Sashe 28
Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*****
Sosai Ummi kemata fada ta Inda takeshiga batanan take fitaba"bayan tagama jin abinda tayiwa Nadiya,Sam bataji dadin dukan datayi wa Nadiya ba" itade hakuri kawai take bata anma kokadan batayi dana sanin akan abinda ta aikataba...Koda Malam Ahmadu yashigo Ummi tasanar dashi abinda yafaru seyashiga yimata nasiyya da fada kan bata kyauta ba kuma ta kiyaye gaba kada yasake jin tayi irin haka"Sannan tayi masa alkawarin baza tasake fada da Nadiya ba.Cike da ladabi ta'amsa tare dayimasa alkawarin Insha Allah hakan bazesake faruwa ba"Albarka yasanya mata kafin yafice...
Koda Malam Ahmadu yafita daga dakin, number Alh Ali yakira bayan sungai sane,Ya sanar dashi abinda yafaru tsakanin Sukainat da Nadiya..Hakuri Alh Ali yabashi tare dacewa Insha Allah yana zuwa yanzu ze mai da ita dakinta"Godiya malam Ahmadu yaimasa kafin yakashe wayar,yakoma dakin.Koda Alh Ali yakashe wayar seya kira number Ahmad anma,akashe"kwafa yayi dan yasan halin Ahmad da gangan ze kashe wayar dan kar aneme sa,fitowa yayi yadauki key motarsa direct gidan Malam Ahmadu yanufa... Abangaren Ahmad kuwa bayan fitarsu yakashe wayoyin sa duka dan kar atakura masa dakira"Kana yamike ya fita coumpound din tare dasake bawa Baba mai gadi umarnin karya bar kowa yashiga masa gida....
Am back💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Alhamdulillah nagama exam insha Allah zakuna jina akai akai.Nagode da addu'o'inku Allahu yabar zumunci😘😘
_VOTE, COMMENTS & SHARE_
*_ESHAA CE~_*🤙🏻
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(True life story)_
*Na Marubuciya*
_REAL ESHAA ~_
*WATTPAD*
_Realeshaa_
_Like my page on Facebook_ 👇🏻
https://www.facebook.com/REAL-ESHAA-FANS-114689303720405/
*_Ya Allah kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*
_Wannan page din kyauta ne agareki hazika kuma fasihiyar marubuciya *AUNTY BINTA UMAR ABBALE* Ubangiji Allah yakara daukaka ki fiye da yanda baki zato Alherin Allah ya kaimiki aduk Inda kike Inai miki fatan alkhairi._ 😍😍😍😍
*PAGE 45&46*🖌️
_______________________________📖Madede cin parlour dattijuwar suka shiga;Wanda akalla shekarunta zasu Iya kaiwa hamsin da biyar, ko sittin.Cike da dattako tanunawa Nadiya wajen zama,tana mebin fuskarta da kallon tausayi ganin yanda fuskar ta tuttuje kamar wacce sukayi kokawa da zakan ya".Zama Nadiya tayi tana matsar kwallar takaici da bakin ciki"Cike da tausayi dattijuwar takalle ta tace"Nadiya barayine suka shiga gidan ku sukayi muku irin wannan danyen aikin haka!?ina mijin naki shi kuma yashiga? ina fatan de basuyu masa illah irin taki ba!?ta karashe cike da jimamin ganin yanda halittar fuskarta tasauya baki daya!.Kuka Nadiya tafashe dashi tace"Wlh Mama hansi ba barayi bane sukayi min wannan abin face kishiya ta,dubi irin wannan abin da tayi min kuma abin bakin ciki agaban mijinmu tayi min, anma sam be dauki mataki akai ba kokuma ya dakatar da ita"karshe ma sakina yayi yakuma Koreni acikin wannan Daren yace inbar masa gidan sa!"Ga mahaifiya ta batada cikakkiyar lafiya,Hawan jini ke damunta,nasan kuma muddin naje mata da wannan bakin labarin, ciwon ta ze Iya tashi karshema yajanyo sanadiyyan ta,shiyasa nazo kitemaka min kamar yanda Allah yatemake ki takarashe cikin wata raunanniyan murya.Cike da jimami,gamida tausayin ta Mama hansi tace taya zantemake ki Nadiya?"Bayan bawata alaka me karfi bace atsakanina da mijinku banda alakar musulunci.Hawaye tashare tace inde mukaje ki kabashi hakuri ze hakura yamayar dani dakina,dan yana ganin kimarki da mutunci ki,amatsayin ki na Dattijuwar arziki wacce duk mutanen unguwar nan suka dauke ki tamkar Uwa.Shiru mama hansi tayi,tana nazarin kalaman ta tasan gaskiya tafada,duk mutanen unguwar nabata kima da mutunci amatsayinta na Babba wacce takama kanta da mutunci ta awajen su.Numfasa wa tayi kafin tamike ahankali tadauki hijab dinta tasanya,suka fice...
