← Book details Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 31

Sashe 12

Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har bakin k'ofar waje da yake tsaye na isa na tarboshi, saboda Kawu Sulaiman Baba ya aikeshi ya tafi, kafin fitowata wurin Yarima. Saboda haka kujeru na roba na Kawu na fito dasu harabar cikin wajen gidan kusa da d'akin Kawu dake kusa da k'ofar fita waje, da yake a katange ba'a hangen na ciki.
Kamar had'in baki, Yarima Shima Man less yasa na maza, kalar pink mai cizawa. Sun masa wani irin kyau Kam.
Duk da naje har bakin k'ofa na tarboshi cikin sakin fuska sosai, da sakin jiki da girmamawa, Sam banga ya sakarmin fuska ba. Ya dai dubeni, a dak'ile ya kau da kai. Tare muka jeru zuwa mazaunin Zaman, hannun'sa cikin aljihu, yana tafiyar nan tasa ta isa da jin kai. Naga Sai wani shan k'amshi ma yake, kamar Wanda aka tilasta Sai yazo wurina.

Kujerun da zamu zauna, suna fuskantar juna, kuma ni na a jiyesu Ina sane a hakan. Zuciyata ce naji ta soma k'ek'ashewa, daga fargabar da nake ciki ma na auran Ancle Fa'izu, saboda na hanga gabas da kudu da arewa, ban hango matsera ba, na tserewa auran. Shi yasa Kawai na Mik'a wuya, tare da nemo hanyoyin da zanbi, na k'ubuta daga tozarcin'sa da ya zama lazim. Nasan idan na ci gaba da nuna d'ari d'ari da shi, da Jan jiki, da alkunyar nan, to kullum gumamin takaici zai ci gaba da yi, shi ko a jikin'sa, ni zai bari da ciwon zuciya.

A tare ma muka zauna. Bayan na gaishe shi nace

"Yaya momi, da fatan tana lafiya "

Sai da ya fara da yi min wani irin salon kallo da Idanuwan nan nasa masu farauce zuciya. Amma na tabbata, babu manufar komai cikin'su.
Baki d'aya Sai naji yanayin komai nawa ya canza tashi guda. Wani irin feeling naji, da bantab'aji ba kan wani namiji. Gashi na jawa kaina, muna fuskantar juna bare na kub'uce.

"She is doing fine. Na barota lafiya Lau. Amma Yaya kikasan Momi?"
Nace
"Tun da nasan'ka ai dole na San'ta.

Yace"A'a ni kad'ai kika sani. Ita dai kinji sunan'ta wurin Sulaiman. Any way, naji dadI, da kulawar ki a gareta."
Karo na farko Kenan da na tab'aji ya nuna jin dad'i a a binda a Kayi masa a sanina.

Gudun kar na kuma laifi, nayi saurin cika cup da lemon maltina mai sanyi na Mik'a masa. Kafin ya karb'a yace
"Kinyi karatun ta nutsu Kenan!. Ban tanka ba.
Ya Mik'a hannu ya karb'a, Amma bai shaba, ya Shiga juya d'aya kwalbar lemon da ban bud'e ba.

"Yaya a Kayi, kika San Ina son lemon malt? aikin Sulaiman ne dai."
Idanun'sa na kan lemon yake surutan.
Ya shanye, ya sake cika cup ya shanye. Ya bud'e d'aya kwalbar ya cika cup ya Sha, ya a jiye ragowar a gefe.
"Da k'ishirwa na iso, Sai kika samu ladana kika yi a binda ya dace. Ina son maltina sosai a rayuwata. Na kansha kwalba uku Ku hudu wurin training ko gasar boll."
Nace
"Lallai kana son"ta da yawa."
"Ke baki son'ta?" Yace
Nace
"Kadai d'arsa min son'ta, ga yarda ka damu da ita."
Yace
"Look, ki fad'i opinion d'inki Kawai, ba ruwan'ki da zab'ina OK?
Naji rashin jin dad'in gwaliyar da yayi min, amma Sai na danne.

"Domin na tayaka son a binda kake so laifine.?"
Yace
"Kukure ne dai"
Kafin na wartsake daga wannan ya jefomin wani.

