Sashe 28
Ni Da Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ban yarda ba, Fa'iz, k'iri k'iri fa ka gani, amma ka zama makahon k'arya. Muhibbat tace min kasamu Khalifa da Sumayya, suna aikata fasadi, amma kak'i ganin laifin Sumayya Sai na Khalifa, har marinsa Kayi. Hakan na nufin a dalci Kayi, kuma ka damu da naka Kenan?"
Ai Ancle Muhibbat naga ya zubawa idanu cikin wani irin fushi, cikin tsawa yace mata
"Ke Yaushe kika zama shahararriyar Mak'aryaciya ban Sani ba?" Wata irin mangara ya kai mata, Momi ta Kare ta matseta a jikinta.ita ma ta ruk'unk'ume uwar.
"Kar ka kuskura, ka tab'amin yarinya Wallahi, domin ta fad'i gaskiya."
Idanun'sa suna nan Jazur, basu canza ba, ya fesar da wani huci mai zafi, na jin ciwon rashin damk'ar Muhibbat, na tabbatar da Sai ta d'and'ana kud'arta. Dai dai nan a ka soma Kiran sallar assalatu na farko.
Ancle yace
"Momi,k'arya Muhibbat ta shirya Miki. Ni idanuna ba suga komai ba. Da naji ihun Sumayya da na Shiga ma basa kusa da juna. Wannan kuwa ko kusa bai kai hujjar yin zargi ba in da adalci. Shaidar zina babbar al'amarice Momi, ko a musulunci sai an samu shaidu hud'u, kuma Sai sun gani ra'ayal aini. Ko uku ne, suka gani, d'aya yace bai gani ba, to sai sun Sha hukuncin bulalai. Kenan a Kwai had'ari ma ga ayi wa Mutum irin wannan zargi, babu shaidu. kuma ni ina da hujjoji uku da ban yarda ba. Na farko Me yasa Khalifa daya ce bore yayi wa Sumayya, domin tona a siri mai yasa bai riga Sumayya ba? ai Sai ya fito cikin daren ya tashi kowa ya Sani, amma Ihun Sumayya na neman a gaji, shi ya fallasa komai. Sannan na biyu a d'akin Sumayya fa a ka ganshi dumu dumu. Ko a Shari'a shine jagoran laifi. Na uku da kunne na naji hirar sa da abokin sa Tajo a k'ofar gida baisan na dawo ba, zan fito na dakata da naji irin hirar. A cewarsa wai Sumayya ta zame masa matsala na katangar Samun aikin a counter a kamfanin su Salima, saboda auren ta da nayi, nak'i mai da kai ga auren Salima, ballanta na ya samu aiki. kuma wai sai ya shirya tuggun da zan saketa. Tajo Inaji yana tinzirashi. Dama a bokan, naka duk baragurbine, shi yasa kak'i kintsuwa. Sam banyarda da kai ba Khalifa. Ko kotu a kaje Wallahi bazan bi bayanka ba, bayan Sumayya zan bi. Nine na farko daga cikin witness d'inta ko high court za'a."
Momi kuwa ta k'ara tunzura., duk da hujjojin Ancle Fa'iz masu k'wari ne da za'a mara masa baya, amma da yake k'iyayyar tawa ce Kawai tafi tasiri a ranta, Sai tace.
"Ban yarda ni kuma da duk tawilinka ba Fa'iz. kuma bazan yarda ba.Idan kak'i bayan Khalifa kabi bare Sai me? ni ina bayan d'ana,haka ma 'Yan uwan'sa. Nan naga Khairat cikin fushi ta kalli Khalifa ta d'an ja tsaki, haushin sa na gani muraran cikin idanun ta.
Momi ta zarce da cewa.
"Na gode Allah ma da Abban Ku yau bai motsaba, saboda maganin baccin da yasha, saboda larurar sa. Yanzu za'a kashe a rufe a bunne, kuma duk Wanda yaje masa da zancen babu ni babu shi. Kai kuma Fa'iz, kwana guda na baka ral! Kasan Wacce kake ciki da Sumayya. Na rabu da ita, taje dan kanta, amma fa dole ka nisantata da mu, ka kuma nisanta ta da kan ka. In dai nina haifeka, dole kayi hukuncin da zai samar min da nusuwa, domin ni ban yarda ka had'a jini da irin wannan matar ba. Sam bata dace da kai ba ko da wasa ba gaske ba."
Duk da Momi bata furta mai Ancle zai yi ba a fili a kaina, duk mai hankali zai halarto.
Duk wannan zance da Momi keyi, ni Ina uwar d'aka ma na barsu, illa jiyo muryarsu. Tuni na tsara Wacce zata fish she ni kafin ma su su yanke manufarsu. Nasan dai Ancle Fa'iz sakina zai yi, to kafin yayin, ni nayi nisa ma, Sai dai ya biyo ni da takardar sakin, ko ya turo. Tabbas Ancle Yayi jarumtar wariya, shi kad'ai yayi min halaccin da ban tab'a zato ba. Amma duk da haka na yafeshi, ko da zan dawwama babu aure, idan na rasa shi. Abinda 'yan uwan'sa suka yi min, ya tabbatar min zasu iya yi min kowani irin mugun a bu, domin nayi nisa da shi. To me yayi zafi, shi ba wuta ba.?
