← Book details Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 31

Sashe 3

Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Koni bawan ubanki ne, nake yi masa bautar koyar dake, baki isa ki dubi idona ki fad'amin wad'annan kalaman ba ki tsira. Saboda kin rainamin hankali zaki fad'amin wad'an nan lafuzan? Saboda jaka ce ke ko? Kuma a Ina kika zama senior? Kan ki fanko ne fa babu komi Sai tarin rubish. Simple topic irin wannan kika sa understanding?
Ballagaza dak'ik'iya irin ki Zaman gida, shi yafi dacewa dake. Mai makon Dai kizo a yi biyu babu. Ki wahalar da malami, ki kuma wahalar da kan ki, tun da k'wak'walwarki ta kifi ce
, ba fahimta za kiyi ba ma."

Intisar Kam ta muzanta a lokacin, Wai ita aka tozarta gaban wad'an da take ganin ta fisu. Za'ace ba'a tab'a ci mata mutunci ba a rayuwarta ma Sai ranar. Kuma namijin da take takawa.
Kasa cewa komai tayi, saboda yarda ta karanci zafin sa, idan ta sake tagawa, Sai a binda ta gani kuma. To bata tsaya nan ba, babban a binda ba'a tab'a yi mata ba, ranar an yi mata. Zafafan bulalai yayi mata da tafi ta kowa. A hannu yake bulalar sa, da tak'i tsayawa ne, ya k'arashe mata a jiki. Tasha kuka, Sai gata magiyar Hak'uri take bashi. Bai kuma saurara ba. Na yarda Fa'izu baisan kalmar hak'uri ba.Kowa bulala Sai da ya fito ya karb'a Kam. Amma biyar biyar, Sai dai ko Wacce d'aya Sai ka fad'awa mutan garin Ku. Yarda yake da zafi, haka ma bulalar'sa. Ni Amma na tsira, Sai d
ai na k'ara tsorata da lamarin malam Fa'izu.

Ai tun daga ranar kowa ya Shiga taitayin'sa da shi. Karatu babu wasa. Nutsuwar fahimta, kowa Sai da ya lalubo, idan ma baka da shi, to Sai ka aro. Tuni ya gyarawa marasa kunya zama da kuma dak'ik'ai , da yayi tambaya kuwa rige rigen bashi amsa ake yi.

"Yan a jin Mu da malamai ke masifar ji damu, to fa'izu yafi tsanar Mu shi. Yafi kuma takura Mana ma. Amma yana da hujja gareshi. A Kwai ranar da yace.

"Na fahimci kun d'auki kan Ku Wata tsiya, shi yasa kuka d'auki girman kai kuka d'orawa kan Ku. To zan saukar muku da shi kuwa."

Gaba d'aya makaran ta ta d'auka da Fa'izu Bukar,ko'Ina ka zaga Zancen sa. Makaranta tuni ta soma gyaruwa, saboda matsayin displine master a ka bashi, saboda jajircewar sa wurin kawo gyara a makarantar. Ya gyara makaranta Kam, ko ga tsafta da tarwatsa Zaman da malamai suke na hira a k'i Shiga a ji koyarwa. Meeting na dole yasa a Kayi harda prince pal aka kawo sauye sauye. Ko a makararru ma an samu sauk'i sosai. Domin Sai a jima ma ba'asamu wad'anda za'a tare ba da sunan makara.
Saboda malam Fa'iz ke hukuntawa. Kuma babu sauk'i ko a fuwa a lamarin sa, ko wacece ke zaneki zai yi tas kuwa. Kuma idan zaki d'ige kina bashi hak'uri bazai hak'ure ba. Bada Hak'urin ma shi fusata shi yake yi. Tofa!. A Watan'sa na biyar nima na fad'a komar sa. Dama yayi min baki.

Garin tsautsayi rannan Sai gani cikin makararru guda biyar. Zance tsautsayi, tun da ban tab'a makara ba.
Abinka da matsoraciya. Jiki har rawa yake Ina bashi Hak'uri da yazo kaina ya rik'e baki.

"Cab' , monita kina shugabar d'alibai amma kika makara? Muk'amin ki bashi da wani amfani, tun da ke shugaba mai gyara kin gaza wazai gyaru kuma?"

"Wallahi sir ban tab'a makara ba, yau ma akasi a kasamu na tuba, bazan k'araba."

Yace"Kome zaki ce ba zaki tsira ba Wallahi. Kuma bulalarki Sai ta ninka tun da shugabanci aka baki ga 'yan baya, dole muna so ki ki yaye.
Zafafan bulalai goma yayi min da naji kamar na shid'e domin zafi. hak'uri da nake bashi naga kamar tunzurashi ma nake, shi yasa na hak'ure. Hannaye na har tara jini suka yi bayan kumbura. Na yarda Fa'iz mugu ne na k'arshe. Da gayya ma nasan yayi min irin wannan bulalar mai ratsa k'ashi. Tabbas Sai a lokacin na yarda da zafin bulalar sa da d'alibai ke fad'a suna tsoro. Tun daga ranar naji na tsaneshi. Tun da uwata ta kawoni Duniya Kam ba'a tab'ayi min bulala ba nima ballantana mai zafi irin wannan. K'udirewa nayi a raina na daina yi masa magana ko a aji.Amma daga baya dole na saddak'ar, saboda malam Fa'zu yafi gaban nan. Tambaya ma baka amsa masa ba, hukunci ne mai zafi. Domin kuwa ko zagin'sa na tsamar nama yayi maka ma bainan nasi, ya cuceka.

