← Book details Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 31

Sashe 22

Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da yamma Lis, na taso daga makaranta da wuri saboda lacture ta ranar gajeriya ce na bud'e d'akin nasa. Gaban su Muhibbat da Khairat suna hira, suka bini da kallo. Gyara nayi masa sosai. Dakin a share yake tas, amma a Kwai 'yar k'ura jikin sib da wardrobe. Na k'alk'ale komai . Na cire zanin gadon nasa masa sabo gau, nawa. Haka ma labule na cire nasa masa nawa mai kyau. Nasan ma mai kyau ne, amma nawa sabone ful, domin kala biyu ne dani masu tsada. Zanin gado kuma kala uku. Na tsara masa Kayan cikin kwabar sa, na jera,saboda yana yawan hautsinawa ya barsu garin binciken kaya. Nayi masa gyaran da bazai rinka hautsina komai ba, komai dalla dalla. Na ware under's d'insa da singlet da gajerun wanduna, har da Kayan boll da babu wanki na kai d'akina na a jiye da niyyar gobe na wanke.
Na fesa masa air freshner Sama Sama, kar yayi min k'orafin turare ya hau masa kai. Shi yasa ma ban k'ara da turaren wuta ba. Dakin nasa yayi kyau sosai kamar ba shi ba. Da yake falon ma babu tarkace, kujerune hudu one seater, sai TV dake jikin bango da risiba.
Wata laptop d'in Ancle na gani madaidaiciya ta d'au hankalina na bud'e. Tabbas da nasan me zan yi tozali da shi, da ban bud'e ba. Hoton Salima ne da Ancle Fa'iz ya cika fuskar laptop d'in. Suna jikin juna, Salima ta kwanto a jikinsa ya tallafota da hannayensa ya mannata gam a jikinsa. Tamkar mata da Miji. Abin ya d'aure min kai, dama Ancle Fa'iz zai iya haka? Ko kuwa soyayyarce duk ta zautar da shi, ya biyewa hud'ubar shaid'an?. Sai da na daure zuciya na sake kallon hoton. Su duka murmushi suke yi a hoton. Sai da nayi tasbihi ga mahaliccin surorin'su. Ita da shi d'in babu kanwar lasa wurin kyau. Sun dace da juna Kam in dai wurin duba ne.idan kuwa suka tashi haihuwa,wad'anne irin kyawawan yara za'su haifa. Za'a Sha kallo.

Ko shakka Ancle Fa'iz yana son Salima sosai. Kusan duk wani abu nasa mai muhimmanci hotonta ne a kai. Wayoyin sa biyu ne banason gani ma, Saboda duk hoton Salima ne. Da dai da key holder dinsa na d'aki hoton Salima ne, k'arami a ciki anyi masa siffar zuciya. Lallai Ina da gagarimin aiki a gabana, tun da ko makami na yak'i daya ban mallakaba, na satar zuciyar Mijin da muka kusa tarayya da Salima. Tayi min fintin kau na k'wace Miji tuni. Tun da familyn sa ma duk mayak'anta ne na fagen daga. Gashi kullum kuma k'ara zarmewa nake cikin Soyayyar Ancle Fa'iz. Shi yasa kullum kishin sa ma k'aruwa yake a raina, duk da bai a jiyeni a rukunin mata ba ma. Ba domin na tabbatar Sai mun d'ebi 'Yan kallo da shi ba, da Sai na rotsa laptop d'in nan. To laifi kan laifi ma zanyi. Na shigo masa muhalli bai Sani ba, kuma nayi masa tsadadden ta'adi. Nan ma cewa zai yi lek'en a Siri ya kaini. Wannan hoton, ko ba'ace ba, nasan yana ji dashi.

Da na fito daga d'akin Ina rufe komai, Momi da Muhibbat na gani daga saman bene sun kafa min idanu, nayi kamar bangan su ba. Nasan Muhibbat ta kai mata tsurku.

Fuskar'sa d'auke da alamomin Mamaki ya shigomin. Hannun sa ya dafe kujera yana daga tsaye yace min.