"Sumayya Wai addu'a kika yi min ne?"
Na waro idanu waje
"Wace addu'a zan yi Maka ni kuwa Ancle Fa'iz?"
Yayi harr da idanu ya sake kafeni da irin kallon d'azu, jin furucina

"Wallahi da da natafi, naci alwashin bazaki sake gani na ba, saboda gidadancin da kika nunamin. Amma bayan few days, Kawai Sai naji Ina son waiwayarki kuma. Naga kin canza yau, kina d'an tab'uka abu. Kenan komai da kika yimin rannan kina sane Kenan.?"
Bani da amsa, idan ma a Kwai bazai jiba. shi yasa na zab'i yin shiru.

"Kin a mince zaki jure irin Zaman aure N'a?"
Samun kaina nayi da juya idanu na rausayar

"Zan jure man, tun da na iya jure zafafan bulalanka goma, masu ratsa k'ashi da tsoka."
Sai ya d'an d'aga idanun'sa Sama, mai nuna a lamun ya tuno komai.

"A shefa kin tab'a fad'owa tarko na ko? amma wannan shafar mai ne, idan kika yi saken da kika sake fad'owa tarko na. Kinsan yanzu matsayi uku zan had'a a wurinki da an shafa fatiha.
Malaminki nake, Sannan Ancle,Sai na gaba mijinki." Da hannun'sa yake nuni, ta hanyar lank'wasasu.
"Haka ne?"
'Yar dariya na saka.
Yace
"Zakiyi ta gasken ne"

Ya tattaro, Nutsuwar'sa.
"Ina so ki fad'amin nawa. Zaki buk'ata na shirin auren'mu na biki, domin na tanadeki , banason auren nan ya wuce Wata guda fa. "
Da hanzari, na dubeshi. Duk nasan saboda manufar sa ne,da yake so ya cimma. Wani zafi,naji a k'irjina.
"Ka barshi, na yafe. Ni babu shagalin da zan'yi."

Ya jefa min kallon hadarin kaji.

"Kija Mani zargi ko? to bazai yiyu ba. Bazaki tozarta min aure ba, ko ba kya Sona , kuma ko banason'ki za'ayi shagali irin Wanda ya dace. Kije kiyi nazarin adadin kud'in da zakiyi amfani da shi. Idan na dawo naji. Dole ne , kima saddak'ar."
Shiru nayi, jin zai soma hawa dokin zuciyar'sa da nake tsoro.

Bayan sa'oi cikin kafeni da idanun'nan nasa masu narkar da zuciya.
"Kiyi min magana ko?"
Nace
"Zan fad'awa Kawu Sulaiman, idan na lissafa."
Ya kwaikwayi salon yarda na furta.

"Zan fad'awa Kawu Sulaiman idan na lissafa. To Wai meyasa zaki nuna bam bamci tsakanin ni dashi? Nima ba kawun bane?"
Da nayi shiru, ya tafa hannun'sa a hankali, ya kuma dunk'ule.

"Shikenan 'yar gidan Kawu Sulaiman, Sai naji daga gareki."

Ya ci gaba da lissafomin irin shirin da ya soma na auren. Lefema da Sadaki, da kud'in aure yace rana guda Zai kawo. Kenan Ranar d'aurin aure Kawai za'asa . Yarda yake nuna a fuwa da komai, Sai a zaci, wani auren soyayya za muyi da shi, na an matsu da juna. Bayan nan bana gaban'sa na Sani, ko na sakan na a gogo. Manufar'sa ya d'anawa k'ahon zuk'a.

Fargaba d'aya nidai ta ragemin, shine kar a zal ta fad'amin Ancle Fa'iz ya samu damar yi min cuta ta k'arshe. Shine burin'sa Yana cika ya sakenj, nazo na bud'e faifan Zaman zawarci. A binda nafi tsana Kenan a rayuwata, zawarci.. Jinake yi, har gabana na yankewa ya fad'i idan na tuno.

