← Book details Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 38

Sashe 7

Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

________________________📖Bayan komai ya kammala ne Ahmad yaita lalla'ba Sukainat hartayi shiru,sannan yakaita toilet cikin ruwan zafi da gishiri ka'dan yasanya ta aciki bayan kamar 30mins yacireta sannan tayi na tsare tafito tana tafiya Ahankali simply gownt tasanya tada da sallah,bayan ta idar ne ta daga hannu bibbiyu tana rokon Allah yabata zaman lafiya dawwa mammiya da kwanciyar hankali me daurewa atsakaninta da mijinta, sannan yatsaresu daga sharrin makiya,tashafa lumshe ido tayi tana jin bacci nafusgarta"Bata ankaraba taji andauketa kan gado Ahmad ya kwantar da ita bayan yacanza bedsheets,din fuskarta yashafa yace sorry my suky na wahalar dake ko?kai tajuya Cike da kunya batare datace komai "shima murmushi yayi yashafa sajen fuskarsa"zuwa yayi yasanya jallabiya kana yatada salla bayan ya idar yaje gefenta ya kwanta tare da janyota jikinsa dahaka bacci me da'din gaske yayi awungaba da Ahmad yayinda Na wahala yadauki Sukainat....Se misalin karfe 9:45am Sukainat tafarka daga wahallen baccin daya dauke ta,'kura masa dara-daran idanunta tayi tana kallon lumsassun idanunsa dake lumshe ga sajensa daya kwanta luf-luf Wanda yakawata kyawun fuskarsa madede cin bakinsa takurawa idanu tana kallo yanda yatsukesu sun sake yin pinch color dasu" Hannu biyu tasanya tarufe fuskarta tana murmushi sakamakon tuna abinda yafaru atsakaninsu,jitayi anjanye hanna yenta dasauri taware dara-daran idanunta Wanda suka kumbura saboda kuka"Gani tayi Ahmad yakafeta da firgitattun idanunsa masu narkar da zuciyar ko wacce diya mace.Iskan bakinsa yahura mata a idanunta yace kallon ya isa haka mana yafada yana aika mata da wani irin kallo mecike da so"Sunkuyar dakai tayi Cike da kunya,'kafafunsa yazuro kasa yace bari na ha'da miki tea kisha sekisha pain relief ko?,"kai tagya'da masa alamar toh"Ficewa yayi yanufi corridor daze sadashi da kitchen dake tsakanin sashen nasu"Tsaye ya hangota tabaiwa kofa baya Arish din datake soyawa se konewa yake da alama batasani ba tazurfafa cikin tunani,cikin sauri yakarasa cikin kitchen din tare da kashe gas din.kafa'dunta yarike Cike da damuwa yace My Queen wani irin tunani kike haka dakikeson kashe kanki dasauri yaja baya ganin yanda idanunta suka koma sunyi wani irin jaaa dasu sunsake kankancewa gawani irin kumburi dasukayi.Tallafo fuskarta yayi da hannu biyu cikin dimuwa yace meyasa meki my Queen waya miki haka?,yafada yana bin fuskarta da matsanancin mamakin abin daya sameta daga daren jiya zuwa yau yanda suka koma haka...Itama ido tazuba masa Cike da takaicinsa jitake kamar tacika masa wuka awuya,koya yi zaton batasan abinda yafaru tsakanin sa da makirar Amaryarsa adaren jiya bane wai Ahmad ne ze Iya ha'da shimfida dawata kuma tana raye.Ka fadarta yajijjiga Cike da damuwa yace kibani amsa mana my Queen ina magana kinyi shiru."Dede ta nutsuwarta tayi tare da kakalo murmushin dole wanda bewuce saman la'b'ban taba tace calm down Honey am fine,nothing happen to me bleive me...be bari takarasa ba yakatsata dacewa taya zakice kina lafiya bayan banga alamar hakan atare dakeba.
