← Book details Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 31

Sashe 18

Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace"Koma wani iri kiyi amfani da shi, amma d'an kad'an zaki sa. Yayi a jiyar zuciya ya zarce.
Dazun Salima ce tazo gidan nan. Ina wanka naji sallamarta. Shi yasa Ina jin ta hau benen Momi, ni kuma da na fito daga wanka shine nayi sauri na shigo d'akinki. Saboda nasan Momi zata tilastani da cewa,na bita Muje wurin mamanta, saboda ta turo kirana har sau uku nak'i zuwa. Tayi laushi tayi nadama sosai, ni take ta zabarin nema nazo ta bani Hak'Uri na auri 'yarta, batasan ta makaro ba. In dai nine to Wallahi ba ta ma soma nadama ba.
Sai jiyan Salima da yamma ta samu labarin aure na dake, domin mamanta b'oye mata tayi a she a son samunta Sai an nemoni an dai daita komai, Sai Salima ta Sani, saboda tasan taga katin auren ma ba k'aramin hauka zata yi musu ba. To jiya ta samu labari, ta tashi hankalin su. Ta nemeni a waya na fad'a mata a binda mamanta tayi min. Kuka ta rink'ayi min sosai, Wai banyi mata a dalci ba da tun farko na rufeta. Wai ai babanta yana raye ai shi Sai ya d'aura Mana aure. Amma Yaya zanyi aure? Ina nake ta tsoma rayuwarta. Ko Ina zaton zata iya rayuwa babu ni. Ke surutai kala kala. Jiya ma cikin dare ta kirani a waya tana kuka da surutai. Gaba d'aya daren jiya ban samu bacci ba fa. Kiran waya, babu Hutu. Lallashin Duniya nayi domin ta fahimci bawai na barta Kenan ba, Ina sonta, kuma Ina da burin auren ta, amma da sauran lokaci. Kuma auren da nayi duk Sabida ita ne, domin idan ban tauna tsakuwa a ya taji tsoro ba, al'amari Bazai gyaru ba. Amma Salima fafur ta kasa fahimtata. Da gaji na kashe waya. Shine fa kika ga tazo da safen nan, Wai mamanta tazo ta tafi dani, saboda ta gigita nutsuwar su."

Duk da fargaba ta rufeni da jin a binda ya faru, da nima zance ya shafeni dole. Cikin taushin murya nace
"Ancle, Kayi Hak'Uri Mana kai ma. Tayi nadama fa maman nata. Kuma naga burinka Kenan. Kayi Hak'Uri."

Ai gani nayi, ya Mik'e zaune sosai ya dubeni.

"What? Nayi me? Wai nayu Hak'Uri yanzu? Lallai Yarinya baki sanni ba, labarina kike ji."

A raina nace"Ban dai gama sanin ka ba.

"Wa'adin da na yankar mata Wallahi Sai ya cika. Ina son Salima. Ina son 'yarta fiye da zaton su. Amma Wallahi ban shirya auren'ta yanzu ba, ko da kuwa za'a tattaromin kud'in masu arzik'in k'asan nan a bani a matsayin gudun mawar aurenta. Wallahi bazan aure ta ba Sai wa'adin da na d'ibar musu ya cika.

Nan nasan lallai Ancle Fa'iz ya wuce sanina da karatuna. Zuciyar da Kawu Sulaiman yace yana da ita, ta wuce zatona. Amma a hakan kullum zuciyta k'ara zarmewa take a son sa, duk da zahirin halayan'sa masu wuyar Sha'ani da juriya, suna dad'a tallata kan"su da kan"su. Wannan bai hana Soyayyarsa k'araci gaba da hab'aka a raina ba. Wuyarta Mu kwana Mu tashi, nayi ido hud'u da shi, naji muryarsa kuma.

*🏤 NI DA GIDANA 🏤*

*_Littafi na daya_*

*NA*

*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

📱15
______ Zan iya cewa, tun da daga ranar nan, gaba d'aya naga gidan sun sauyamin fuska, idan a ka cire Khairat, da Ancle Fa'iz. Amma Khairat ta d'an ja baya dani kad'an a kan da. Ta yiyu kashedi a Kayi mata, saboda ko magana zata yi min zan ga bata da nutsuwa. A kan matsalar Ancle fa da Salima na zurma wannan rigima. Saboda Momi tayi iya yinta Ancle yak'i saukowa a yi sulhu shida maman Salima. Domin burinta Kawai yazo ta bashi hak'uri ya auri Salima. Shi kuma yace ba yanzu ba, bashi da ra'ayi Sai lokacin da yayi ra'ayi. Momi da kan'ta tasan halin d'an ta, idan ya kafe a hak'ura, idan ba haka ba, to lamari b'aci zai yi. K'arshe ma a yi uwar watsi, yace auren ma baza'ayi ba ya hak'ura da ita. Da wannan dalili Momi ta danne zuciya tasa masa na mujiya. Wato ido. Amma a dame take game da lamarin, saboda wurinta a ke kamun k'afa, ita kuma ta kasa yin yadda suke so ga Ancle. Shi yasa Sai a Kayi haushin kaza huce kan dami, ni fushin a ka juyeshi a kaina, saboda su so suka yi ya sakeni ya auri Salima a lokacin, tun da sun zo neman sulhu. Shi kuma Ancle sunga bashi da niyyar, hakan. Sun fahimci baya nunamin Wata kulawa,ko ta aure. Domin kowa ya Sani, baya zaman minti biyar a d'akina, ballanta na Wai ya kwana ciki. Amma kuma babu wani fitintunu na rikici tsakani na da shi, duk da borar da na zama. Ina girmamashi, da yi masa biyayya dai dai gwargwado. K'alau muke zaune ba'ajin ko tari na na Wai muna ko da da musu. Wannan shi ya zamo k'arin umda da ya had'u da na bijurewar sa ga auran sa da a ke so yanzu da Salima, a kace Ina wuta a jefani. Alhakin komai kamar gani suke a wuya na yake, nice sila.