"Sun dauki sama da minti goma atsaye awajen suna knocking kofar anma shiru ba abude musu ba"seda Mama hansi tayi magana kafin baba mai gadi yabude mata,yana ganin ta da Nadiya yayi saurin maida kofar zerufe,gudun kar yayi lefi awajen Ubangidan sa"cike da kamala tace"Yi hakuri bashiga zanyi ba sonake kayimin sallama da me gidan.Baba Mai gadi komai bece komai ba yajuya yanufi cikin compound din dan isar da sakon su"Mintuna ka'dan da shigar sa,se gashi yafito Ahmad na biye dashi abayansa.Koda yaga mai kiran tasa seya durkusa har kasa yagaishe ta cike da mutunci dakuma karramawa.Amsa wa tayi fuska asake tare dacewa dan Allah Alh alfarma nazo nema awajenka,ba danni ba sedan girman Allah dakuma darajan manzon tsira Annabi Muhammad(S.A.W).nake rokon ka dakaji kan wannan yarinyar kamaida ita dakinta,duk da kasancewar bansan wani irin lefi tayi maka ba!anma dan Allah kayi hakuri kamai da ita dakinta tarayu akan 'ya'yan ta,yanda zata basu tarbiyan daya dace sannan hankalin iyayenta ya kwanta domin zamanta adakin mijinta shine kwanciyar hankalin su."Shiru Ahmad yayi yakasacewa komai saboda kunya da nauyin matar dayakeji bakaramin kwarjini tayi masa ba"hakika bazeki bin maganar taba,kodan fitowa da tayi awannan Daren,gakuma girman Allah da darajan ma'aikin Allah data hada shida shi yaci, ace yahakura ko dan mutunta maganarta..Cike da jin nauyi yace hakika Mama ina ganin girmanki dakuma kimarki,anma kiyi hakuri bazan Iya maida Nadiya ba harse tayi hankali takuma koyi hakuri da zama da mutane kafin in mayar da ita dakinta!!..Durkushewa Nadiya tayi tare da rike kafafunsa, cikin muryan kuka tace dan Allah Dadyn Rufy kayimin rai, Wallahi bazan sake aikata kwatan kwacin abinda Na aikata abaya, ba natuba nabi Allah da manzo,nakuma bika" idan harka sake kamani da laifi akan Sukainat Wallahi nayadda kayanke min duk hukuncin dakaga yadace akaina;Nayi alkawarin zamu zauna lafiya tamkar yanda ko wasu abokanan zama suke zaman lafiya, sannan zan riketa kamar kanwata koda lefi tayimin zanyi hakuri da ita babu Wanda zeji kan mu,takarashe zancen cikin gunjin kuka... Kafin Ahmad yace"wani Abu Mama hansi tace"dan Allah Ahmad kadubi darajan Allah kakuma dubu yarinyar nan, kayafe mata lefin datayi tunda ta amshi lefinta,ta kuma yi alkawarin bazata sake aikatawa ba.Shiru Ahmad yayi nawasu mintuna kafin daga bisani yace"Shikenan Mama taci albarkacinki nayafe mata nakuma mayar da ita dakin ta, Allah yayafe mana lefin mu baki daya..Cike da murna Mama hansi tashiga yimasa Albarka tare da fatan gamawa da duniya lafiya."seda yarakata Har kofar gidanta kafin yadawo cikin gida ko kallon Inda Nadiya take beyiba yawuce sashen,Sukainat yayi kwanciyar sa lokacin goma da Rabi yagauta...
Alh Ali na isa kofar gidan; yakira number Malam Ahmadu batare daya fita daga motar ba.Koda Malam Ahmadu yadaga, se Alh Ali yasanar masa da cewa yana kofar gida,sannan ya sanar masa su fito da Sukainat ze mayar da ita dakinta"Har tafara bacci,Malam Ahmadu yasa Ummi ta tasheta"tashinta Ummi tayi,Malam Ahmadu yarike hannunta suka fito.Batare da bata lokaci ba yashiga motar yatayar.Se misalin shadaya dawasu mintuna suka isa"hong ya danna,Dasauri Baba mai gadi yataso yabude masa kofa yana parking yanufi sashen tare da knocking, Ahmad dake kwance idanunsa alumshe kamar me bacci anma ba bacci yakeba tunani da damuwa ne suka mamaye masa zuciyarsa haka kawai yake jin canji ajikinsa yana jin tamkar wani mummunan Abu zefaru da rayuwar sa,wanda besan menene ba...Karan knocking din yakatse masa tunani hakan yasa yamike jiki asanyaye yanufi kofar.Karo sukaci da nadiya da alama itama karan knocking dinne yafito da ita"Batare dayace da ita komai ba yakara sa yabude kofar."Alh Ali yagani atsaye fuskar sa amurtuke babu alamar sassauci atare dashi,Dasauri ya durkusa kasa yace"Barka da wannan lokacin Baffa, kallon banza Alh Ali ya watsa masa yace"Bana bukatar gaisuwar ka,kuma banzo dan ka gaisheni ba dan haka karike abinka bana bukata... Kasa da kai yasake cike da jin nauyinsa,cikin sanyin murya yace "Dan Allah Baffa kayi hakuri Wallahi bahaka bane.Tsaki mai karfi Alh Ali yayi yace" ai ita wancan dake matar so ne kaje kamayar da ita anma wannan dake dole akayi maka ka aureta dole ka wulakan ta ta kakoreta,Ahmad kaji tsoron Allah acikin rayuwar ka shin kanaso ka mutu ranan gobe kiyama Allah yatasheka gefen ka ashanye saboda rashin adalci atsakanin matanka!!?Jikinsa ne yayi sanyi dajin kalaman Baffan nasa yace"Dan Allah Baffa kayi hakuri Wlh duk bahaka bane ba abinda kake zato bane anma Insha Allah zankiyaye ka kuma tayani da addu'a kan Allah yabani ikon adalci atsakanin su.Addu'a kam munayi sede kaima ka kokarta kokuma rika kokarin boye San daka keyiwa ko wacce atsakanin su dan susamu zaman lafiya.Cike da ladabi yabaiwa Allah Ali hakuri kana yamaisa alkawarin adalci atsakanin su, albarka yasanya masa kana yasake dan ka masa amanar Sukainat...Wucesa tayi tashiga sashen ta batare datace dashi komai ba tayi kwanciyar ta,shima bayanta yabi ya kwanta egenta zuciyarsa acunkushe dahaka bacci yadaukesu..