← Book details Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 31

Sashe 4

Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Tashi Kije" Yace dani da nayi sunk'ui da kai.
Tun daga ranar, ban sake yarda naje staff room ba, saboda gargad'in malam Fa'iz. Domin nasan makomata ma idan ya kamani.
Ba'ajima ba kuwa na fahimci anyi gyara. Domin da lokaci ya Shiga malami Zai shigo da kan'sa. Ba kuma Zai fita ba, Sai lokacin'sa ya fita. Kuma karatu ya k'ara zafi. Malamai sun daina shigo da hira da wasanni cikin karatu, Wanda nafi kyauta ta zaton malam Fa'izu ya fahimci duk matsalolin dake cikin harkar koyarwa yasa aka kawo gyararraki. Ko Mak'iyin malam Fa'izu tabbas ya yarda sanadin zuwan sa, makaranta ta gyaru. Sauye sauyen ci gaba da ya kawo da yawa na ci gaba. K'orafin da a ke yi da shine bai kau ba wato na tsanani da cin zarafin studen't fiye da k'ima idan sun yi laifi. To ni fahimtata da hakan , Kawai na fahimci Fa'iz Mutum ne mai fushi da zafin zuciya. Shi yasa ma Sam baya d'aukar raini. A binda ya shige min duhu da shi, na yarda baya karb'an uzuri. Kuma baisan kalmar Hak'uri ba.

Watanni uku suka rage muyi jarrabawar kammala makaranta. Saboda haka rannan Bayan malam Abba ya gama yi Mana subject d'in sa na mathematic, ya zauna yana bamu shawarwari domin Mu k'ara zage damtse da karatu, Mu samu sakamakon jarrabawa mai kyau.

"Ko da yake yanzu Kuna birgeni, naga ma ai duk kun canza kunyi laushi. Da idan an shigo a jin nan kamar kasuwar trade fair. Amma yanzu kamar gidan makoki. Ko babu malami Zanga Kowacce ta d'auko littafi tana bitar karatu. Wai Yaya a bin yakene.? Ko walwalar Ku ma bana gani."

Fati d'alha tace."Sir, an kawo mai takura Mana ta yaya za'aga walwalarmu

Zulaiha ta karb'a.

"Abokin ka ne ai ya kamata Kayi masa nasiha, ya fiye tsanani.laifi da k'arami da babba duk hukunci d'aya. Zagin da yake Mana, ko iyayenmu basa yi Mana. Wallahi matar'sa ta Shiga uku."

Intisar tace"Addu'a zaku yi masa Kawai, domin ya gyara halin sa." Kowa Sai da ya dubeta na Mamaki. Shi kuwa malam Abba murmushi yayi.

"Yauwa 'yar gari, Kunji in da ake kalamai na nutsatstsu. Kuma idan b'era da Sata ai daddawa ma da wari. Kuma k'iriniyarku tayi yawa, dole Sai irin malam Fa'izu ne zai yi dai dai daku. Malam Fa'izu idan ba'ace Sam barka ba, baza'a kushe ba. Gyaran da ya kawo cikin makarantar nan ai ya yawaita. Ko prince pal da vice sun Sara masa. Ai addu'a ya dace Kuyi masa ta alkhairi. Bayan tarbiyyar da ya kimsa muku ya gyara muku harkar karatu sosai. Kuma Ku zakuci amfanin sa a gaba. Shi ba ma mazauni bane jiddin. A Kwai a binda yasa a gaba, da ya samu Zai bar harkar Koyarwar. Saboda kishin k'asa Kawai ya Shiga harkar da ba itace burin'sa ba. Zan iya rantse muku albashi ma shi baya gaban'sa. Burin sa a samu sauyi da ci gaba. Saboda haka kuskure ne d'alibi ya zauna yana aibata malami ko da dalili, tun da kullum cikin cin amfanin sa yake. Kuma ba'a iya biyan malami"

Jikin kowa yayi sanyi. A ka rasa me iya cewa komai. Ni kuwa dama nasan kuka suka kawo gidan mutuwa. Malam Abba na hannun Daman malam Fa'izu ne, bazai tab'a yarda a ai bata shi ba ya k'yale, duk da dai gaskiya ya fad'I.

Alkhairan da malam Fa'izu ya kawo, a makaranta, bai kamata a aibatashi ba, koda yayi laifin. Kowa ma yaji ba domin kud'I yake koyarwa ba, Sai domin kishin k'asar'sa. Wannan kad'ai ya isa yasa ya karb'I lambar yabo. Tunani na Kenan da na wasu d'alibai da muka zanta daga baya.

