← Book details Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 31

Sashe 11

Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bazan yarda burina ya rushe ba. Tuni zuciya ta ta tsaramin, yarda nake son rayuwar aure na ta kasance. Rayuwa nake so, sosai ta soyayya da nishad'i da walwala, da farin ciki, da fahimta. Na tabbatar na auri Ancle Fa'izu duk sun rushe. Ballantana ma Wai auren wucin gadi, yake so nayi,Wanda Zai k'are kusa ne, nesa ne ban Sani ba, shi ya Sani. Abinda na Sani, ni Zai Cuta Kawai. Domin na tabbatar ko wani abu bai ratsa tsakanina na aure da shi ba, tilas ya sakeni kallon bazawara za'ayi min. Ban isa na goge tambarin zawarci a goshi na ba a idon mutane. Ga zato mummuna da za'ayi min a ce bani da hali ne. Dad'i ma samarina na baya suyi min dariya, da Allah ya k'ara, tun da ga zaton'su ni mayaudariya ce. Mak'iya na su samu hak'oran yi min dariya. Bani da abokin fad'a Sam. Amma duk Mutum nasan baya rasa masoya da Mak'iya.
Nasan kuma Kawu Sulaiman bashi da masaniyar nufin Yariman'sa. Nasan ko giyar wake yasha, bazai so nayi irin wannan auren ba. Dad'i ma naji daga baya, da yake bani da hak'k'in Yarima, gashi ya fad'a min k'udirin'sa kafin aure. Kenan na Samun hujjar ya kice auren cikin ruwan sanyi. Sai dai idan
Kawu Sulaiman bai ji ba. Dole kuwa yajin.

A d'akin Kawu Sulaiman, Ina rakab'e bakin k'ofa, shi ya fara magana kafin na fara,kamar yarda naso.
"Abinda kika yi, dole ya b'ataran Yarima, saboda shifa wayayye ne sosai, mai son harka ta Wayewa. Ballan,tana shi da ya sabayin hira da wayayya gogaggiya mai babban a ji irin Salima, dole ki sik'eshi.Bai kamata ki rikid'e masa ga siffar da nima nasan ba taki bace Sumayya .wani daliline a ranki, kika yi masa haka ko? Sannan domin k'arin kwab'a kika yi tafiyar'ki baku ko yi sallama ba. Menene damuwarki Sumayya?"

Wannan damar nake jira.

"Kawu, ni Wallahi halin'sa bazan iya da shi ba. Ko a makaran'ta tsoron karo da shi nake. Abu k'arami, Sai ya tozarta Mutum. Ka gani ma da idanun ka Kawu, gaban'ka ya rink'a yab'amin maganganu, ko nauyin'ka bai jiba.
Ya katseni da hannu.

"Da Kinsan Yarima sosai, da fahimtar'sa bazaki yi wannan k'orafi ba."
Na fahimci kamar Kariya kawuna Sulaiman yake bashi ma, shi yasa na fito masa da da Zancen da idan yaji, Sai ya zargeshi.

"Ancle Fa'izu fa cewa yayi aure na Zai yi na wani lokaci ya sakeni Kawu, saboda cikar burin'sa. Wallahi ya fad"a kaji na rantse."

Ga mamakina Wai Kawu nan nan ma bai damu da furucin Yariman'sa ba, da manufar'sa.

