad'aice 'yarta a duniya, tana son'ta kamar rai.
Salima tana da tarin masoya da yawa 'ya'yan attajiran gaske, amma Yarima take so kadai, kuma tasan wanene shi.Sun had'u da fa'izu a heal's and Bally da sallah. Shekarar su biyar Kenan suna soyayya.Wannan Shekarar Salima ta soma bautar k'asa. Maganar auren'ta ta taso, tace bata son kowa Sai Yarima. Mahaifiyar'ta ta nemi ganawa da Yarima.

Bayan gaisuwa tace masa me yayi tanadi, game da auren 'yarta, tun da yasan 'yarta ba irin gama garin 'yammata ba ce. Bai b'oye mata komai ba na matsayin'sa da kuma a binda yake yi. Amma yace yana da wani buri da yake so ya cimma. Kuma in dai ya cimmasa to komai da take so zai yiyu, amma yanzu haka bashi da wani shiri irin Wanda take nufi. Yace yana da dai dai arzik'insa Wanda Zai iya rik'e mace. Sannan gini yake yi ma yanzu ko rabi bai kaiba.

Nan Sai ce masa tayi.

"Haba Fa'izu! Yaushe zamu saka rai da a binda bashi da tabbas? Wayasan San'da wannan buri naka ma zai cika. K'arshe Salima tayi aure har tayi haife haife burin bai cika ba. Nama tabbatar Sai ta rigaka aure. Kai da kan'ka kasan Salima ba matar talaka bace, ko a talaucin ta taso, ballan'ta na ta taso, gidan iko. K'warya ai 'yar uwarta take bi, domin idan tabi a kushi kunya zata sha."

Yarima baya barin ta kwana, da anyi masa Zai mai da raddi.
Yace
Chapter 8 · 0% Book details