**********
'Yar jakata madaidaiciya na d'auka, na d'ebi Kaya kala uku, da sauran a bubuwan amfani na mata da kud'i. Ina idar da sallar a suba, gari da sauran duhu na himmata. Na doka sa'a Ancle yana d'akin'sa bai kuma shigowa wurina ba, tun da aka gama hatsaniyar ya fice. Nasan yana d'akin sa yayi luf, yana nazarin Wacce za'ayi, kuma nasan bashi da zab'in da ya wuce yiwa Momin sa biyayya. Rabuwa dani sassauk'an a bu ne ai a wurin'sa tun da yana da wannan k'udirin nan gaba a nawa zaton. A hankali, na rink'a k'wank'wasa K'ofar d'akin Ancle Sulaiman dake daura da hanyar fita waje, saboda kar cikin gidan su jiyo, domin na fison ya fara sanin komai kafin kowa na gidan ya Sani. Can ta ciki yace waye? Nace "Kawu nice Sumayya." Da sauri kuwa ya bud'e. Wani kallo ya sakarmin, Sannan ya dire kan jakar da nake rik'e da ita. Yace
"Me yake tafe dake da duku dukun nan, har da jaka? a binda nake fargaba ya auku ko?. Na soma matsar hawaye mai zafi.
"Ancle wani sharri mai muni aka k'ullamin." Na soma sheshshekar kuka. Jikin sa yayi sanyi, yanayin sa gaba d'aya ya canza. Ya koma cikin d'akin yace nima na shigo.
Yayi tsai yana kallona kafin yace "Yarima ya sakeki ne?"
Na girgiza kai "A'a, amma nasan yana gab da yi." Yace cikin canzawar kamanni lokaci guda.
"Yaya a Kayi kika san hakan?"
Nace cikin sharar hawaye.
"Momin 'sa ta bashi umarnin batason kasancewar mu tare."
Ya nisa.
"Shi yace ki taho gida?"
Nace "Bai San ma na taho ba. Babu Wanda ya gan ni a gidan dana fito.
Yaja kwafa irin ta ban takaici. "Ai kinji tsiyar.menene to amfanin fitowar taki? Kenan a ce zargin da ake miki gaskiya ne Kenan? tun da kin gudu a sace.shi kuma Yarima ki k'ara tunzurashi ko baiyi niyyar sakin ki ba ya sakeki? da auransa bai sakeki ba ki fito babu sanin sa, baisan inda kika jeba, ai da Sai kiyi hak'uri Sumayya ki zauna a d'akinki kiga mai zai zartar tukun. Amma haka kawai ki zartar da hukunci kafin ya zartar.?"
"Kayi hak'uri Ancle hankalina ne ya tashi ya gushe, Sai Samun kaina nayi da yin komai." Nace cikin share hawaye, wani na sake zubowa.
Yace "Fad'amin a binda ya farun."
Tun daga farkon zuwa na gidan har zuwa inda aka yi min sharri, ban b'oyewa Ancle Sulaiman ba na matsalolin da na fuskan'ta.
Yayi shiru kafin ya dubeni yace "Kukan ya isa haka Sumayya, in dai ba so kike hawayen ya k'are ba. Komenene nina ja miki dai "
Da sauri nace "No Ancle. Komai da ya faru dama yana cikin littafin k'addarata, ko babu kai Sai ya faru."
Yace
"Bantab'a zaton zaki samu matsala da mutan gidan su ba, zatona iyakaci keda Yarimane kafin Ku fahimci juna ko kuso juna nasan dole Ku samu Sab'ani iri iri, amma bani da haufi saboda nasan 'yata ta garice mai juriya da iya Mu'amala. Amma duk da haka an samu ci gaba, tun da har Yarima ya yarda dake ya goyi bayanki bai yarda da sharrin da aka yi Miki ba, duk da girma k'azafin mai girmane da dole yasa zuciya rawa da girgiza da shakku tsakanin ma'aurata. Nayi mamakin irin wannan girman yarda da Yarima yayi miki da har ya k'arya ta take gaban Momin sa, ai ko domin wannan ba kya bashi kunya ba ki fito. Dan adam ba'a cin alwashi a kan'sa ko Yaushe, ki fad'amin gaskiya Sumayya, me yasa Khalifa yayi miki irin wannan sharrin, me ye tsakanin Ku in dai haka ne." Nace
"Wallahi Ancle ba wani abu. Salima suka fi son sa dani, shi kuma yak'i koma mata har yanzu, bai huce ba, shine ni nazama mai alhakin komai a ke wahaldani, a kemin haushin kaza huce kan dami."
Kafin Kawu na ya kuma magana wayar sa ta d'auki k'ara. Yana d'agawa Sai ji nayi yace
"Yarima.!.
Gabana ya yanke ya fad'i. Nabi Kawu da kallo yayin da ya ci gaba da cewa a wayar.
"Gata nan ma a gabana, nan tazo. Karkaji komai, nine fa naka, kuma ai bata b'aci tsakanin Mu.
To Sai kazo"
Kawu bayan ya kashe wayar ya dubeni.
"Ga Yarima nan zai zo yanzu."
Da sauri nace "Takardar sakina zai kawo amma"
Wani kallo mai kama da harara Kawai Kawu Sulaiman ya sakarmin.
*🏤 NI DA GIDANA 🏤*
*_Littafi na daya_*
*NA*
*ZAINAB ILYAS MAZAWAJE*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association