← Book details Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 31

Sashe 31

Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Khairat ta tafi da sauri. Tun da ta tafi, babu Wanda ya kuma magana. Ta dawo tace "Yaya ta rufe k'ofa, nayi nayi tak'i bud'ewa.
Ancle yace"Kice tazo babu a binda zan yi mata, Ina wurin Momi, magana Kawai za'ayi."

Momi kuma tace "Kice tazo in jini."
Nan nasan Muhibbat tana tsoron Yayan su sosai. Sai gasu kuwa tare, amma batabi ta kusa da Ancle ba, ta can baya tabi gefe, ta isa jikin Momi ta rab'e.

Ancle Fa'iz ya nutsu ya soma magana.

"Momi, bayan an gama hatsaniyar nan da safe , Khairat ta sameni a d'aki a kwance, tace min tazo za muyi Wata magana. Cikin fushi nace ta tafi ta bani wuri bani da lokaci.saboda cikin damuwa nake. Sai tace min ita ma Maganar a kan matsalar da ta faruce da ta dameni, tazo ta fad'amin gaskiyar lamari, saboda taga yin shirun ta b'oye matsala ce gagarima zata kunnu. Sannan tana so Sumayya ta fita daga zargin a binda bata ji ta gani ba. Idan yaso, kome Muhibbat da Khalifa za'su yi mata suyi, yafi sauk'i. Amma gata nan Momi ta sake fad'a kiji."

Sai naga Momi ta watsawa Khairat wani mugun kallo, amma ko kallon Momin bata yi ba, taci gaba da cewa.

"Gaskiya da kunne na naji Sanda Ya Khalifa da Ya Muhibbat suke tsara yarda zasu shiryawa Anti Sumayya wanan sharrin. Kuma Muhibbat ita ta tsarawa Khalifa komai, da yarda za'a aiwatar. Lokacin da suke tsarawa, a d'akin Khalifa, ni kuma nazo wucewa naji komai, amma Sai na bari suka ganni, ko saji tsoron aiwatarwa. Amma gargad'i Yaya Khalifa yayi min yace Wai Muddin na fad'a Sai ya kusa halakani. To gaskiya, banyi niyyar fad'a ba, Sai domin Anti Sumayya ta wanku daga mugun zargi, domin ta bani tsananin tausayi."

Nan naga idanun Ancle har sun soma sauya kala ga sabon su idan ransa yayi mugun b'aci.
Muhibbat naga yanayiwa wani kallo na tsantsar jin haushi da muguwar harara. Tabbas nasan darajar Momi taci da yasan zata kawo masa cikas wurin hukunta Muhibbat, da ta raina kanta a lokacin.

Yace "Mutuniyar banza, Wacce batasan nauyin hakkin cutar Mutum ba. Yau da a ce kin mutu da hakkin Sumayya, Wallahi da kin kad'e.Kaico ke dai da irin wannan mugun hali naki na mugunta bansan wa kika gado ba."

Da sauri Momi, ta katseshi. "Ya isa haka Fa'iz, idan ba za ka yi mata addu'a mai kyau ba, to Kayi shiru. Wanene baya aikata laifi?"

"Momi, Amma wannan fa k'ololuwa ne, yarinya kamar Muhibbat har ta iya shirya kaidi irin wannan, kamar Wacce tayi cos, a karatun iya shirya sharri, Sha Sha Sha wawiya mai tunani irin na mugwayen mutane."
Na lura Momi Bata so yakewa Muhibbat ma fad'a shi yasa ta sake katseshi tace "Ya isa haka. Komai ya wuce, tun da gaskiya ta bayyana. ama babu inda Maganar taje, an rufe kuma ba za.'a d'agata ba."
Ancle Dai bai bar Muhibbat ba a fusace yace "Sai ki bata Hak'uri. Da tayii Jim! Ya daka mata tsawa." Ba zaki bata hak'uri ba, Sai na kakkaryaki?"
Momi tace "Haba Fa'iz, Yaya kake uzzurawa Yarinyar nan ne, ba nace komai ya wuce ba?
Nasha Mamaki da bai saurari Momin ba, yayi kan Muhibbat gadan gadan,babu ta dubeni tace "Anti Sumayya kiyi hak'uri, ki yafemin. Bata tab'a cemun Anti ba Sai a ranar naci arzik'in Ancle.
Nace "Babu komai, tuni na yafe Muhibbat."
Ancle yaCE "Allah ya taimakeki, da so nayi na yi Miki dukan da Sai kinyi jinya, sakaran banza Mara hankali."
Momi dai Bata sake tankawa ba, amma fuskar nan babu annuri.

"Ke kuma Khairat cikin su ko kallob banza wani yayi Miki kizo ki fad'amin, Shima Khalifan zai zo muyi zube ban k'warya da shi, ba k'yaleshi nayi ba, a Kwai matakin da zan d'auka a kan sa, Sai ya gane kuskuransa.

Momi dai bata ji dad'in a binda d'anta yayi ba, dannewa tayi. Nan nima na Shiga neman a fuwar Momi a kan duk a binda nayi mata a Zaman Mu, cikin ladabi, da girmamawa. Nasan duk domin shawo kan ta Ancle yace nayi hakan. bata ko kalleni ba, tace a hankali
"Komai ya wuce." Ta manta da babina domin k'arar TV ta k'aro da ta ragewa sauti. Na jawo jiki na fito tun da an manta dani ma a wurin.

Ban jima da sauko wa ba, Ancle Fa'iz ya sauko Shima yace min
Zanje meeting na club, domin zamu buga Wata zazzafar boll a kusa, kuma daga nan zan je Wata unguwa ma"

Nace "Sai na ganka dai Ancle."
Yace "Zan yi k'OK'arin dawowa da wuri bazan yi dare ba, saboda yau muna da hira doguwa mai dad'i, So sweet." Ya huromin iskar bakinsa.

Murmushi nayi, domin ni ga zato hirar da nake k'ulafuci ce, wato ya bani lokaci muyi hira ko ba Wacce ta shafemu ba. Ina son na ganni ga Ancle Fa'iz muna hirar nishad'i da wasa da dariya. Babban burina ne wannan na duniya.

Bansan dalili ba, Sai naji zuciya ta ta d'an tsargu da Kishi, na unguwar da yace Zai je bai fad'amin ba. Kai tsaye zuciya ta ta zargamin cewa wurin Salima Zai je. Na. Tuno ko shekaran jiya da safe da na Shiga d'akin sa waya yake tayi da Salima, shi yasa na fito da sauri kar na jiyo a binda zuciya ta zata zafafa da Kishi.
Duk da Ina iya k'ok'arina wurin sarrafa zuciya ta wurin nuna kishin.
Chapter 31 · 0% Book details