"Karki damu da Abinda ya fad'a. Ikon komai da tabbatar komai yana hannun ubangiji. Zukatan bayi, yana hannun ubangiji, shi yake sarrafasu yarda yaso. Saboda haka karki damu da komai. Ke ki nufi auren Ku, da kyakykyawan zato,da niyya mai kyau, da kuma kyakykywar addu'a zaki dace.za kuma ki a mintu daga a binda kike fargaba Sumayya. Ba kya gani, ko Mutum ne, ya nufeka da mugun nufi, kai kuma ka nufeshi da zuciyar alkhairi, sharrin'sa bayayin tasiri a gareka? Karki turje, kan wasu a bubuwa marasa tabbas d'in d'orewa, ki yasar da a binda yafi alkhairi a gareki, baki Sani ba. Ki dubama yarda k'addara take ta had'aki da Yarima, Ku had'u Ku rabu, Ku sake had'uwa.Sannan ni da nafi kowa son'ki a yanzu, ubangiji ya jarrabi Zuciyata da son ki auri Yarima. Kuma Sam, bana k'aunar a binda Zai kawo cikas a auren. Gani nake, Yarima shine kad'ai ni ya dace da rayuwarki a Duniya kaf Sumayya. Shine kuma Wanda nake jin Zai rik'emin a manarki ko bayan raina. Jikina ke fad'amin haka Sumayya. Sai auren ya gabato, zan fad'amiki dalilan da yasa na nace da aurenki da Yarima. Ban kuma damu da yana son'ki ko baya son'ki ba. Ke da kan'ki baki Sha Mamaki da ya amince da auren'ki ba? Aikin k'addara Kenan.Hakan na nufin fa, ke k'addarar cikin rayuwarsa ce. Wannan bai sheki ishara ba? In da na barki, kema auren rashin soyayya zaki yi da d'aya daga cikin masu son aurenki. Tun da haka ne, ki jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya Mana. Ki auri Yarima domin dalilai da zan fad'a Miki su a gaba. Kuma ki yarda shi k'addarar rayuwarki ne, da bakisan me Allah ya shirya muku ba, ki aure shi saboda wannan. Ni dai ya fiyemin tarkacen samarin ki sau d'ari. Domin nasan komai a kan'sa, usuli da halayan'sa. Na gani, kuma naji a majiya ta gaskiya.Amma nasan ba lallai ki yarda da shi ba har zuci yanzu, saboda kallon wasu halaye na zahiri da kike masa. Amma a Kwai na bad'ini da bakisan da su ba. Shi yasa kike gani baza ki iya da shi ba. Tabbas zaki iya zama da Yarima, matuk'ar kika fahimceshi, kuma kika kiyaye a binda yakeso da wan"da baya so. Nasan ko baki gwanance ba, zaki iya koyawa zuciyarki, ki jure kiyi. Saboda kina da hak'uri da biyayya. Kuma ki Sani, idan ma kink'i auren'sa ba damuwa Zai yi ba, ba kuma hak'ura Zai yi ba da auren cimma Wata manufa ba. Wata Zai samu ya aura. To ita Watan kina zaton irinki ce mai kyawun zuciya da zata ceto shi daga yin kuskuren da yake son aikatawa, nayin auren wucin gadi? Ke kuwa nasan ko baki taimakeshi da komai ba, zaki taimakeshi, da nasiha da addu'a. Sanin kan'kine yin aure da niyyar Saki daga baya saboda Wata manufa, haramun ne. Kika yi kandagarkin hana afkuwar hakan bakiyi babban aikin Lada ba Sumayya? Naji jikina yayi sanyi Lis, da furutan Kawu. Tabbas Gaskiya ya fad'i , a binda nake shakkar yiyuwar, na yarda Ancle Fa'izu zai karb'i nasiha daga gareni, ko shawara. A yarda yake ji da kan'sa, ni kuma yake ganina a raine?
Kawu yace
"Kuma ki rink'a nuna kulawarki wurin mahaifiyar'sa, domin yana tsananin son'ta. Zan iya ce Miki nan ne sirrin farin cikin'sa. Ki soma d'ana tarkon'ki tanan. Ki kula, NAN FARIN CIKIN'SA YAKE.
ni na sake jaddada wannan a raina, har sau uku ma.
Da wad'an nan kalamai Kawu Sulaiman ya sake farauto Zuciyata ta a minta da auren Ancle Fa'izu. Amma fa ban daina farga ba ba, da zullumin auren. Tabbas ba domin na yarda da irin K'aunar da kawuna kemin ba, cewa zanyi farin cikin rayuwata ne baya so, yace na auri Ancle Fa'izu.