Daga baya ga mamakin Mu, malam Fa'iz ya sassauta tsananin nan da tsaurara hukunci garemu. Kuma na lura canzawar da Yaga munyi ne, Shima yayi d'an laushi. Sannan ya fito da Wata hanya ta taimakon mu da yaga jarrabawar Mu ta gama makaranta ta gaba to. Lesson ya tsara duk yamma cikin makaranta ga duk Wacce ke ra'ayi amma. Shi ya d'auki nauyin komai.hud'u da rabi an Shiga a tashi k'arfe shida na yamma. Duk d'alibai kuwa a ka yi ta tururuwar zuwa, saboda kowa so take taci jarrabawa. Ba kuma iya darasin turanci yake koyawa ba, har ma da sauran darussa. Kuma yawancin a binda yake koya Mana Wanda yake tunanin Zai fito Mana ne a jarrabawa.
Baki d'aya muka ga ya canza ma. Ya rage zagi da fad'an nan da tsare gida. Amma duk da haka fa babu fuskar da za'a kawo masa raini ko wasa. Har hira ma yake damu Amma fa a kan karatu, da bamu shawarwari masu kyau, duk a kan harkar karatu, saboda jarrabawar dake dosomu.

Da jarrabawar tazo kuwa mun taki babbar sa'a. Domin kuwa yawancin a bubuwan da malam Fa'iz ya koyar damu shi ya fito. Har zargi ma muka rink'ayi anya bai samu liket d'in jarrabawar ba? Domin komai ya fito da ya koyar damu. Ai Sai yayi kuma farin jini wurin Mu. Domin yayi Mana k'ok'arin da babu malamin da yayi Mana irin sa. Mun kammala jarrabawar cikin sa'a da kyautata zato. Har fati aka k'irk'Ira a ka Sha hotuna. Har da malamai a Kayi hotuna. Amma fa banda malam Fa'izu. Kuma anfi kwad'ayin ayi hoton da shi, saboda tarihi. Kuma Abin alfaharine ga d'alibai, Amma mirsisi yak'i. Ko da yake tsoron tun karar'sa ma a ke yi, malam Abba a ka tura. Ya dawo yace.

"Kuyi Hak'uri fa. Abokina yak'i yace yana da mata, kuma zatayi kishin haka.

Duk d'alibai sun yarda, nice dai kunne na bai karb'a ba. Lambobin waya ma na malamai da ake karb'a malam Fa'izu hanawa yayi. A ka koma takan malam Abba ya Bada lambar wayar fa'iz yace shi bashi da ita. Ta yiyu shi ya hana shi ya bayar, ko bashi da itan.
Intisar tafi kowa damuwa da lambar Fa'iz, saboda son da take masa ma ya fito fili. Amma ko giyar wake tasha bazata iya tambayar sa ba. Tun daga Sanda tayi masa rashin kunyar nan suke takun sak'a da shi. Ta gasu a hannun'sa.

Tsakanin sa da ita hararace. Duk Sanda ya shigo class Sai ya tasheta yayi mata tambayoyin Abinda ya koyar. Ta fad'i Wanda ta d'an fahimta, tana yi yana jefa mata kallon banza. In da ta gaza jikinta ya fad'a mata, ko tasha zagi da aibatawa. Wannan shine hukunci mai sauk'i wurin Fa'iz, wato cin zarafi, da Mutum Zai muzanta ya raina kan'sa. In banda ma shu'umanci irin na So, ta yaya soyayya zata cillata wurin Fa'izu Bukar? ai had'in bai yi ba. Ko a iya ma b'angaren'ta a bin ya tsaya.

Ni dama Ina gefe, babu a binda yayi min zafi ma da kowani malami. Da k'awaye na Irina yaku bayi nake mu'amala ma. Ko hotuna ma b'uya mukayi can cikin furanni muka Sha su. Allah ya Sani Ina da gudun zuciya. Kuma bani da kwad'ayi da shishshigi ga wad'an da nasan ba tsara na bane. Komai nawa sassauk'a ne, saboda nasan ni ba 'yar kowa bace. Ko sunan da nayi a makaranta da class, k'okarina ya d'agani, aka Sanda ni.

Wasu kuka ma suka Sha na rabuwa da juna,yayin da wasu suka raja'a da musayan adireshin juna da lambobin waya.
Ni k'awaye na uku ne cal da naga tafiyar mu iri d'aya ce. Lubabatu, Atika da Zuhra. Ni suna fi jajanta rabuwar Mu, kuma da su Kawai muka yi musayan wayoyin juna, da alk'awarin zamu rink'a ziyarar juna muka rabu. Wannan Kenan.

*🏤 NI DA GIDANA 🏤*

*_Littafi na daya_*

*NA*

*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

📱4
________ Tsawon Wata guda, tun da na gama secondry, babu in da nake zuwa bayan islamiyya. Sam kuma fitar bata dameni ba ma saboda ni dama ba ma'abociyar son yawo bace. Sannan soyayya da tarairayar da nake Sha wurin kawuna sulaiman ta isar min daga damuwa da wani a bu na d'ebe kewa. Kulawa gata, sangarta so da k'auna duk Kawu sulaiman ya tattare su a kaina. Haka ma kakana Laminu mai turare. Sai 'yar korar su mai taya su, matar kakana baba Talatu da ya auro bayan rasuwar Inna Hajara kakata. Duk da baza'a had'ata da kakata ba Hajara, amma tana kamantawa sosai.
Chapter 4 · 0% Book details