Ga dai intisar nan duk tayi laushi ta horu. Duk rashin kunyar nan da felek'e ta dire. Muddin ya shigo class Wata nutsuwa ma take yi. Amma a jita jita naji Wai son sa take kuma. Bama ita ba ya kwashi Jama'a masoya mata jingim, amma na b'oye. Tun da dai kota Ina babu Wata alama da ta nuna Fa'zu Bukar Zai karb'I tayin k'ok'on barar Soyayyar wata mace a makarantar, face ma Sai dai yayi fatali da k'ok'on barar. Ni Kam duk Wacce zata so ma Fa'iz wahalalliya na d'auketa, Wacce kuma aka yankawa kazar wahala a kace Sai ta fige.wahala bata ishe suba ne da wulak'anci suke neman k'ari. Haka nake cewa duk Wacce aka cemin ta Mato a kan son Fa'izu Bukar.

*🏤 NI DA GIDANA 🏤*

*_Littafi na daya_*

*NA*

*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

📱3
________ Ban kuma yarda ta had'oni da malam Fa'izu ba, gudun inda zan ganshi ma nake yi idan ba 'ajin Mu ya shigo ba. Duk domin kar ya kamani da laifin da zai ci zalina, saboda na daku, jikina bai manta ba. Kuma kumburin hannu n'a bai gama Sab'ewa ba. Amma duk guduna da shi, Sai da rannan ta sake had'oni da shi. Rannan na Shiga staff room Kiran malam labahani saboda period d'in sa ta Shiga bai zoba.

Ina Shiga staff room bisa tsautsayi idanu na da malam Fa'izu suka fara kicib'is. Suna zaune shida malam Abba da na fuskanci tasu tafi zuwa d'aya suna cin gyad'a. Malam Abba yana kan desk d'in da suka zube gad'ar, shi kuma malam Fa'izu yana kan kujera, suna hira har suna 'yar dariya ma. A raina nace. Dama malam Fa'izu yana dariya? Zatona ko murmushi bai iya ba. Da wuya ma naje staff room na ganshi Sai Jifa Jifa idan bashi da class, saboda a Kwai himma a wurin sa wurin kula da karantar da d'alibai.

Muna had'a idanu da shi kuwa, ya wani d'aure fuska, ya kuma sakar min wani uban muzurai.

"Zonan ke monita"
Jiki na rawa na isa garesu. "Gidan'Ku ba'a koyar da tarbiyya ne?" Yace , bayan ya jefa gyad'ar da ya murje bakin sa. Na Shiga dawurwura saboda bansan laifin da nayi ba, Sai da malam Abba yace min.
"Tsuguna Mana Sumayya. Ya kiraki kuma kin zo kin tsaya Mana a ka." Nan na fahimci Laifina, Amma ni shi duk ya gigitani. Ganin Fa'izu Kawai tsorata nake.

Malam Fa'izu batare da ya ko kalleni ba yace.
"Sintirin me kike damun Mu da shi a staff room? Kullum kina kan hanyar zuwa nan? Uban me yake kawoki matattarar malamai?"
Na sunkuyar da kai sannan nace.

"Malami nake kira idan period d'in sa ta Shiga bai shigo ba".

Ya tsaya da cin gyad'ar cikin d'aga murya da fusata yace.

"Wayace Miki aikin ki na monita yana cikin haka? Hak'k'in ki ne Kiran malami, ko Hak'k'in malami ne yazo teaching da kan'sa?" Ba suna da time table ba ma?" Nayi tsuru tsuru da ni nak'i magana, gudun nayi laifin da zai casani. Tuni duk kallon malaman dake staff room yayi yo kan Mu, saboda yawancin malaman suna hallare. Da k'arfi Fa'izu yake magana, kuma nasan domin sujine, domin babu Wanda yake shakka, Sai ma su da suke shakkarsa, har ma da prince pal, da vice prince pal.saboda bayan zafin sa,ya tab'a cewa a kunne na da suna hira da malam Abba bayan staff room da zan wuce ta window, cewa yaja kunne a meeting domin kowa yayi hattara, na yana da hanyar da zai kai k'ara ma'aikatar ilimi ga shugaban kula da matafiyar ilimi na k'asa, in dai shugaba da malamai suka ci gaba da cin albashi a b'agas babu kula da hak'k'okin aikin su.

Malam Fa'izu ya dubeni cikin fushi.

"Kar ki sake na k'ara ganin k'afarki a staff room da niyyar Kiran wani malami. Wallahi na sake ganin ki? zaki fuskanci hukunci na ban Mamaki. Ihope you get it?

Na jinjina kai.

"Kin fahimta nace? Talk to me."

Na gyad'a kai da sauri.

"Na fahimta, sorry sir."

Yaci gaba kallo ga malamai da suka kafa Mana idanu.

"Albashi a na biyan kowa duk month mai nauyi kowa ya lamushe cikin jin dad'i amma ace Wai Mutum baisan time d'in aikin sa bama Sai an kirashi? Why? Is not fair gaskiya. Menene amfanin time table da agogo Kenan?
zamu sake zama da prince pal da teachers dole a yi gyara."

Babu Wanda ya iya cewa kanzil kuwa, saboda gaskiya ya fad'i da ba kowa zai iya bugar k'irji ba ya fad'I, Sai irin sa Mara tsoro mai dakakkiyar zuciya kuma.
Chapter 3 · 0% Book details