*🏤 NI DA GIDANA 🏤*

*_Littafi na daya_*

*NA*

*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

📱 10
________ Nayi sauri na fito daga d'aki, na karb'e tsintsiyar da Baba talatu, ta soma Shara da ita. Bata Musa ba, ta sakar min. Sai da na share ko Ina na cikin gidan tas!. Na had'o Kayan wanke wanke zan'yi Sannan tace"Ke dai Sumayya bakison kiga nayi komai, in dai kina gidan nan."
Nace.
"To, Baba Talatu, kina da kamata kiyi aiki? aiko tsari babu. Kiyi kwanciyarki, nayi aiki nayi kuma girki, Sai dai Kawai na kawo miki kici. In dai Ina gidan nan baza kiyi aiki ba."
Tace
"Koda a Kwai d'iya irin'ki mai kyawun hali, gaskiya k'alline. Kina da kyawun d'abi,a Sumayya, ga biyayya, ga tausayi. Ta Yaya kuwa bakina zai gajiya da sa miki albarka? da Fata na gari. In Sha'Allah Sai kin haifi masu binki, kuma Sai kin gwangwaje Miji na alfahari. Saboda kowa ya bud'i baki a kan'ki fata na gari ne. Addu'ar iyaye da 'yan uwa kullum bibiyarki za tayi tayi."

Tuni na saba da lafazan Baba Talatu dad'ad'a, kullum ne bata gajiya.

Tsawon kwana tara, ban sake ganin ko inuwar Ancle Fa'izu ba, ga wawtata farin ciki na Shiga sosai, a zatona ai ba zai iya dani d'in ba ne, kamar yarda yace, shi yasa ya janye.

A tsukin aka sake gayyatar k'ungiyar su Kawu sulaiman Kaduna united zuwa ga buga boll, cikin k'asar Enugu, za'su kara da club d'in Ranger's.
Nan ma su Kawu nane suka cinye. Ya bugo min waya, cike da farin ciki Yana mai shaidamin, dama sau biyu muna waya da shi, bayan tafiyar'su. Nasan da Ancle Fa'izu suka tafi, amma ko Zancen'sa bai yi ba, nima banyi ba.
Na fiddaran hakan, Sai ji nayi Ancle d'ina yace.

"Ga Ancle Fa'izu zan kai masa ku gaisa, kuma kiyi masa murna, domin shi Yaci Mana k'wallon nasarar guda biyu. Yana resting room amma na barshi yana shan mutuniyar tasa multina, bari na kai masa.

Da sauri nace
"Don Allah Kawu ka rabu da shi, basai munyi magana ba, kace Ina yi masa murna Kawai. Yace
"Zai fi kyau ki kira wayar'sa Ki fad'i masa. Idan baki da ita zan turo Miki. Nayi d'an Jim, daga bisani nace
"Ina jin nauyin hakan, Ancle. Naga shi ya kamata a ce yama nemi sanin lambata, ya kirani, amma bai yi ba. Shi yasa nake ganin kamar zan karyar da kaina idan na fara. Amma idan kace na kirashi, zan kirashin."

Yace
"A'a. Rabu da shi Kawai, na fad'a masa. Kinsan dai komai a kan'sa. Kinga kuwa komai ba zai shige Miki duhun menene dalili ba. Kinsan dole zaki rink'a had'uwa da irin haka, amma kiyi hak'uri wataran Sai labari kinji shalelen. Ni da shi mukayi 'yar dariya.

"Gaskiya Ina son Kawu Sulaiman, har bansan adadi ba, ko misali.

Kwanan'su d'aya tal da dawowa kawuna yace min.
"Sumayya, yau Yarima zai zo. Don Allah, ki kula a komai, kar ki bani kunya kuma. Ki canza"
Nace
"To, Kawu zan yi bakin iyawa ta" yaji dadi.
Na samu kaina da tsala kwalliya da ado fiye da farkon zuwan'sa sosai. Less nasa mai kyau, da nasan Ina kyau a ciki.
Chapter 11 · 0% Book details