"Wa ki ka ga ya shigar min d'akina?"
Kamar da gaske na dake

"Anya an Shiga d'akinka kuwa yau Ancle? Wani a bune ya faru?"

Yaja dogon numfashi.

"Tabbas an Shiga an jima, domin komai na d'akin ya canza. An canzamin tsarin komai na wurin. Wanene mai wannan aiki, ko nace wacece?"
Na kanne cikin b'oye dariyar dake son k'wacemin.

"Ta'adi a Kayi Maka Ancle?"
Yace"Gyara a Kayi, tun da wurin ya k'ara haskaka yayi kyau.
Naji dad'i sosai na yabon da yayi. Ancle Fa'iz kafin ya yaba abu a ya'ra.

Saboda Jan zare, na zolayeshi da cewa.
"Ancle, Ina Jifa aljanun cikin d'akinka ke sonka, suka yi Maka gyara."

Yayi min k'Uri da idanu, har Sai da naji wani abu mai hargitsa yanayi ya nisa tukun yace.
"In dai haka ne, to Kece shugabar aljanun, ke kika jagorance su."

Dariya nasa ta burgewa. Wato ya fahimci ni nayi masa dai gyaran.
"Ina kika samu mukullin d'akina? Yace
Nace
"Jikin mukullayenka na cira."
Nayi zaton Zai min fad'a, amma Sai naji yayi shiru.Na fahimci yaji dad'in gyaran da nayi masa a fuska. Duk da kullum nunawa yake baya so nayi.
*🏤 NI DA GIDANA 🏤*

*_Littafi na daya_*

*NA*

*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

📱18
_______ Tamkar kaska haka na Mak'alewa Ancle Fa'iz. Domin takai ko bai shigo d'akina ba, ni zan bishi nasa d'akin, bana kuma shayi, ko fargabar mutanen gidan. Tuni na soma yin sabo da shan zagi, harara, habaici da zund'e. Shi yasa idan ma anyi min, bana d'aukar'su a bak'on al'amari da zai yi ta damuna. Wannan yasa zuciya ta ma ta kangare ta bushe, domin idanuna sun rufe da Soyayyar Ancle da bin hanyoyin da zan janyo ra'ayin'sa gareni. Duk da Shima Ancle Fa'iz d'in Ina shan wuyar sarrafashi wurin shishshige masan da nake yi. Yakan nunamin ma k'arara cewa na ta kuramasa, amma Sai na shanye.

Bayan Ancle Fa'iz ya sauko daga saman Momi, ya sameni zaune a d'akin'sa Ina dakon'sa.
Ya samu wuri ya zauna, ya fara da cire hular kan'sa. Nayi zaraf na d'auka, nasa a kaina na dubeshi nace.

"Ancle tayi min kyau?".

Ya jefeni da kallo d'aya na gefen ido yace.

"Ke namiji ce da hula za'ta yi miki kyau?".

Sai na cire daga kaina nasa masa a kan'sa. Ya cire ya ajiye. Na sake d'auka na rik'e nace
"Wallahi hula ba k'aramin kyau take yi Maka ba, my Ancle."
Yace "Ko?"
Na sake saka masa a kan'sa, ya kuwa cire da sauri yace.

"Wai yaya haka ne, Ina cirewa kina samin?"
Nace "To, ni nafi son ganin ka da hular, kafi kyau Allah"

Wannan Karon wani murmushi naga yayi Maimakon hasala, yace "Sumayya, kina fa takuramin kwanan nan. Yarinya duk kin bi, kin hanani sakat? bulala Allah zan a jiye kusa dani. Surutun da kike Sani banyi niyya ba, yayi yawa."

Nace "Barewa fa a dawa ance da d'anta take wasa Ancle Fa'iz. Kaman ta bani da kowa Sai kai? Kaine uwa, kaine uba, kaine Kawu, kaine Yayana kaine....."

Ya da katar dani da hannu "Ya isa !. Ke kin fiye Surutu, Sai kace aku kuturu."
In da sabo na saba da irin wad'an nan lafazai nasa. Kuma a hakan muke ci gaba da hirar bana fushi kamar kullum.