A tunani na inda a dalci basa yi min haka ba. Matsalar Auren Salima da Ancle tun kafin a San Ancle zai aure nine. Ya kuma fad'i hujjar bijirewar sa ga Momi. To don me zan zama a bar juyewa haushi? nima a barni naji da kashe wutar gabana Mana, da suma sun San da ruruwar ta. Zaman aure na da Ancle Fa'iz ko a suna ma bashi da takwara, ko mahad'i.

Ban ware girki na ba, har lokacin tare muke yi da Khairat na gidan duka. Wani zubun ni keyi, amma Ancle bayaci momi ke yi masa nasa shi kad'ai kullum.
Momi ta kirani har saman ta, naje na gurfana cikin sababben ladabi da nake mata, ko uwata albarka, domin jiki na har rawa yake, saboda tsabar biyayyar da nakewa Momi idan ta Sani a bu. Idan nasan tana son a bu ma, bana jira, Sai ta Sani, yi nake.

Cikin d'aure fuska Momi ta dubeni."Sumayya daga yau, bana son ki sake saka hannunki cikin girkin gidan nan, ki rink'ayin naki.Dama Fa'iz Nike yi masa, Kinga iya cikinki zaki dafa. Na fad'awa Fa'iz ma zaki soma girkin ki."

Nace"To, Momi"

Naci gaba da tsuguno, koda sauran umarni, da naga tayi banza dani, na Mik'e na janyo sanyayyun k'afafuna nayi waje.

Ancle bai min zancen girki ba, momin ce ta sake kirana tace"Nayi magana da Fa'iz yace kome kike so, na amfanin girki wurina zaki amsa, tun da ni yake bawa komai idan ya sayo."
Nace
"Momi, ai ba sai na karb'a ba, tun da Ina da Kayan garata da komai na girki."
Ta zabgomin wani kallo na baki isa ba.

"Na Sani d'iyar tajiri, 'yar na gada. To, hak'k'in Mune ciyar dake. Babu ruwan Mu, da Wanda aka kawo daga gidan tsoho. Namu za'kiyi amfani dashi."
Ni Kam Mamaki ya kamani ma, Na menene a bin zafin a ciki. Ai duk domin a amfana dashi aka kawo garar.
Na sanyaya murya nace.

"Allah ya huci zuciya, Momi, ayi a fuwa, tuba nake. Zan rink'a karb'a.Duk da haka komai na Aikin gidan Nike yi. Wanke wanke Shara, wanke band'akuna da Kayan k"amshi. Amma fa banyi fari ba, bata hanani ba dai. Khairat girki ne nata. Muhibbat Sai taga dama take sa mata hannu, kuma Momi bata yi musu gyara ba.

Daga nan damuwa ta soma Samun gurbi a Zuciyata. Gani da yalwar kud'i, ga Kayan a binci a store, da a ka kawomin komai a Kwai, amma Wai kullum Sai naje wurin Momi karb'ar komai, kuma idan naje, Sai an min wulak'anci kafin a bani, musamman idan Khalifa da Muhibbat, suna wurin. Habaici, da zambo da tsaki, nafi shansu ma.
Gaba d'aya Momi ta canza min. K'iyayya muraran ta fito min da ita. Ko kirana tayi, ban ji ba,ko na kuskure wani a bu, to zagine. Banza ,shashasha, sauna, d'iyar matsiyata, wannan sunaye nane,da Momi ta rad'amin daga baya. Sam bata Kiran Sunana ma. Kullum a mai laifi nake,da nayi da banyi ba, Sai an k'irk'irar min.
Khalifa da Muhibbat sun fi takuramin. Bani da 'yancin fitowa tsakar gida Sai Habaici, harara da tsaki. Amma Khalifa idan shi kad'ai ne, kulani ne Kawai bayayi, Sai dai idan Muhibbat tana kusa, ya samu 'yar uwa Sai suyi min taron gayya. Khairat idan tana kusa, a fuska Zanga ta nuna damuwa sosai a kan a binda suke min. To sai dai bata yarda zata yi da su, sun girmeta. A Kwai Sanda tayi magana a kan bai dace ba a binda suke, suka hayayyak'o mata. Khalifa ma saura k'iris ya kai mata duka Muhibbat ta Kare. Yace mata a gabana. "Wallahi, kika sake yi Mana shishshigi jikinki Sai ya fad'a Miki. Kuma Sai na fad'awa Momi, zagon k'asa kike mana."
Tun daga lokacin, Sai take jan jiki, da taga sun soma yi min iya shege.
Sunan da suke kirana da shi, Wai 'Yar jiran k'ofa. A bin nufi, ni Salima nake yiwa gadon wuri, kafin tazo. Wato bani da wani amfani face kula da muhalli suke nufi. Jin sunan ya zamemin jiki, domin suma shi suka rad'amin ko kirana za'suyi, bayan na Momi da nake ji da shi kuma.
Chapter 18 · 0% Book details