Shitttt tace dashi tana daura hannunta asaman labbansa,alamar yayi shiru"kamar wani soko haka yayi shiru se ido dayake Binta dashi"talakace masa hanci tayi tace let me tell u exactly what happen:Kafin yace Wani abin tace, Ina cikin bacci da daddare nayi mafarki wai wata mata wacce bansan wacece ita ba tana zugaka kasakeni kancewa ni bamatar arziki bace kuma idan bakasakeni ba duk abinda yasameka kaikajawa kanka,ganin duk maganan data fada maka kaki yarda yasanyata kaika wajen boka",kasan meyafi girgizani acikin mafarkin ta tambayesa tana me kallon yanda yanayin sa yasauya baki daya zuwa tashin hankali"kai ya girgiza kai yayi Cike da damuwa yace a'a"Sukainat itace bokar kuma itake son rabamu,Wannan shine sanadiyyan dayasa kaganni awannan halin wannan abin bakaramin sake daga min hankali yayi ba ina tsoron tarabamu"ta'fada tana share hawayen daya zubomata.
Kamar saukan aradu aka haka yaji kalamanta,dan haka ya daure fuska yace kidena irin wannan kalaman Nadiya domin mafarki ba gaskiya bane saboda haka karki sake danganta Sukainat da boka sannan kirufe wannan maganar anan" nasan bazewuce sharrin shaidan bane anma taya Sukainat zataso rabamu"?rau rau tayi da idanu tace dalilin dayasa naki fada maka kenan anma kamatsamin tayaya kake tunanin nizan kwashi sirrinka infadawa wasu kada fa kamanta kamar 'kanwa haka nadauki Sukainat anma kaida bakinka kake fadin haka takarashe cikin rawan murya,Kai yadafe yace nifa bahaka nake nufi ba dan haka kibar maganan kawai.
Yana gama fadin haka ya dauki cup ya ha'da tea mai kauri yafice batare daya sake cewa da ita komai ba.
Da kallo tabisa haryafice 'kwafa tayi tace lokacin kane Ahmad.Gas din takunna tacigaba da soya arish da kwai bayan tagama tahade komai a dining area dake sashenta sannan tashiga toilet ta watsa ruwa kasancewar 'ya'yan ta basunan suna gidan mahaifiyar ta.
Yana shiga yaga batanan zaman sa badadewa tafito daure da towel wanda tsawonsa yakai gwiwarta sekuma Wanda tarike a hannunta tana goge kanta"Ido yakura ma santala santalan cinyoyinta"Hannu yasanya yashafi sajen fuskarsa, ita kuwa tsayawa tayi takasa karasawa sakamakon kafeta dayayi da sexy eyes dinsa "bata ankaraba taji yajanyota kansa, dasauri tasanya hannunta tarike towel dinta jin yana kokarin sincewa.Jitayi yafara yimata cakulkuli batasan time datafara 'kyal'kyala masa dariya ba tana kokarin 'kwatar kanta"Fararen hakoranta yazubawa idanu ganin yanda suke haske" Jisukayi anturo kofar bedroom din, dasauri duk sukajuya Nadiya sukagani tsaye takafesu da idanu tamkar zasu zazzago.....