Nina shirya had'uwata da Nuriyya domin taji labarin da zai kid'imata. Wato na aure na da Ancle Fa'izu. Mutumin da ta k'wallafarai a kan'sa kamar ta zautu, wai yau shi yake shirin aure na. Inda a ke neman'sa yayi b'atan dabo..

Ta kuwa girgiza da jin komai. Nasan baza taji dad'iba, tun da ta nunamin irin son da take masa. Sai dai bani da zab'i face dole na fad'a mata, tun da babbar a miniyata ce dole taji. Ban sanar da ita sirrin komai ba, na dai ce Kawu Sulaiman ya had'a auran, amma ni a fargaba nake.idanunta naga yayi rau rau.

Tace"Sumayya al'amarin ubangiji ya shallake tunanin bayi. Tsakanina dake a wannan lamari addu'a Kawai, to yaya zanyi? bani da yarda zanyi Sumayya."
To nima d'in dabara ta kubce, bani da yarda zanyin da na barmata. Dani da itan da ya sacewa zuciya, duk rukuni guda muke. Babu Wacce ta rabauta da Soyayyar'sa, Sai ni da k'addarar auran'sa ta sauka a kaina.

"Ni haushi kike bani da kike Kiran Wai kina zullumin auren'sa. Kamar wannan zuk'ek'en saurayin za'a nok'ewa auran'sa? Wallahi da motsi a kan'ki. Ke koma ba na gari bane, ke dai ko baki tashi da ribar komai ba, kika tashi da ribar kyawawan fararen yara, ai kin gama da shi. Kasuwa ta tashima ai d'an koli yaci riba".

Ni kam haushi furucin'ta ya bani. Ana ga yak'i tana ga k'ura.
"Inaji ganin jarabarki ta son kyau da fari, Sai kin auri maye, nasan ko Kinsan mayen nema auren'sa za ki yi ".

Tayi 'Yar dariya.
"Tabbas!. Ko zai rink'a lasar kurwata kullum Ina suma na farfad'o zan aureshi in dai irin Ancle Fa'izu ne."

Na jinjina furutanta.
"Al'amarinki Sai dai neman sauk'i Nuriyya, amma ba waraka ba."

"Bani buk'atar warakar Dama"

Tace a daken'ta.

*🏤 NI DA GIDANA 🏤*

*_Littafi na daya_*

*NA*

*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

📱11
_______ A kwati shida set da kit d'aya Ancle Fa'iz ya had'o min na lefe. Ya zuba abubuwa kuma gaskiya masu tsada fiye da zaton kowa.

A tamfofi Holand manya guda goma ne. Bayan masu matsakaitan kud'i goma. Lesuna masu daraja guda goma ne. Shaddodi da material ma sunyi . Hakanan Takalma da jakunkuna babu masu rangwamen kud'i. Sai a jakar Kayan sarkoki' za'a sha kallo. Duk da babu gold, Sai da aka zab'a a ka darje wurin zab'o k'ayatattun sark'oki na cinyewa, launi launi. Tilas a ce isashshiyar mace da tasan kan sirrin iya ado da kwalliya ta zab'o.

Ni dai Abin yayi matuk'ar d'auremin kai, na yarda ya narkar da kud'i irin haka a auren da yafi kowa sanin manufar'sa da makomar'sa a gaba.

Hajiya Mariya tafi kowa, murnar zuwan aure na, inda tayi ta kod"a lefen tana labartawa ga wad'anda basu gani ba, tamkar kaina farau, kuma k'arau. Haka ma 'yan uwan uwa da ubana kowa Sai Sam barka da Fatan alkhairi.

Sati hud'u a kasa d'aurin auren. An tasheni tsaye an kuma tashi Kawu Sulaiman tsaye da kakana. Domin duk basu shirya ba suma, saboda basu zaci zuwan aurena a tsukin ba. Amma Kawu Sulaiman naga ko a jikin'sa. Murna yake sosai da zumud'in zuwan auren . Kuma dama komai Ancle Fa'izu yace ga yarda yake so a yi a kan aurena da shi, to ta zauna. Shi yayi ta nacin kar a d'aga bikin ma kamar yarda kakana yaso, saboda yasan Yariman nasa, bazai so ba Sam!..
Chapter 12 · 0% Book details