Ranar dai na ganshi cikin walwala dai, Bansan dalilin ba. Ya nutsu ya soma cemin.

"Ki ta yani murna, na samu shigowar wasu kud'ad'e masu yawa na wasu wasanni da muka yi a state uku, Sai jiya aka turomin nawa cikin a count. Ban tab'a Samun kud'i masu yawa a wasa ba irin wannan. Nayi kasafin su ma. Na wari Wanda zan ba Momi da Baba, na wari Wanda zan Sai mota, domin tana cikin tsari na. Sannan ragowar zan k'ara cikin harkar ginina da kullum cin kud'i yake"

Naji dad'i sosai da na samu matsayin da ya fad'amin sirrin ci gaban'sa. Na kuma yi ta surfamasa godiya da addu'a na kyautar kud'in da zai ba iyayen'sa, Sai a zaci nawa iyayen zai bawa.

"Wallahi ka kyauta Ancle Fa'iz, musamman alkhairi na kyautatawa ga iyaye yafi kowanne. Allah ya saka da alkhairi, ya k'ara bud'i"
Ya gyara zama daga kishin gid'ar da yayi yace

"Kema za'a baki Lada na ganin ido, kamar 'yar dubu goma, tayi?"
Nayi masa murmushi

"Wanda za'a ba kyauta har yana da zab'i? aiko naira goma ka bani godiya zan yi tayi, ballantana har dubu goma Ancle?"

Ya kanne ido guda cikin dubana yace.

"Na lura, kina da Yakanah! Saboda haka bari a k'ara Miki dubu goma su zama twenty thausand. Godiya nayi ta surfawa da addu'a."
Yace"Ya isa haka Sumayya, Sai kace kyautar rai na baki?"

Na kau da wannan , nace

"Ancle Wai kuwa wacece Anti Husna da naji su Khairat suna yawan fad'e?"
Yace"K'Anwar Momi ce, ita ce autar su.
"To, Ancle Jamil fa?"
Yace"Yayan Momi ne"
Na sake cewa "Maman fahad fa?"

Cikin nuna 'yar k'osawa yace

"K'anwar Babar Momi ce, Kenan uwa take a wurin Momi. Na gaji Sumayya, tashi Kije ki kwanta, bacci zanyi."

Nace"Abin har da kora my Ancle?"

Yace"Wanzami dama ba yason jarfa, ni me yasa jiya kika koroni daga d'akinki?"

Cikin 'yar dariya nace"Au, daga kayi bacci na tasheka nace kaje ka Mik'e a gado.?"

Yayi doguwar hamma kafin yace "Wannan a bu duk mai sauki ne, idan baki son tafiya, nan d'akin yayi miki, Sai na kawo miki guzurin filo, ba Shike nan ba?"

Na kuwa ce "Kawo min"

Sai kuwa naga ya tashi, ya shige ainihin cikin d'akin, nan nasan da gaske yake. Kafin ya fito kuwa na arce.

********

A tsukin cikin wata uku da aure na da Ancle Fa'iz, a bubuwa sun soma zuwa min yarda nake so. A lokacin ne kuma na sake Shiga tsangwama da takura da fitintunu a cikin gidan, saboda sun fuskanci muna d'an d'asawa da Mijina, yana nunamin kulawa fiye da da. Kwana ne Kawai Ancle bayayi a d'akina, amma har a binci tare muke ci, idan ya shigo d'akina. Kuma ni na gadar masa da hakan, domin ko shi kad'ai ya soma ci, Sai na zo na sashi a gaba,nima na soma ci, muci gaba da CI tare. Ko a bincin Momi ne kuwa, domin naci na yasa kullum Sai yaci nawa. Shi yasa baya cika cikin'sa ma da a bincin Momi, saboda yasan nawa d'an k'a'ida yana jiran'sa.

Wulak'anci da cin mutunci muraran a ka Shiga yi min a gidan, da Kare ma ba zai ci ba.
Chapter 22 · 0% Book details