_VOTE_ ✅
_COMMENTS_
*_AND_*
_SHARE_

*_ESHAA CE~*_🤙🏻
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_

*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*

*WATTPAD* _Realeshaa_

*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*

*PAGE 13&14*🖌️

________________________📖Kawar da kai Ahmad yayi tare da janyo Sukainat tafado kansa, ha'de bakinsu waje 'daya yayi yana bata wasu hot kisses masu wuyar mantawa, yayinda yatura 'daya hannun cikin sumar kanta dake da damshi yana yamutsa gashinta"Cikin karfin hali Sukainat tajanye bakinta daga nasa tayi kasa da kanta cike da matsanancin kunya.
Hannu Ahmad yasanya yashafi sajen sa yana sakarmata dawani killer smile,cike da zumudi yasake mika hannu zejanyota taja baya dasauri,tana girgiza masa kai alamar yabari,Cike da begenta yace pls me da'dina kibarni insha wannan sweet mouth din, shiru tayi taki cewa komai kuma taki matsowa kusa dashi"Kamar Wanda akace ya'daga kai yahango Nadiya tsaye kamar wacce aka dasata awajen idanunta sunka'da sunyi jawurr dasu fiye dana farko.
Mutsits-tsika ido yayi domin tabbatar wa shin itace ko idanunsa ke masa gizo"innalillahi wa'inna ilahi raji'un yake maimaitawa aransa, zahiri Nadiya ce atsaye kenan in haka da farko ita yagani be gezau idanunsa kemasa ba,?ya tambayi kansa"wani matsanancin kunyarta da shakku ne suka diran masa a zuciya"Anma dake namijin duniya ne se yada go kansa Cikin basarwa yace My Queen karaso mana kikatsaya a can, shiru tayi takasa cemasa komai sema sake kafesa datayi da kananun idanunta,sake cewa yayi pls come in"Da 'kyar ta Iya cewa no basena shigoba nazo ne in sanar daku breakfast is ready tanagama fadin haka tajuya afusace tabude kofar tamkar zata tashi sama.Dasauri Ahmad yamike zebi bayanta"hannunsa Sukainat tarike tana kallon yanda fuskarsa ke bayyanar da tashin hankali karara,cikin dakewa tace ina zakaje ya Ahmad?, Bakiga yanda Nadiya tafita bane ranta a'bace yafada yana kokarin mikewa janyosa tayi yafada kan bed din,cike da mamaki yake kallonta"Kau da Kai tayi tace agaskiya bazaka bitaba domin ita tashigo dakin batare datanemi iziniba,aganina ita yakamata tabamu hakuri bamu ba saboda haka bawani hakurin dazaka bata.
Har yabude baki daniyyan magana tayi saurin hade bakinsu waje daya,tashiga aika masa da sakonninta masu wuyar fassarawa Wanda batasan ta Iya ba,besan time dayafara mayar mata da martaniba suka rikewa juna"seda taga takawar da tunanin Nadiya aransa kafin tajanye jikinta daga nasa ta'fada toilet"sabon wanka tasake sannan tafito hango shi tayi yayi matashi da hannunsa yakurawa P.O.P dakin ido,kallo 'daya tamasa tadauke kai, direct jikin siff tawuce Riga da skirt na atamfa pink da ratsin fari tasanya"dinkin yazauna 'das ajikinta,skirt din yafitar mata da shape dinta hakama rigan yaimatukar amsar jikinta zama tayi akan stool tayi simple make up sannan tashafe jikinta da humra masu dadin kamshi,'dan kwalin tadauko tayi daurin ture kaga tsiya(No respect)abin hannu da sarka dakuma dankunne tasanya.Masha Allah kawai Ahmad ke maimatawa aransa ganin wani irin masifeffen kyau datayi,kasa hakuri yayi danhaka yamike cikin san'da ya isa gareta ya runguneta tabaya yana shakar dadda'dan kamshin humran datake kansa yacusa atsakanin wuyanta ya lasa.Murmushi tayi tasanya Hannu tadauki wayarta dake gaban dressing mirror tafarayi musu selfie ahaka ganin yanda sukayi kyau.'dago kansa yayi yakarbi wayan yana kallon pic din data dauka yayi wani irin kyau naban mamaki tamkar wasu jaruman India"Shima selfi ya shiga yimusu kala kala wani yana kissing dinta wani tasakalo hannunta awuyansu wani tana kan cinyarsa sunyi pic sunfi kala ashirin kowanne style dinsa daban"wayarsa yadauko yatura baki daya pic din dasu kayi,kamar Wanda akace yaduba time yaga 12:00pm ido yazare yace oh my God My Kainat dubi yanda time yawuce bakiyi breakfast ba bejira amsartaba yasun gumeta yayi dining area dake sashen Nadiya da ita.
Chapter 7 · 0% Book details